_Bossladieswriters_
_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q
WhatsApp Group
https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_
_ZAINAB BATURE_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 15
Dawowa hajiya ta yi ta nufo cikin falon tana gyara zama glasses dinta tare da faɗin, "Kai, abun dai bai yi dadi ba sam, ni bana son abun tashin hankali wllh..." Tsayawa ta yi ba tare da ta ƙaraso cikin falon ba ta ce, "Salma ta so kin ji." Miƙewa ta yi tana gyara gyalenta ta nufi hajiyar, kama hannunta ta yi suka koma hanyar da ta fito, cikin corridor ɗin da ɗakuna suke suka nufa, wata ƙofa hajiya ta tura suka ta shiga tana riƙe da hannun Salma, wani irin sanyin ac da ƙamshi ne suka karade cikin ɗakin, gaban Salma ne ya faɗi ganin Fahad ɗin kwance a saman lafiyayyan gadon ɗakin ya kwanta rigingine tare da rufe idanun shi,
"Zo ki bashi haƙuri, ai durƙusa ma wada ba gajiyawa bane, balle ma wannan ba wadan bane, shi bin na gaba bin Allah ne." A ɗarare Salma ta matsa daga bakin gadon ta durƙusa ƙasa, idanunta cike da ƙwalla cikin rawar murya ta furta, "D...don Allah Ka yi haƙuri." Shiru kaman bai san da su a wurin ba don ko motsawa bai yi ba,
"Fahad, baka ji ana magana ba."Hajiya dake tsaye bakin gadon ta faɗa idanunta akan shi, sai da aka ɗan ɗauki lokaci sannan ya bude idanunsa da har sun ɗan sauya kala, nuni hajiya ta yi mashi da Salma ta ce mashi gata nan tana bashi haƙuri, ɗaura idanunsa ya yi akanta still tana durƙushe suka haɗa ido ya wani ƙara tamke fuska, "Ka yi haƙuri don Allah..." Ta faɗa tana sussune kai tare da kai hannu tana ta6a gefen fuskarta, ɗauke idanun shi ya yi ba tare da ya ce komai ba, hajiya ce ta ƙara ce mashi ya yi shiru sannan a taƙaice ya ce, "Ta je." Sanin yana da zuciya ya sa hajiya yin ɗan murmushi ta ce, "Ka haƙura ko?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ɗan ɗaga hannu, hajiya ta ce, "Ba shike nan ba, taso to Salma." Miƙewa ta yi suka nufi ƙofa, a hankali ya juya yana kallon bayan su har lokacin fuskar shi a ɗaure take, can ƙasan maƙoshi ya ɗan ja guntun tsoki bayan sun fita.
Cikin falon suka dawo Deen ya ɗaga ido yana kallon su, wuri hajiya ta nuna ma Salma ta ce ta zauna itama ta zauna, "Ta bashi haƙuri ba shike nan ba, dama duk sharrin zuciya ne ba wani abu ba, da kuma shaiɗan da bai son ya ga an zauna lafiya." Hajiya ta faɗa tana daga hannu idanunta akan Deen, ɗan murmushin gefe Deen ya yi ya ɗauke idonsa daga kan su, bayan ɗan lokaci Salma ta miƙe tana kallon hajiya ta ce mata zata tafi gida,
"To shike nan Salma na gode. Komi ya wuce kada ma ki yi maganar a gida kin ji ko. Kuma daga yau kada ki sake yi ma babba haka, idan babba ya yi maka abu ka rama people will see you as disrespectful, don haka koda abu bai yi maka daɗi ba, in dai babba ne ya yi maka ka yi haƙuri ya fi kuma hakan ba faɗuwa bane, kin ji?" Kai ta ɗaga a sanyaye ta ce, "In sha Allahu ba zan ƙara ba." Hajiya ta ce, "Yauwa Salma, dama na san ba halin ki bane, kawai sharrin zuciya ne." Shiru Salma ta yi kafin a hankali ta ce mata sai anjima ta juya ta nufi kofa, "Salma ɗan dakata, bari a kawo maki robar...koda yake je ki ma kawai zan aiko a kawo harda saƙo." Kai ta jinjina ta ci gaba da tafiya, tana zuwa ƙofa zata fita, a hankali ta juya da niyyar ta saci kallon Deen, kamar an ce shima ya ɗago karaf suka haɗa ido da sauri ta juya ta fuce, ya yi kaman zai yi murmushi ganin yadda ta yi.
