Sha'awada Jaraba Page 7&8 By Mom Islam - Abokiyar Hira Novels


SHA'AWA DA JARABA*

    (Love and Romantic story)

          💋💋💋



          Mom Islam 



Page 7-8


Ba wani lokaci mai tsawo suka ɗauka a hakan ba, yai janyeta daga jikinsa, kana ya wuce toilet, tana kwance a lulluɓe da blanket, ya fito ƙugunsa ɗaure da pink towel, da wani siriri a hannunsa, sumar kansa da take sheƙi tayi yalaf, ya fara gogewa, cikin sauri tare shiryawa, tana kwance tana kallonsa, "zanyi miki transfer.."


Ya faɗa yana ɗaukar key car ɗinsa ya fice, 

A gajiye ta miƙe ta shiga toilet ta tsarkake jikinta kana ta fito, doguwar rigar da tazo da ita a jikinta ta saka, ƙananun kayan ta ninkesu sosai sannan tasa a bag irin ta zuwa school, wacce ke ɗauke  da littafai a ciki, ciro farin ribom ɗin da yake ɗaure da gashinta tayi, ta sake gyara gashin wanda ya saukar mata har gadon baya, kulle ɗakin tayi, kana ta sauko ƙasa hannunta riƙe da school bag da key wanda, wata wacce take tsaye a reception ɗin ta bawa, wacce dama sun riga sun saba tun farkon zuwanta da doctor Muzaffar, 

Kai tsaye ta fice zuwa bakin titi ta tari mashin, kai tsaye gidan yayarta ta wuce,

Bayan mai mashin ya sauketa ta fara nocking a bakin get na gidan, mai gadi ya leƙo dan ganin mai nocking ɗin, sannan ya buɗe mata, gaishesa tayi cike da girmamawa saboda shi ɗin dattijo ne, ta ƙarisa ciki, Door bell ta danna, kana ta tsaya jira na buɗe mata, yayar tata ta buɗe ƙofar fuskarta ɗauke da murmishi, ga tace "yau ina kika tsaya ko baku tashi da wuri bane?"


Resh tace "anty Zubaida ai yau ba ƙaramin wahala nasha ba gurin karatu"

Anty Zubaida na riƙe da mararta tace "dan Allah tashi ki ɗora min abinci tun safe nake kwance babu lafiya, gashi Yazeed baya gari tun jiy"

Resh tayi mata sannu, tana cire hijab ɗin jikinta tace "baki je hospital bane?, wannan babyn yana wahalar dake, kafin ki haifeshi kin gama galabaita"

Anty Zubaida tayi murmishi kafin tace "Resh sai aka ce miki shikenen dan mutum ya samu ciki bazai warke ba kafin ya aihu?"


Resh ta shige ciki tana taɓe baki, da gyaran kitchen ta fara, kana ta gyara ko ina tsaf-tsaf sannan ta fara hidimar ɗora abinci, parlor ta dawo ta samu Anty Zubaida tayi barci, ga shi tana son tambayarta me take son a dafa, komawa kitchen ɗin tayi ta gyara kayan miya sannan tayi blanding ɗinsu kana ta kunna electric stove sannan tasa tukunya da mai ta soya albasa bayan sun soyu Harda su spices da su maggi ta zuba soyayyen kifi wanda ta gama cire masa ƙaya, kana ta rage wutar sosai, sannan ta juye couscous ɗin ta fara gaurayawa bayan ta gama ta zuba masa tafasasshen ruwa iya adadin yawan couscous ɗin ya rufe, ƙarar shigowar massage da taji a wayarta dake parlor a cikin bag yasa tai saurin zuwa parlon ta zuge zip na jakar ta ɗauki wayar sannan ta koma kitchen ta ɗauko warmer mai kyau ta juye abincin ta gyara ko ina kana ta dawo parlor duba massage,

Alert ta gani na 50k, tayi murmishi tana mai maita sunansa a cikin zuciyarta "Doctor Muzaffar" matashi mai jini a jiki mai ji da kansa.


 lokacin da ya shigo da motarsa cikin gidansu, yai parking kana ya fito ya fara taku cikin ƙasaita ya isa ciki, Diyana da Fateema ne a zaune, ko wacce tasha kwalliya da hand bag a saman cinyarta, sallama yayi kana ya nemi guri ya zauna, "Yah Muzaffar Barka da shigowa.."

