Acikin Rayuwa Page 14 by ZAINAB BATURE - Abokiyar Hira Novels


 _Bossladieswriters_




_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q


WhatsApp Group


https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt




*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*



    

   _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ 



_ZAINAB BATURE_



   

   _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._






Page 14



Ƴar tafiya kaɗan Deen da Fahad suka yi daga parking space ɗin suka ƙaraso bakin babbar kofar shiga 6angaren, falo ne babba mai ɗauke da haɗaɗɗun kujeru royal kalar blue mai duhuwa, yadin kujerun na daga wurin da ake zama yana da zane-zanen kalolin blue mai haske da ruwan madara har da ɗan ratsin brown, akwai hadaddun labulaye masu inganci da babban carpet da ke shimfiɗe a tsakiyar kujerun saman tiles din da aka malala cikin falon, gaba daya komai na cikin falon kalolin su ya hau sun ƙawata cikinsa, akwai kayan kallo da na sauti da sauran na'urorin wuta da kayan ƙawata falo, akwai manyan hotunan ahalin gidan a wurare daban-daban, sosai falon ya haɗu tun daga kan ginin yadda ya tsaru kai ka ce ba falon tsohuwa ba. 



Zaune a saman kujera mai mazaunin mutum biyu Hajiya Binta ce tana sanye da cotton ɗin doguwar riga irin wadda ta dace da yanayin da ake ciki na zafi, don ma akwai sanyin Ac ya karaɗe ilahirin cikin falon, kanta ta saka hula, a yanayin halitta bata da jiki sosai amman kuma ba siririya can bace, kana ganinta kasan ta manyanta sosai don a shekaru za ta yi saba'in da ɗoriya amman da gani da ɗan ƙwarinta, tana da kyawun fuska doguwa mai dauke da dogon hanci da madaidaicin baki, daga yanayin jikinta yadda yake ƙem zaka fahimci ta haɗa iri da fulani duk da yanayin fatarta ba fara ce, za a iya kiranta da wankan tarwaɗa.


Idanunta dake sanye cikin glasses na akan tv tana kallo, yayin da daga gabanta saman madaidaicin center table plate ne an yanka kankana a ciki, a hankali take ɗauka da fork tana kaiwa bakin ta, daidai zata kai kankana bakinta, sallamar da ta ji an yi ya sa ta kai idanunta saitin kofar shigowa tana amsawa, tana yin tozali da waɗanda suka shigo, da sauri ta mayar da kankanar saman plate tare da washe baki ta fara ƙoƙarin miƙewa, nufo cikin falon suka yi Deen ne a gaba yana ta sakar mata faffaɗan murmushi, yana zuwa gabanta ya ware mata hannuwa ta nufe shi da sauri ya rungumo ta yana murmushi, tare da lumshe idanuwan jin daɗin ganin kakar tashi da ya ɗauki lokaci bai gani ba, ɗagowa ta yi suna kallon juna da murmushi ta kai idanuwanta kan Fahad dake tsaye a gefe yana mata murmushi,


    "Wannan wane irin zuwan bazata ne haka!" Ta faɗa tana washe baki, 


    "Yea, It's a suprise." Deen ya faɗa yana ƙoƙarin zama saman kujera tare da ita, kallon Fahad ta yi ta ce ya zauna mana ya yi tsaye, a saman kujera mai mazaunin mutum ɗaya ya zauna daga gefen su ya ɗaura duka hannuwansa a saman hannun kujeran,


     "Ɗan ball, Allah Ya yi an samu an leƙo ƙasar tamu ke nan, ai na yi zaton ma sai ka ɗan kwana biyu ka huta zaka zo nan." Ta faɗa tana ta murmushin jin dadin ganin jikan nata da ta dade bata sanya shi a idanunta ba, sai dai ta waya ko a tv in tana kallon wasan shi, amsa ya bata da ba zai iya jurewa ba yana ƙasar ya bari har sai bayan wasu kwanaki sannan zai zo ya ga sweety ɗinshi da yake missing sosai, ta washe bakin jin dadin maganar.