Miƙewa ya yi zai bar falon hajiya ta ce halan ya gaji da zaman, shafa sumar shi ya yi ya ce mata zai je ya shirya ne za su je gidan su Fahad,
"Ko ku bari zuwa bayan magrib don ga awara can ana haɗa maku kuma tafi daɗi mutum ya ci ana gama soyawa, na san dai ba wani ƙoshin kirki kuka yi ba, bama kamar kai nasan ka baka wasa da abinci, dama ana cewa ƴan ƙwallo cin tsiya ne da ku. To dama yadda kuke jijjige jiki ma ai dole ku ci abinci." Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya juya ya nufi hanyar corridor.
Cikin sauri take tafiya bayan da ta fito daga cikin gidan, lokacin da ta shigo kwanar gidan su ta hango su Sagir acan saman dandamalin gidan dake kallon gidansu, su da yawa suna ta hargowa, ashe baya a gida, tun yana gama cin abinci bai daɗe da kwanciya ba wani abokinsa ya kira sa yake sanar masa game da zuwan Deen, aikuwa wuff ya tashi, rigarsa ma a ƙofar gida ya ƙarasa saka ta, lokacin da Salma ta shiga gidan hajiya yana a cikin mutanen da ta gani a wurin parking space don da bala'e sai da ya yi yadda ya samu suka shiga, zaman da suka yi a nan tattaunawa suke akan ganawar da suka yi da Deen ɗin inda ya yi masu albishir da zai kafa sabon club ɗin shi anan Funtua shine ya basu za6in sunan da suke son a saka ma club din shine fa ake ta musayar ra'ayi kamar za su tashi sama don daɗi, ko kallon su Salma bata yi ba lokacin da ta ƙaraso saitin su ta wuce zata shiga gida,
"Ke, Salma zo nan..." Banza ta mashi ko juyowa bata yi ba,
"Ba ki ji ina kiran ki! ga Aliyu nan shine ke son magana da ke." Wani irin 6acin rai ta ƙara ji ya kama ta, Aliyun abokin shi ne yake haɗa ta da shi wai son ta yake, ita kuma ta ƙi kula shi don harkar samari bata a gabanta karatunta ta saka a gaba, bama Aliyun kaɗai ba ana yawan cewa ana son ta amman bata sauraran wani saurayi, burinta ta gama makaranta ta wuce ta yi karatun nursing ta zama kamar auntynta Kubra, kuma har da ita Kubran ta yi mata huɗubar kar ta biye ma samari ta maida hankali kan karatun ta don in dai tana son zama nurse sai ta yi karatu sosai. Bata iske kowa ba a tsakar gidan bayan ta shiga, kai tsaye hanyar banɗaki ta nufa, a bakin rijiya ta ɗauki buta wadda ke da ruwa a cikinta, ƙarar motsin da innarsu ta jiyo ya sa ta ɗaga murya daga cikin ɗaki tana tambayar waye anan ta bata amsa da ita ce,
"Salma kin dawo?" Ta ce mata eh, tana ƙoƙarin shigewa cikin banɗakin daidai innar ta fito sai dai ta ga shigewar ta, tana shiga ciki ta yi tsaye tare da jingina da bango zuciyarta ta shiga dawo mata da abun da ya faru, ƙwalla ne suka shiga zubo mata ta fara yin kuka a hankali, bata ta6a dana sanin abu kamar wannan ba, maida akalar tunaninta ta yi kan Deen, yanzu ta gane shine ɗan ƙwallon da su Sagir ke maganar shi, ita sam bata san shi ba, ko Fahad bata ta6a gani ba, dama bata fi shekara