Suka faɗa cikin haɗa baki, "Barka.." ya amsa yana ciro wayarsa da tai ƙarar shigowar saƙo, a tare suka tashi dan basa ƙaunar zama a inda yake zaune, bedroom ɗinsu suka wuce Fateema ta murza key, tare da jingina da jikin ƙofar murya ƙasa-ƙasa tace "shikenen mun shiga uku, wannan ba zai barmu mu fita ba"

Diyana tace "kina nufin bazamuje birthday din ba kenan.?"


"Eh mana ko kin manta waye Yah Muzaffar?"


Diyana ta sauke ajiyar zuciya kafin tace "Fateemah ki samo mana mafita dan ko gurin momy mukaje bazata taɓa bamu goyon baya ba tunda ya shigo, dama bai shigo bane"

Suna tsaye suna shawara sukaji anyi nocking,

Kowacce sai da ƴan hajinta suka kaɗa, Fateemah dake tsaye a jikin ƙofa ta matsa da sauri, Diyana tace "kamar da wannan nocking ɗin ba irin na Momy bane"

Fateemah tace "wa kike tunani?"

Diyana tace "na tabbatar da Yah Jawad ya tafi gurin aiki, kai wannan bugun ƙofar na yah Muzaffar me saboda wlhi komai nasa daban yake"

Ko wacce tayi tsuru-tsuru da idanu, suna gudun aikata laifi saboda shi baya raina duk ƙanƙantar laifi sai ya hukunta mutum dashi,

Fateemah ta murza key ƙofar ta buɗe, tsaye yake a bakin ƙofar idanunsa na kan wayarsa da yake daddanawa, sarai yaji buɗe ƙofar tasu, bai kalli gurin ba kuma bai ce musu komai ba, bakin Fateemah na rawa tace "mun..mun..buɗe...gamu.."

Har yanzu bai kulata ba, dan tayi tunanin bai jita bane, zata sake magana Diyana ta taɓata tayi shiru, ɗago fararen idanunsa yayi kana yace "kuje kitchen ku yimin farfesun naman rago kuma bana son ƙazanta, kafin ku taɓa kayan miya ko wacce ta wanke hannu, idan kun gama a kirani" ya faɗa yana barin gurin.

Wani irin takaicin baƙinciki suka ji dukkansu, fuskokinsu babu walwala suka amsa da cewa "toh" dole kowacce ta cire kayan ta, suka saka riga da wando t-shirt da jeans da hula a kansu, kitchen suka wuce, shi kansa naman yayi ƙanƙara a cikin frizer, suka fito dashi suka wanke, Diyana ta ɗauko turmi ta daka ɗanyar citta da su tattasai, ta ɗauko tumaturin leda, nan fa suka shiga aiki gadan-gadan wai duk dan suyi sauri su gama su tafi tunda dai ya fice, Fateemah tace "mun manta mu tambayesa manja ko mangyaɗa?"

Diyana tace "Mu saka manja kawai, saboda Momy yawanci na manja takeyi"


Fateemah tace "hmm Wllhi ina tsoron hukuncin yah Muzaffar inda kasan yayi rayuwar cikin sojoji, amma dai bari inje parlo in ɗauki waya in kirashi in tambayeshi"

Fita tayi zuwa parlor ta ɗauki wayar tafi da gidanka ta kirashi, baya wasa da ganin kiran gidansu, dan haka ya ɗaga da sauri, Fateemah tace "yah Muzaffar manja za'a saka ko mangyaɗa?"

"Mangyaɗa"

Ya faɗa yana katse kiran,

Fateemah ta dawo ta gayawa Diyana, a tare suka sauke ajiyar zuciya suna cewa Allah ya taimake su, sun mugun gajiya kafin su kammala, Diyana tace "yau kashinmu ya bushe a gurin classmate ɗinmu"

Fateemah tace "ba wata matsala ai mun kammala kawai ki juye masa sai a kirashi a waya, ki fito mana da kayan da zamu saka da bags sai mu wuce, shigowa yayi ya samu Siyan ta ajiye Warmer ɗin a saman table na parlor, ya kai hannu ya buɗe "good" ya faɗa yana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, Please ku dafa jollof ɗin shinkafa yanzu abokaina sun kusa ƙarasowa, sannan ayi musu juice, ayi abincin har dare tunda yamma tayi, Hajiya ma ta kusa dawowa,

Suka wuce kitchen, Fateemah ta fashe da kuka marar sauti, haka ma Diyana kuka ta farayi...!

Ayi haƙuri da typing errors 

Mom Islam 08141799224

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post