   "To ya ball ɗin, ai ina gani in kuna yi a tv, kana ƙoƙari sosai, ana ta ƙara ƙwarewa. Allah Ya ƙara taimakawa ya kuma tsare." A tare suka amsa mata da Amin,


   "Kun ga da kun sanar da zuwan naku da an shirya maku sosai, yanzu ba wani shiri da aka yi maku, na san dai jiya mun yi sallama da Fahad akan zai tafi tarbarka amman ba wanda ya sanar da ni yau zaku taho nan, don haka sai ku yi haƙuri duk abun da ya samu da shi za a tarbe ku." Gaba ɗaya ɗan murmushi suka yi Deen ya ce mata no problem, mai aikinta Balaraba ta shiga ƙwala ma kira, fitowa ta yi daga cikin wata ƙofa ta nufo cikin falon, ƴar babbar mace ce jikinta sanye da riga da zane na atamfa, tana fitowa idanunta suka hango Deen nan ta shiga washe baki, ƙarasowa ta yi gaban su cike da girmamawa ta ce ma hajiya gata, kafin ta faɗi mata dalilin kiran nata ta kalli Deen cikin washe baki ta yi mashi sannu da zuwa tare da gaishe da shi, ya amsa mata da ɗan murmushi, gaishe da Fahad ta yi ya ɗaga mata kai, 


    "Baƙo ne muka yi ya yi mana zuwan bazata, akawo masu abun da za su sha sai ki shirya masu abinci a table." Amsa mata ta yi da to ta juya, Deen na murmushi ya ce mata shine baƙon, hajiyar na dariya ta ce mashi eh mana mutumin da za a yi shekaru ba a gani ba ai ya zama baƙo, yar hayaniya suka fara jiyowa daga waje hajiya ta kai idonta kan ƙofar shigowa tana faɗin kamar hayaniyar mutane take ji, miƙewa Fahad ya yi ya nufi kofar ya leƙa, juyowa ya yi yana faɗin a gate ne ya san su officer ne suka sanar da zuwan Deen, hajiya ta ce ai Deen ɗin ne yana da masoya har zuwa ake ana tambayar ta yaushe zai zo, zama Fahad ya yi tare da ciro wayar shi ya yi sending kira, magana ya yi da officer ya bashi umarnin kar a bar kowa ya shigo sai Deen ya huta ko zai ga mutane, cire wayar ya yi daga kunne yana faɗin dole sai an ƙara security a gate, hajiya ta ce gaskiya don ta san yanzu mutane za su cika gidan. Bayan Balaraba ta gama shirya masu abincin ta zo ta sanar da su, Deen ya ce ma hajiya ta taso su je su ci abincin ta ce ai ita tuni ta ci abinci shiyasa ma ta zauna tana shan kankana, ya ce to ta taso su je ta bashi a baki ya yi missing hakan, tana murmushi ta miƙe, Fahad ma ya tashi, Deen ya kama hannunta suka nufi wurin table tana faɗin ita yaushe rabon ma da ta zauna cin abinci a can ta fi jin daɗin ta zauna kan kujera ta ci, balaraba ce ta yi serving na su abincin hajiya ta ce dole a ƙara sama masu wani abun su ƙara ta amsa mata da to, bayan ta gama ta bar wurin, a nutse suka fara cin abincin hajiya ta fara ba Deen a baki kamar yadda ya buƙata suna ta murmushi, lumshe ido ya yi yana tauna abincin ya furta ya yi missing ɗin wasu abinci na nan, 


"Ko dai santi kake yi?" Hajiya ta faɗa tana faffaɗan murmushi, amsa ya bata da in ma ya yi santin ba laifi bane don cook ɗinta ta iya abinci sosai,