biyar da ta dawo garin ba daga Kaduna, kuma basu daɗe da suka fara yin hulɗa da hajiyar ambasada ba sanadin Balaraba da ke kawo a yi masu awara, kuma ba kasafai ta cika zuwa gidan ba don wani lokacin idan aka gama Balaraba ce ke zuwa ta amsa ko kuma a aika su Imran su kai, ita zuwanta gidan ma za a iya ƙirga shi, fuskar Deen ce ta shiga dawo mata, ita kanta ta gasgata kyawunsa sosai, ga shi komai nasa mai burgewa ne, ba ƙaramin daɗi maganar shi ke yi mata ba,
_"Kina ma wa kuka? Ko wani ya sa ki ne ki yi mashi rashin kunya....."_ Maganar da ya yi mata ta tuno, a ranta ta ayyana yanzu shike nan kallon mara kunya suke mata, idanuwanta ne suka cicciko da ƙwalla ta ƙura ma wuri ɗaya ido, ta ɗauki mintuna a haka kafin ta duƙa ta wanke fuskanta da ruwan cikin butar da ta shigo da ita, dama ba wani abu za ta yi a banɗakin ba kawai bata so innar su ta fahimci wani abu ne. Lokacin da ta fito daidai innar su itama ta fito daga cikin kicin, tsayawa ta yi da murmushi tana jiran ƙarasowar ta, daga gefe Salma ta tsaya ta ce mata hajiyar ta ce zata aiko da robar da kuma saƙo innarsu ta ce to, shiru suka ɗan yi Salmar tana kallon gefe,
"Salma..." Har saida gabanta ya bada rass jin yadda ta kira sunan ta, juyowa ta yi suka haɗa ido, "Ya aka yi ne?" Ƙaƙalo murmushi ta yi ta ce mata ba komai,
"Ah saidai idan abun da baki yi mani zaki fara, amman daga ganin fuskar ki akwai abun da ke damun ki, kamar ma har kuka kika yi ko?" Shiru ta yi tana kikkafta ido, tunowa ta yi da gargadin da hajiya ta yi mata kuma ko ba haka bama bata jin zata sanar da ita abun da ya faru don ta san itama ta yi ba daidai ba abun da ta yin, dabara ce ta faɗo mata cikin ɗan yamutsa fuska ta ce, "Ba wanccan Sagir ɗin bane." Tana jin ƴar ajiyar zuciyar da innar tasu ta sauke alamar hankalinta ya kwanta, "To mi kuma ya haɗa ki da shi ku da baku gajiya?"
"Wai yanzu na taho zan shigo shine ya kama yi mani maganar wannan Aliyu, kuma ya san na ce mashi ya daina haɗa ni da shi ban so amman ya ƙi dainawa." Yar dariya innar tasu ta yi ta ce to in banda abun ta miye laifin wanda ya nuna yana son ka, cikin tura baki ta ce ita dai bata so kuma ma ba aunty Kubra ta hana ta yin wata soyayya ba ta ce ta maida hankali akan karatu,
"Haka ne, shike nan ki bari zan gargaɗi Sagir ɗin kan hakan. Kin ma tuna mani da baki nan mamar taki Kubra ta kira waya tana tambayar ki na ce mata kin fita idan kin dawo kya kira ta." Lokaci guda ta washe baki jin maganar, Allah Ya sani tana son Aunty Kubra sosai saboda itama tana nuna mata ƙauna, wani lokacin har mamaki Salma ke yi yadda take tsananin ƙaunarta, duk da dalilin hakan kusan a bayyane yake bai rasa nasaba da rashin haihuwar da Allah bai bata ba, tambayar innar tasu ta yi ina wayar ta kira ta ta ce mata tana cikin ɗaki, ta wuce da sauri don ta je ta kira ta.
