Sha'awa da Jaraba Page 3&4 By Mom Islam


Mom Islam: 💋💋💋

*SHA'AWA DA JARABA*

    (Love and Romantic story)

          💋💋💋

          Mom Islam 

Page 3-4

Tashi yayi cikin natsuwa gami da takunsa mai ɗaukar hankali, Momy ta fito hannunta riƙe da cups ta ajiye a saman table, kafin tace "dan Allah ayi musu haƙuri suyi breakfast"

Doctor Muzaffar yace "no. Momy rainin su yayi yawa, kamar inda na faɗs sai na kammala, Momy ce ta fara zuwa ta zauna kana ta ɗauki plate ta sakawa Doctor Muzaffar soyayyen dankalin turawa da ƙwai, kana ta haɗa tea ta ajiye a gabansa, wayarsa ta sake yin ringing again sunan Doctor Ashraf ne, tsaki yaja, tare da ɗaukar cup ɗin tea yakai bakinsa, a hankali yake tauna cikin natsuwa, "Doctor ba kiranka akeyi ba..?"

Momy ta tambaye shi, "kira ne.."

Ya faɗa a taƙaice.

Sautin kukan Diyana ne ya karaɗe parlon, ta mugun gajiya dan ko iya ɗaga ƙafafunta batayi, Fateema ma durƙushewa tayi tana kuka marar sauti, Momy ta ja kujerar da take zaune baya, ta tafi gurinsu dan ta kasa kai koda wani abu ne bakinta, shiko cin abincinsa yake hankali kwance,


"Ku tashi kuzo muyi breakfast"

Momy ta faɗa tana riƙe musu hannu, kowacce ɗingishi takeyi haka suka zauna a kujera daƙyar, ko wacce kanta a sunkuye basa fatan haɗa idanu dashi ko kaɗan, bai ce komai ba, har ya gama breakfast ɗin, Jawad ya shigo yana murmishi saboda yaji sautin kukansu tun daga bakin ƙofa, shima kafin ya shigo sai da yayita tunani dan ba wani shiri sukeyi da Doctor Muzaffar ɗin ba, 

Har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da Momy, ta amsa cike da nuna kulawa kafin tace "ai inata maganarka a zuciyata ashe kana hanya?"


Jawad yace "Yah Muzaffar good morning, kafin ya amsa masa sai da ya sake kai cup ɗin tea bakinsa kana ya ajiye, yace "morning too" ya tashi yabar gurin,


Muzaffar kyakkyawa ne sosai, yanada dogon hanci gashi fari tass duk da cewar ahalin gidan duka farare ne, saboda iyayensu maza, farin Muzaffar ya fita daban, saboda har wani shining yake yi, idanuwansa suna dauke da zara zaran gashin ido kai kace mace, gashin girarsa yayi luff, sannan baƙin saje mai kyau ya kewaye daga saman bakinsa zuwa gemunsa har gefen kumatunsa,  sannan ya kasance ingarman namiji, yanada faffaɗan ƙirji tare da baƙin gashi a ƙirjinsa wanda yayi luf, hatta hannayensa da ƙafafunsa duka yanada gashi irin wanda yake fitowa maza, ya kasance mai izza da iko a ko ina sannan miskili ne na ƙarshe, ba kasafai zaga yayi dariya ba, sannan a fannin aikinsa na asibiti gwani ne, saboda yanada hazaƙa mai yawa, kuma a hakan al'umma suna alfahari dashi, yafi ƙwarewa a fannin tiyata, duk girman hospital ɗin babu kamarsa.


Gaban mirror ya ƙarisa, girgiza kai yayi, alamar kayan dake jikinsa basuyi masa ba kenan, ya fara ciresu cikin sauri kana ya buɗe drowarsa da ta kasance doguwa, kowanne guri yana cike da kaya iri-iri ga kuma agogon hannu suma gurinsu daban haka takalma belt, ɗakin yanada girma sosai,

Farar riga ya ɗauko ƴar ciki kana ya ɗauko ta waje baƙa ya saka, pants ɗinsa ya ɗauka wanda ya mugun ɗamesa sosai, ya saka kana ya saka dogon wandonsa baƙi sannan ya ɗauki hanky ya sa a gaban aljihu, kana ya ɗauki farin gilashi ya sanya, turarukansa masu tsadar gaske ya ɗauka ya feshe jikinsa, kana ya isa gurin takalminsa dark brown sai da ya fara saka farar safa kana yasa cover shoe ɗin ya fito, Momy na zaune a parlor ita da su Fateema da Diyana, yace "Momy zan wuce.."