    "Ko kana son in baka ita idan ka yi aure sai ta rinƙa dafa maku abincin, ko kuwa ka fi son na matar ka?" Hajiya ta tambaya bayan ta bashi abincin yana taunawa, Fahad ya ɗaga ido ya kalle shi da ɗan murmushi, shima murmushin kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, a ranshi ya ayyana baya ma tunanin Basma ta iya ko ruƙe tukunya balle akai ga maganar iya yin girki. Bayan sun gama cin abincin Fahad ya ce ma hajiya ta sa mai aikinta ta ɗauko masu jakunkuna a cikin mota kafin suka wuce bangaren da ɗakin da Fahad ke zama a gidan don su huta, hajiya kuma ta koma cikin falo bayan ta kirawo Balaraba ta bata umarnin ɗauko jakunkunan.




Da sallama ta shigo cikin gidan, saida ta ƙara yin wata da ɗan ɗaga murya sannan ta jiyo muryar innarsu tana amsa mata daga can cikin ɗaki, nufar ɗakin innar tasu ta yi tana haye tudun baranda lokacin innar ta fito jikinta sanye da doguwar rigar atamfa, tana ganin Salma ta saki faffaɗan murmushi tare da faɗin, "Alhamdulillahi, hasken gidanmu ya dawo."    Washe bakin jin daɗi Salma ta yi ta nufe ta da sauri tana ƙarasawa innar ta buɗe mata hannu ta faɗa jikinta, ɗagowa ta yi tana kallon innar ta ce, "Innarmu ina wuni, ya gida?" 


   "Lafiya lau tauraruwata, ya makarantar, kin dai ci abinci ko?" Tana ƴar dariya ta ɗaga mata kai, dama kullum ne idan ta dawo daga makaranta sai ta tambaye ta ta ci abinci, 


   "Je ki rage kayan jikin ki, bari na kawo maki abinci." Kai ta ɗaga mata ta wuce inda ɗakinta yake innarsu kuma ta nufi kicin, ba a jima ba Salma ta fito ta cire hijab ɗinta sai riga da wandon uniform kanta ba kallabi sai tufkar kitsonta dake naɗe, wata irin suma gare ta mai kyaun gaske daga gaban kanta ta kwanta mata luf luf, cikin barandar ta dawo lokacin innar ta iso gabanta riƙe da plate ɗin abinci ta saka mata cokali ta bata, 


"Thank you best mom." 


Murmushin daɗi innar ta saki Allah Ya sani tana tsananin jin son ƴar tata, ita ɗin kyautar Allah ce a gareta don gani take kamar bata isa ta haifi kamar ta ba, ganin tana ƙoƙarin zama akan tudun baranda ta nuna mata tabarmar dake a shimfiɗe ta ce ga wuri nan ta zauna, Salma ta ce lafiya lau bari ta zauna anan ɗin, ita kuma innar ta zauna a saman tabarmar.


    "Ban ga su Imrana ba, ba dai basu dawo ba har yanzu?" Salma ta tambaya tana kai abinci baki, 


   "A'a sun dawo, na aiki Imrana kantin Mubarak ya siyo mani ɗan tsami shine Hamza ya bishi." Kai ta gyaɗa ta sake cewa, "Halan bacci Usman ke yi?" Innar ta bata amsa da kamar ta sani, ƴar dariya Salma ta yi ta ce ai kusan kullum ne idan ta dawo daga makaranta yana bacci, tana cikin cin abincin ta ƙware ta dafe ƙirji tana tari, a ruɗe innarsu ta miƙe ta nufi hanyar kicin da sauri, dawowa ta yi hannunta riƙe da ɗan babban kofi ta kawo mata, da kanta ta bata ruwan a baki, bayan ta gama sha ta ce mata ta yi haƙuri ta manta bata haɗo mata da ruwa ba, Salma tana murmushi ta furta, "Innarmu kina ji da ni sosai, shiyasa Sagir yake kishi da ni." Dariya innar ta saki tana komawa wurin zamanta ta ce to ba dole ta ji da ita ba ƴar macen tata guda ɗaya tal,


   "Ai zaki ƙara haifo mana wata in sha Allahu." Waro ido innar ta yi, "Haihuwar lafiya kuma Salma, ai na gama ina laifin ku da na haifa, mun bar ma yara dai." 