Bayan sallar magrib su Deen suka fito cikin falo don tafiya gidan su Fahad, yana sanye cikin ƙananun kaya farar t-shirt sai overshirt ja irin riga da ake ɗaurawa a saman wata mai budaddan gaba da ana ganin ta ciki, wandon jikinsa dark-washed jeans ne sai ƙafafunshi ya sanya takalma fararen gucci ace, hannun shi haɗaɗɗan agogo ce mai duhu da ta hau da kalan wandon jikinshi, ya yi kyau har ya gaji sai faman baza ƙamshi yake, shi kuma Fahad ƙananun kayan da ya canza ɗazun ne a jikin shi, gaba ɗaya falon ya karaɗe da kamshin jikinsu, hajiya dake zaune ta kalle su da murmushi ta ce sun fito Fahad ya amsa mata, Balaraba ta ƙwala ma kira ta fito, umarnin ta ɗauko saƙon ta bata ta amsa da to kafin ta juya ta koma cikin kicin, fitowa ta sake yi hannunta riƙe da wani ɗan madaidaicin kwando kalan na ƴan gayu a cikin shi warmer ne guda biyu yar madaidaiciya sai mai bi mata,
"An ce so so ne, amman dai son kai ya fi, gashi nan ku kai ma baban naku." Murmushi suka yi gaba ɗaya, Fahad ya ce amman dai ta san zata haɗa rigima ne, tana dariya ta ce ai ta san zai samma su, Fahad ya ce ma Balaraba ta je ta kai basket ɗin wurin motar shi ta amsa mashi da to cikin ladabi duk da da gani ta girme mashi, sallama suka yi ma hajiya ta ce su gaishe mata da kowa. A motar Fahad da suka zo da ita suka fita, lokacin da suka fito wajen gate ɗin akwai wasu mutane a tsaye da alama Deen suke son gani ba a basu dama ba,
"Mutanen nan fa baza su ƙyale ka ba, duk da ka faɗa masu baza ka samu ganin su ba ka ga still suna nan." Deen ya ce Allah ma ya sa basu san yana a motan ba ya san har biyo su suna iya yi, ya ce zai yi ƙoƙari ya samu isasshen time ya gan su. Bayan wasu mintuna suka ƙaraso gidan su Fahad dake a bakin babban titi wanda babban gida ne na gaske, karya kan motar Fahad ya yi ya tunkari tangamemen gate ɗin gidan, yana yin horn maigadi ya leƙo ta ƙaramar ƙofa, yana ganin motar da sauri ya koma ciki ya fara buɗe masu, ciki suka shige mai gadin na ɗaga ma motar hannu duk a tunanin shi Fahad ne kawai, bayan sun shiga cikin harabar gidan mai girman gaske kai tsaye katafaren ginin gidan motar ta tunkara basu nufi inda parking space yake ba, a bakin entryhall motan ta tsaya a tare suka fito, maigadi dake can bakin gate yana ganin sun fito su biyu ya ƙara ware ido a ranshi ya shiga ayyana ko dai tare suke da Deen, nufo su ya yi da ɗan sauri yana ƙara wara ido don ya tabbatar ma kan shi ko Deen ne, tun kafin ya ƙaraso ya gane shi ɗin ne saboda hasken dake akwai a wurin, washe baki ya shiga yi bayan ya iso ya shiga faɗin, "Barka da zuwa yalla6ai...barka da zuwa, dama sai da na yi tunanin ko kai ne wllh." Sam ya kasa rufe baki sai kace yaro ya tsinci haƙori, amsa mashi Deen ya yi ya ce mashi ya aiki, da sauri maigadin ya ce, "Aiki Alhamdulillahi gashi muna akan shi muna ta ƙoƙari. Yallabai ya naku aikin ai kaima gaskiya ba ƙaramin ƙoƙari kake ba wllh muna matuƙar yaba maka, da yake nima ɗan club ɗin ku ne duk wani wasa da zaku yi sai na kalla, da a wayata nake kallo lokacin ina da andiroyin kafin ta lalace in koma mai madannai, amman duk da haka duk idan za a yi ƙwallon ku akwai wani ɗan ƙauyen mu da ke anan shi nake sawa ya zo ya tsare gate ɗin in je gidan kallo in kalla. Wllh ai duk muna yin ka yalla6ai..." Sai faman washe baki yake kai ka ce wanda aka ma albishir da gidan aljanna, murmushi ne akan fuskan Deen ya yi mashi godiya, Fahad da ya fara gajiya da tsayuwa ya ce mashi an gode daga haka ya kama hannun Deen suka wuce, maigadin nata hargowa yana faɗin a fito lafiya yallabai, ɗan ɗaga mashi hannu Deen ya yi ya ce zai ganshi da sauri ya amsa mashi da to, nufar komawa bakin gate ya yi a ranshi yake ayyana ina ma wayan shi andiroyin bata lalace ba da sai ya roƙe shi sun yi hoto ya watsa a fesbuk, a yanzu ma ɗin ma alla alla yake ya je ya fara kiran abokansa da suke kallon ƙwallo tare ya yaɗa masu labarin zuwan shi,