"Allah yayi maka albarka Allah ya tsare gabanka da bayanka doctor, ina fatan Allah ya baka nasara a duk abinda kasa gaba"


Ya amsa da Amin, su Diyana kam sai susunkuyar da kai suke har ya wuce,

Koda ya isa harabar gidan mai gadi ne kawai sai driver wanda shi baya buƙatarsa, ya shiga motarsa baƙa wacce sai ƙyalli takeyi, key yayi mata, bayan an buɗe masa get ya fice, karatun Alkur'ani ya sa, a hankali yake bin karatun cikin ƙwarewa muryarsa na fitar da kowanne harafi cikin daɗin sauti, cikin ikon Allah ya iso hospital ɗin, kana yai parking a gefen jerin motocin da suke a pake, fitowa yayi cikin natsuwa ya ƙarisa ciki, anata gaishesa, yana ɗaga musu hannu har ya isa Babban office ɗinsa, yana zama, aka fara nocking, "come in.."

Ya faɗa yana ɗaga wasu sabbin files da ya gani ajiye a saman table ɗinsa wanda bai san dasu ba, Doctor Ashraf ne ya shigo shima yana cikin shiga mai shigen ta Doctor Muzaffar, bai ɗago kai ba bare yaga waye ya shigo, Sallama doctor doctor Ashraf yayi masa gami da miƙa masa hannu, Doctor Muzaffar ya miƙa masa hannu shima suka gaisa, Doctor Ashraf ya nemi guri ya zauna fuskarsa cike da damuwa, "lafiya..?"

Doctor Muzaffar ya faɗa yana ci gaba da buɗe takardar da hannunsa, "ɗazu na kiraka akan maganar wanda za'ayiwa Surgery.."

Doctor Muzaffar ya rufe takardar ya kai dubansa ga doctor Ashraf kana yace "ina jinka?"

"Gaskiya yana buƙatar taimako yana iya rasa ransa a kowanne lokaci hatsarin mota sukayi gilass ya yanke shi a cikinsa, abin babu kyan gani saboda har kayan cikinsa ana gani, min bashi taimakon.."

Doctor Muzaffar ya miƙe gami da cire rigarsa ta waje, ya rataye a jikin kujera ya ce "muje"

Suka wuce Surgery room su biyun, koda doctor Muzaffar ya ga halin da saurayin yake ciki, ya shiga ɗakin da zai sauya kaya wanda zai yi tiyata, bayan ya sauya kayan ya buƙaci kayan aiki, wanda shi a ƙa'idarsa mutum ɗaya ya yarda dashi wato doctor Ashraf, cikin hikima da ƙwarewa ya fara gabatar da aikin dukkansu suna sanye da facemask da kuma kayan aiki wanda ya rufe musu ko ina harda hand gloves a hannayensu, yana gabatar da aikin yana adu'oi koda yaushe haka tsarinsa yake,

Ƴan uwan saurayin suna zaune a waje, mamarsa ko tayi kukan tayi kukan har ta koma ta zauna a ƙasa ta mimmiƙe ƙafafu cewa take "ance min yarona bazai rayu ba mutuwa zaiyi, saboda akwai wasu ma da irin wannan hatsarin ya faru dasu basu rayu ba, wata likita ta iso inda matar take, cikin sigar lallashi tace "komai na Allah ne, ko mu kanmu da mukeyin aikin bamu da tabbacin mutum zai mutu ko zai rayu, Allah shi ya barwa kansa sani, dan haka ina mai shawartarki ba kuka ya kamata kiyi ba, adu'a ya kamata kiyi masa, wannan kukan ba zaiyi masa amfanin komai ba, ina banda ki tayarwa da wasu marasa lafiyar hankali"

Tashi matar tayi ta tafi inda pampo yake, ta ɗauki buta ta zuba ruwa kana ta fara alwala, bayan ta idar bata da abin yin sallah ɗankwalinta wankakke ne, yana riƙe a hannunta ta shimfidashi a ƙasa ta fara Sallah tana kuka...!

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post