  "Ai innarmu kema ba wani girma kika yi sosai ba, kamar ma baki haife mu ba Allah." Tana dariya ta ce ta girma mana tun da ta kai shekara arba'in.


  "Amman dai Allah innarmu baki girmi haihuwa ba, kina da kyawun jiki ba wanda zai ce kin kai shekara arba'in." Shiru innar ta yi bata ce komai ba tana yar dariya.


 "Ina mutumina man Sagir ko an shige gari." Salma ta tambaya, innar ta bata amsa da bada jimawa ba ya shigo ya ɗauki abinci ta tambayeta ta duba ɗakin su ne baya nan, Salma ta ce da ta shigo ta ga an ɗan turo ƙofar ɗakin shiyasa bata leƙa ba, innar ta ce to ba mamaki yana ciki yana bacci, wayar innarsu dake a cikin ɗaki ce ta fara yin ƙara, Salma har ta yunƙura zata je ta ɗauƙo mata innar ta dakatar da ita ta ce ta ci gaba da cin abincinta bari ta je ta ɗauka, lokacin da ta shiga ɗakin har kiran ya yanke, ɗauko wayar ta yi tana kokarin duba wanda ya kira ta, daidai tana fitowa wani kiran ya sake shigowa, zama ta yi akan tabarmar tare da ɗauka ta kai kunne, sallama ta yi kafin cike da girmamawa ta gaishe da wanda ya kira ta da fara'a har da ɗan rankwafawa, ɗan saurarawa ta yi kafin ta amsa da yaran duk suna lafiya gasu nan duk sun dawo daga makaranta.


  "Eh hajiya....to lafiya lau ba matsala za a samu dama cikin yin ta nike yanzu haka." Ɗan saurarawa ta yi kafin ta sake cewa, "Lafiya lau hajiya bakomai a basshi." Da sauri kuma ta ƙara cewa, "A'a ba a yi haka ba hajiya." Shiru ta yi tana sauraren hajiyar da ta kira ta, daga baya ta furta to zata faɗi sai an gama, daga haka suka kammala yin wayar ta cire daga kunnanta tana murmushi tare da faɗin, "Ina ruwan hajiya.." Salma dake kallon ta ta tambayi wace hajiya ce?


  "Hajiyar Ambasada ce, awara take so ta rabin tiya, wai baƙi ne suka yi mata zuwan bazata ba a shirya masu wani abincin kirki ba shine take son a haɗa masu awarar da sauce ta san za su ji daɗinta, to wai da ta tambayi kuɗin na ce ta basshi shine ta ce man to nima na bar awarar tawa." Ƴar dariya Salma ta yi, 


   "Mutumin da haka nan ma kullum cikin yi maka alkhairi yake, duk aka yi mata awara haka zata bada kuɗi fin abun da aka faɗa ai ba wani abu bane don an ce ta barshi." Innar ta faɗa tana ta murmushi, 


  "Yanzu wata za a yi mata daban?" girgiza kai innar ta yi ta ce, "Kawai bari sai a bata cikin wadda aka yi tun da sauri ake kada a 6ata mata lokaci, ke sai ki soya ragowan kawai." Kai Salma ta ɗaga, su Imrana ne suka dawo daga aiken, suna ganin yayarsu ta dawo suka nufo ta suna murmushi, ware ma hamza hannu ta yi ya faɗa jikinta yana dariya ta ce masu ya makaranta duk suka amsa, kallon Imrana dake tsaye gefe ta yi da murmushi ta ce, "Malam Imrana ya, yau akwai assignment ne?" Kai ya ɗaga mata kafin ya ce mata amman bashi da wahala zai iya ta jinjina kai. Bayan innar ta amshi saƙon aiken ta koma kan aikin awaran Salma ma ta bita don ta taya ta, innarsu na ta basshi ita da ta kwaso gajiyar makaranta kuma anjima zata fita suyan awara, Salma ta bata amsa da ai yau awaran bashi da yawa bazata gaji ba.