Tun a walkway ɗin shiga cikin gidan zaka fara shaida tsaruwar shi, har da wani haɗaɗɗan console mirror da manyan flower vases masu ɗauke da tafka tafkan fulawoyi, wani babban falo suka shigo mai ɗauke da light purple ɗin kujeru, komai na cikin falon kalar light purple ne wasu abubuwan an yi ratsin dark purple, hatta hasken fitulun cikin falon wasu na bada launin purple, a saman luntsuma luntsuman kujerun dake ciki wasu daga cikin ƴan gidan ne ke yin kallo, autar su Binafa ce ta shigo cikin falon zata nufi wurin da sauran suke, tana hango su Fahad da suka shigo ta nufi wurin su, tun kafin ta ƙarasa idanunta suka sauka akan Deen, cikin ƙaraji ta furta, "Laa, ga yaya Deen ɗin ball nan wllh!" Hakan ne ya jawo hankalin sauran kan su, da gudu Binafa ta nufi Deen ya wara mata hannu yana sakin faffaɗan murmushi, tana zuwa ya ca6e ta tare da ɗaga ta sama ta shiga ƙyalƙyata dariyar farin cikin ganin shi, Sadeeq ne ya rugo shima yana washe baki, Deen ya sauke Binafa shima ya ca6e shi ya ɗaga shi yana faɗin, "My man ka ƙara girma ka yi nauyi da yawa.." Duk suka yi dariya, Binafa ta ruga tana faɗin bari ta je ta faɗo ma momy ga ya Deen ɗin ball ya zo, bayan ya sauke Sadeeq kallon Khaleel dake tsaye yana ta sakin faffaɗan murmushi ya yi ya miƙa mashi hannu suka gaisa, cike da zolaya Khaleel ɗin ya ce shi ba za a ɗaga shi irin na su Sadeeq, Deen na murmushi ya ce, "Ai kai ka girma da yawa, kama kusa kamo ni tsawo." Duk suka yi dariya Khaleel ɗin ya yi mashi an zo lafiya ya amsa mashi, yayarsu Sadeeya wadda ita ce ke bima Fahad ta ƙaraso wurin tana sakin murmushi jikinta tana sanye da straight skirt da riga na atamfa, a yanayin halitta bata da tsawo sosai amman tana da diri kuma tana da kyawun fuska, akwai kamanceceniya sosai tsakaninta da Fahad duk da haskenta bai kai na Fahad ba,
"What a surprise visit! You'are highly welcome my lil bru." Ta yi maganar tana miƙo mashi hannu alamar su gaisa, Deen na kama hannun ya murɗe shi ba arziƙi ta saki ƙara tare da duƙewa, cikin jin zafi ta furta, "Mi na yi maka kuma, daga abun arziƙi na yi welcoming naka." Yana murmushin ƙeta ba tare da ya saki hannun ba ya ce, "Who's ur lil bru?" Cikin nuna alamun jin zafi ta furta, "Ƙarya na yi to kai ba ƙanin nawa bane..." Bata ƙarasa ba ta ƙara sakin ƙara da ƙarfi sakamakon ƙara lanƙwasa hannun nata da ya yi,
"Ahhh...kar fa ka karya mani hannu Deen, kasan dai wanda zan aura soldier ne zaka tsinci kan ka a guardroom wllh." Yana ƴar dariya ya ce tun da ita yayar shi ce ba sai ta ƙwace hannun ba, su Fahad dake tsaye suna ta murmushi, hajiya Amina ce ta shigo cikin falon tana tafiya a nutse irin ta manyan mata masu cikar kamala, tana da ƙwarjini sosai a fuska gata jajir da ita, doguwar riga ce a jikinta ta yafa mayafi a saman kanta daga gaban kanta kitson da aka yi ma baƙar sumarta ya ɗan fito, da murmushi akan fuskarta ta iso wurin, Sadeeya na ganinta ta ce, "Momy kin gani zai karya ma ɗiyar ki hannu ko, pls ki ce mashi ya sakar mani hannu." Dariya ta yi ta ce ita ba ruwanta dama ai sun saba kuma ta san ita ce ta ja shi.