Zuwa bayan sallar la'asar sun gama awaran Salma har ta yi wanka, fitowa innar su ta yi daga ɗaki ta ƙwala ma Salma kira, bayan ta amsa ta ce mata ta fito ta kaima hajiya awaran ta san zuwa yanzu ta tsane, amsawa ta yi da to daga cikin ɗakin, ba a jima ba ta fito jikinta sanye da doguwar rigar material ta yafo madaidaicin baƙin gyale a saman kanta, nufar inda innarsu take a duƙe tana maida awaran cikin roba ta yi ta ce mata gata, nuna mata robar ta yi bayan ta ɗauka ta ɗago ta ce ma innar idan ta tambayi kuɗin ya zata ce mata, 


"Jeki kawai, idan ma ta tambaya ki ce kawai ban faɗi maki ba." Amsawa ta yi da to ta wuce hanyar fita. A nutse take tafiya ta rungume robar awaran a gefen cikinta, da alamun mamaki take kallon ƙofar gidan hajiyar da yake danƙam da mutane ga motar jami'an tsaro an faka daga can gefe, yayin da a bakin gate ɗin gidan jami'ai ne sun kai guda shidda sun tare mutane, a cikin ranta ta shiga raya ko lafiya? wani 6angare na zuciyarta ne ya bata ƙilan wannan ɗan majalissar ɗan hajiyan ne ya zo, tabbatar ma kanta ta yi da hakan ne ma, tsallaka titin ta yi tana ci gaba da tunanin ko ma za a barta ta shiga, da ƙyar ta samu kaiwa bakin gate ɗin inda jami'an suke, wani officer ne ya tambaye ta ya aka yi? A ɗarare ta ce mashi aiko ta aka yi ta kawo ma hajiya saƙo, tambayar miye acikin robar ya yi saboda a rufe take, hannu ta kai ta cire marfin ya gani ya ce ta wuce, wani a cikin sauran officers ɗin ya buɗe mata ƙaramar kofa ta wuce, tana shiga nan ma cikin harabar wasu dandazon mutanen ne daga can gefen parking space sun kewaye wurin sai hargowa suke yi, nufar shiga cikin gidan ta yi tana yi tana waiwayen mutanen har ta isa ƙofa ta shige, falon wayam ba kowa sai tv dake ta aiki, shiga ta yi ta tsaya daga tsakiyar falon ta fara yin sallama, sai da ta yi sau ukku sannan ta ji an amsa mata, Balaraba ce ta fito tana amsawa, tana ganin mai yin sallamar ta nufo cikin falon da murmushi, "Salma ke ce?" Tana murmushi ta amsa mata, "Eh Aunty Balaraba, ina wuni." Amsa mata ta yi da lafiya lau ta tambayeta ya makaranta har an dawo ta ce eh, faɗi mata saƙon da aka aiko ta ta yi Balarabar ta ce har an kawo awaran ke nan to bari ta yi ma hajiya magana ta nuna mata kujera ta ce ta zauna, ba a jima ba ta fito daga bangaren hajiyan ta ce mata gata nan zuwa, ba a ɗauki lokaci ba hajiya ta fito ta nufo cikin falon, 


   "Salma ce?" Ta tambaya da murmushi tana ƙarasowa, miƙewa Salma ta yi ta amsa da eh tare da gaishe da hajiya, amsa mata ta yi ta tambaye ta ya karatu, ganin ta miƙe ta ce mata ta koma ta zauna, 


     "Wai nikam hayaniyar mi cece nike ji tun a cikin ɗaki sama sama?" Hajiya da har zata zauna ta dakata tana tambayar Balaraba,


    "Mutane ne da yawa a can wurin ajiye motoci, a waje ma wurin gate akwai wasu sosai ofisoshi sun hana su shigowa, nima na ɗauka baza su barni ma in shigo ba." Salma ce ta faɗa, nufar hanyar babbar window hajiya ta yi ta leƙo wajen, jinjina kai ta hau yi kafin ta juyo ta dawo tana faɗin, "Mutanen Deeni ne. Wannan ma ai har ya fi mahaifin shi tara jama'a. Su dai maza Allah Ya yi su da jarabar son ƙwallo." Dawowa ta yi ta zauna kan kujera tare da kallon Balaraba ta ce mata ta ɗauki awaran ta je ta fara aikinta ta amsa da to bayan ta ɗauka ta tafi, 


    "Duk ya ƴan'uwan naki." Hajiya ta tambaya tana kallonta da murmushi, "Suna nan lafiya lau." Ta amsa itama da murmushi,


   "Nawa ne ta ce kuɗin?" Amsa ta bata da bata faɗi mata ba kawai ta ce ta kawo, ɗan kwa6e baki hajiya ta yi bata ce komai, gaba ɗaya maida hankalin su suka yi akan tv suka ci gaba da yin kallo a tare, after some minutes suka ji an yi sallama, a tare suka kai idanun su wurin ƙofa, Deen ne ya shigo jikin shi ya sauya shigar da ya zo da ita zuwa farar jallabiya mai gajeran hannu ta fito da suffar shi ta ƙaƙƙarfa, cikin falon ya nufo ya nufi can gefen hajiya saman kujera ya faɗa ya kai hannu ya shafi goshin shi tare da huro iska waje, hajiya dake kallon shi tana murmushi ta ce halan mutanen na shi sun tara mashi gajiya, amsa mata ya yi da wallahi ai bai ma iya gama ganin su ba ya gaji sai wani lokacin, tun lokacin da ya shigo Salma ta kafe shi da ido tana bin shi da kallon al'ajabi, tabbas in dai ba ƙarya idanunta ke nuna mata ba wannan shine mutumin nan na ɗazu, abun da ya ƙara tabbatar mata da hakan sumar kan shi duk da a yanzu ba a fake take ba ya sake ta ta kwanto a wuyanshi, sai kuma muryarsa da bata tunanin zata ƙara jin irinta ba tare da gane ba don ta fita daban, sam bai kalle ta ba bayan ya gama yi ma hajiya magana wayar shi ya shiga latsawa, Fahad ne ya shigo da sallama shima ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt dama bayan sun yi wanka ne suka fita yin sallar la'asar da lokacin ta ya yi shine fa mutane suka hana su shigowa ciki sai yanzu, wani iri faɗuwa gaban Salma ya shiga yi lokacin da ta kallo mai shigowar idanunta suka yi tozali da Fahad suka haɗa ido, da sauri ta janye idanun nata ta koma kallon ƙasa, cikin falon ya shigo ya nufi kujera ya zauna hajiya ta ce mashi an shigo ya ɗaga mata kai, bin Salma ya yi da kallo tun da ya shigo suka haɗa ido ya so ya gane ta, a hankali ta ɗago zata saci kallon shi aikuwa karaf idanunsu suka haɗu, kasa janye idanun nata ta yi duk ta bi ta kama kanta ta shiga kikkafta idanu yayin da bugun zuciyarta ya tsananta, ji take kamar ta tashi ta tafi amman ta rasa ƙwarin gwuiwar yin hakan, ganin irin kallon da yake jefa mata yasa ta sauke idanunta da sauri tana yamutsa yatsun hannunta,