"Welcome my son." Ta faɗa da murmushi, ɗan rankwafar da kan shi ya yi ya gaishe da ita ta amsa tare da yi mashi an zo lafiya,
"Pls ka sakar mani hannu wllh fa ina jin zafi." Yar harararta ya yi, ya ce, "Sai kin faɗa da bakin ki ni yayan ki ne." Tura baki ta yi ta ce, "To wai a ina ka zama yayan nawa ba na girme ka ba, ko don ka ga ka zama jibgege shine zaka fara yin runton shekaru." Ɗan girgiza kai momy ta yi jin yadda basu gajiya da yin musun shekaru duk in suka haɗu,
"Bari in raba gardaman, rigima ne kawai naki Sadeeya amman kin san Deen ya girme ki, duk da ba wani nisa ne sosai tsakanin ku ba, ya baki shekara ɗaya." Dariya duk suka yi Deen ya ce mata small girl, tana dariya ta ce ta ji to ya sakar mata hannu, ƙin saki ya yi ya ce sai ta faɗa a gaban kowa shi yayanta ne, ƴar hararar shi ta yi aikuwa ya ƙara murɗe hannun ta saki ihu tana faɗin, "Don Allah Ya Deen ka yi haƙuri wllh zaka karya mani hannu fa." Gaba ɗaya suka saki dariya jin ta yada makaman nata ta kira shi da yaya, yarfe hannun ta shiga yi bayan ya saki tana faɗin kamar da hannun ƙarfe ya riƙe ta,
"Wllh ya yi maki ma da sauƙi yaya Sadeeya, da ya kama ki sosai to sai kin yi acawi a jiki." Dariya duk suka yi jin kalaman Sadeeq, momy ta ce mutum ya zo sun ƙi bari ya shiga ya je ya zauna, kallon Deen ta yi ta ce, "Let's go in my son." nufar ciki suka yi duk suka zazzauna a saman kujeru, ƙara gaisawa suka yi da momy ta tambaye shi ya zo lafiya da kuma iyayensa na can,
"Yaya Deen ai duk in kuna yin ƙwallo muna ganin ka." Binafa ce da ta maƙale a jikinsa ta faɗi hakan, ɗage mata gira ya yi ya tambaye ta da gaske, ta ɗaga mashi kai ta sake cewa, "Kuma ka iya sosai, idan ka ci ball sai mu yi ihu mu ce, 'A goalll..' har rawa muke yi, idan kuma baku ci ba sai bamu jin daɗi, mu yi ta tsoki har mu zagi waɗanda suka ci ku." Momy da ke zaune ta ce 'assha' duk suka yi dariya, ƙara rungume ta Deen ya yi ya ce mata ai haka wasa yake ba kowane lokaci nasara ke a wurin naku ba su daina damuwa. Hira suka ci gaba da yi Sadeeya ta iso wurin su tana riƙe da tray an ɗaura jug da glass cup a kai, a saman wani babban haɗaɗɗan center table na glass wanda ke bada launin purple ta ɗaura tray din, wani ƙarami ta ɗauko a can gefe ta aje daga gaban Deen ta sauko tray ɗin ta ɗaura sama, tsiyaya mashi lemun ta yi ta bashi tare da faɗin gashi don ba halin shi na mugunta ba, yana murmushi ya kar6a ya ce, "Thank you my lil sis." Ƴar hararar shi ta yi tana murmushi ta zauna a saman kujera,
"Son, ka yi mana zuwan bazata, ban yi tunanin zamu gan ka yanzu ba, I thought sai ka ɗan kwana biyu a Abujan, gashi ba a shirya maka abu na musamman ba nasan ka yi missing food din nan. Koda yake ƙilan ai mom ɗinka na can na yi maku irin su." Ta ƙarasa da murmushi a kan fuskarta, amsa mata ya yi da ba komai ai sun ma jima da zuwa suna gidan hajiya, kallon Fahad ta yi ta ce miyasa bai kira ya sanar da zuwan su ba, dakatawa ya yi da latsa wayan da yake ya ɗan kalle ta ya ce ya manta bai yi tunanin hakan ba,
"Akwai tuwo, kasan dad din naku ƙa'ida sai ya ci tuwo da dare, amman idan baka son shi sai Sadeeya ta yi preparing maka wani abincin." Momy ta faɗa da murmushi, ce mata ya yi lafiya lau yana son tuwon ya daɗe bai ci shi ba,
"Yaya Deen a can ba a yin tuwo?" Binafa ta tambaya, kallonta ya yi ya bata amsa da mom Sapna na yi masu idan ya je gidan amman wani lokacin yana daɗewa bai samu zuwa ba idan sun tafi wasa, umarnin zubo mashi tuwon momy ta ba Sadeeya ta tafi, kafin ta dawo daddy ɗin su ya shigo cikin falon ya nufo inda suke, Alhaji Sa'ad mutum mai dattako da haiba yana sanye da riga da wando na brown ɗin shadda, da ganin kayan ƴan cikin babbar riga ne amman bai saka babban rigan ba, sannu da zuwa mutanen cikin falon suka shiga yi mashi yana amsawa yayin da ya nufi Deen da murmushi, miƙewa Deen ya yi yana gaishe da shi dad ɗin ya miƙa mashi hannu suka gaisa, "Mutan turai barka da zuwa, fatan ka zo lafiya" Amsawa ya yi da ɗan faffaɗan murmushi, daddy ya ce mashi ya zauna shima ya nufi kujera ya zauna,
"To ya ƙasar taku, ya kuma tamolan. Ai ina ganin yadda ake ta ƙoƙari, Allah Ya ƙara taimako Ya kuma tsare." Gaba ɗaya suka amsa da Amin, Deen na murmushi ya ce, "Daddy ashe kana kallon ball." Dariya daddy ɗin ya yi, ya ce, "Can baya dai ina kalla amman sai na bari, yanzu kuma tun da yarona na yi ai dole in rinƙa kallo." Duk murmushi suka yi, Binafa ta ce, "Ai tare ma muke kalla, kasan mi yaya Deen?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, ta ci gaba, "Idan muna kallon ball en ka ka ci sai daddy ya ce, 'goalll, that's my son, I'm very very proud of you Deen, ya yi ta jin daɗi yana dariya. Idan kuma kuka gama yin ball baku winning ba sai bai jin daɗi, fuskan shi ya yi haka, sai ya ce, 'dama wasa ya gaji haka sai haƙuri." Ta ƙarasa tana ƙyalƙyata dariyar kwaikwayon daddy ɗin nasu da ta yi, kowa dariya ya yi har da daddy ɗin, hannu ya kawo alamar zai kamo ta yana faɗin,"Zo nan ummina, wato kina nan kina karantar duk yadda nike yi ko, har na zama abun zolaya." Hayewa ta yi kujera ta lafe jikin Deen tana ta dariya, Sadeeya ce ta iso hannunta riƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci, tambayar Deen ta yi ko ta kai mashi dining area ya ce eh ta juya,
"Ba dai tuwo zaku ba mutamin turai ba, koda yake watakil ya daɗe ma bai ci shi ba, ƙilan ya ji dadin shi." Momy na murmushi ta ce haka ya ce ya daɗe bai ci shi ba, ce mata ya yi to shima akai mashi nashi can dining ɗin sai su ci tare da son don an daɗe basu ci abinci tare ba, sai lokacin Fahad ya tuna da saƙon da hajiya ta bada, kallon Khaleel ya yi ya ce mashi ya je motanshi a backseat akwai basket ya ɗauko, after few minutes ya dawo hannun shi riƙe da basket ɗin, Fahad ya kalli daddy ya ce mashi ga saƙo nan in ji hajiya,
"Ni aka ce akawo ma saƙon?" Daddy ya tambaya idonsa akan basket ɗin Fahad ya ce mashi eh, gyara zama ya yi yana faɗin to bari ya ga saƙon miye hajiyan shi ta bada a kawo mashi, da sauri Binafa ta taso tana faɗin bari ta buɗe mashi, maƙe kafaɗa daddy ya yi ya ce shi zai buɗe abun shi, zama ta yi a kusa da shi yayin da ya duƙo yana kokarin buɗe warmers ɗin, yana buɗewa ƙamshin abun ciki ya dakar mashi hanci har sai da ya ɗan lumshe ido yana murmushi, waro ido Binafa ta yi tare da washe baki, Sadeeya da ta dawo falon ta matso tana faɗin bari ta ga miye aka kawo ma daddy din, "Ya Fahad anya baka yi kuskure ba bamu hajiya ta ce akawo mawa ba?" Sadeeya ta faɗa, ɗan murmushi ya yi ya ce na daddy ne, momy dake murmushi ta tambayi miye aka kawo ma daddyn? Binafa ta yi saurin cewa awara ne da chicken sauce, awaran daddy ya ɗauko guda ɗaya bayan ya dankwalo sauce ya kai baki, lumshe ido ya yi tare da furta, "Uwa mai daɗi. Allah Sarki hajiyana, Allah Ya ƙara maki lafiya da nisan kwana masu albarka." A tare duk suka amsa da Amin, rufe warmer ɗin ya yi ya fara kokarin miƙewa yana faɗin shi yama fasa cin tuwon bari ya je part ɗin shi ya ci abun da mamanshi ta aiko mashi, aikuwa da sauri Binafa ta riƙe basket ɗin tana faɗin to su fa, ɗaure mata fuska ya yi ya ce to su aka aiko ma da shi ne, suma idan suna so momynsu ta yi masu,
"Wayyo daddy, amman ya za a ce ido guba." Sadeeya dake tsaye ta faɗa, miƙewa Khaleel da Sadeeq suka yi suma suka je suka zagaye daddyn abun gwanin ban dariya,
"To wai ku ma ba tana aiko maku da abu ba ina saka maku ido ne, sai yanzu don nima an kawo mani zaku yi mani taron dangi. Ga momynku nan idan kuna so sai kuma ta baku kamar yadda nima momyna mai sona ta bani." Tura baki Binafa ta yi ta ce to ai dai suma hajiyan kakarsu ce ko, miƙa ma Sadeeya ya yi ya ce ta ba kowa tun da basu son ya ci ya ƙara ƙiba, amsar basket ɗin ta yi tana dariya ta ce, "Daddy dama ai kaza mai ƴa'ƴa bata maiƙo." Yana yar dariya ya ce kawai dai sun cika son kai. Kowa ya yaba da daɗin awaran bayan sun ci har da daddy ɗin ma, Deen da Fahad su basu ci ba cewa sukai sun ƙoshi sun ci a can gidan hajiya, Sadeeya ta ce gaskiya suma za su yi irinta gobe, momynsu ta ce to sai a kira hajiya a yi mata magana tun da dama idan suna son awaran daga can unguwarsu ake yo masu.
Bayan sun gama cin awaran, gaba ɗayansu har da daddy da Deen suka wuce dining area don cin abincin dare dama duk basu ci ba, Binafa da Sadeeq dai cewa suka yi yadda suka ci awara mai daɗi baza su ci tuwo ba sai dai su haɗa cornflakes da madara su sha, momynsu ta ce su dai suka sani da gulma tuwon ma ai special tuwo ne. Bayan sun gama cin abincin Fahad ya wuce da Deen zuwa part ɗinsa dake a can saman bene......