   "What the hell are you doing here?!" Kallon Fahad hajiya ta yi jin yayi magana duk da bata fahimci mi ya ce ba, ce mashi ta yi magana yake ne, ganin direction ɗin da yake kallo yasa ta juya ta kai idonta kan Salma da itama shi take kallon tana ɗan motsa baki, kasa fahimtar kallon mi suke ma juna hajiya ta yi ta sake kallon Fahad, a daidai lokacin ya miƙe ya nufo wurin da Salma take ta miƙe da sauri, bayan ya tsaya daga gabanta, fuska a ɗaure tamkar bai ta6a yin dariya ba ya sake furta, "Mi ya kawo nan!" Cikin yar tsawa ya yi maganar, hakan ne ya jawo hankalin Deen da ke latsa waya ya maido hankalin shi kan su, 


    "Baki ji maganan da nake maki ba, uban me ya kawo ki gidan nan??" Jikinta ne ya shiga yin rawa don a fusace yake mata maganar, cikin rawar murya ta ce, "D..dama aiko ni aka yi wurin hajiya..." 


  "Get out of this house! Idan na sake ganin ki a gidan nan sai na tattaka ki." Da sauri ta juya zata tafi hajiya da gaba ɗaya ta ruɗe da ganin abun da ke faruwa da sauri ta miƙe tana faɗin, "Fahad wai mike faruwa ne? Ka san Salma ne? Mi ya haɗa ka da ita?" Shiru bai bata amsa ba idon shi na kan Salma da ta fara tafiya da  sauri za ta bar falon,


   "Ke Salma dakata, zo nan!" Hajiya ta faɗa, tsayawa ta yi ta juyo a ɗarare ta dawo ta tsaya daga gaban su, tambayar ta ta yi miya haɗa ta da shi, motsa baki ta shiga yi ta kasa cewa komai, kawai sai gani hajiya ta yi Fahad ɗin ya kai hannu cikin zafin nama zai wanka ma Salma marin da yayi niyya yi ɗazun, da sauri Salma ta goce duk da haka saida ya ɗan same ta, ruɗewa ta yi ta fashe da kuka gyalenta ya zame daga saman kanta, salati hajiya ta rafka tana ce ma Fahad mike damun shi? Mi ta yi mashi wai?" 


   "Hajiya just ta bar gidan nan yanzu, and I don't want to see her again, idan ba haka ba yanzun nan zan sa officers su kama ta su je su kulle ta." A zuciye ya yi maganar, wani salatin hajiya ta ƙara zabgawa hakan ya ja hankalin Balaraba dake a cikin kicin ta fito bakin ƙofa tana kallon abun da ke faruwa, yunƙurin barin falon Salma ta sake yi hajiyar ta dakatar da ita tana tambayar wai mi ya haɗa su,


   "Fahad wai bazaka buɗe baki ka gaya mani abun da ya haɗa ku bane? A ina ka san Salma kuma mi ta yi maka ne? Wuri na fa aka aiko ta." Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya tafi, hajiya da Balaraba suka bi shi da ido cike da al'ajabi har ya shige ciki inda ɗakuna suke, maido kallon ta ta yi kan Salma ta matsa tare da dafa ta ta ce ta faɗi mata mi ya haɗa su, sam ta kasa magana sai kuka take yi tare da ƴar ajiyar zuciya, hajiya ta fahimci jin nauyin faɗi mata take yi, kallon inda Deen yake zaune yana kallon duk abun da ke faruwa ta yi ta ce, "Ko ka san abun da ya haɗa su ne?" Ɗan yamutsa fuska ya yi ya ce ba komai ya sani ba amman ita yarinyan ai ta san mi ya haɗa ta da shi ta faɗi mata mana, zaunar da Salma ta yi saman kujera mai mazaunin mutum biyu itama hajiya ta zauna, hannunta akan kafaɗarta cikin sigar rarrashi ta ce mata kar ta ji komai ta faɗi mata abun da ya haɗa su zata fahimta, dakatawa ta yi da murzar idon da take yi da gyalenta tana ci gaba da yin kukan cikin zuciya tana kikkafta ido, a hankali take bin mutanen cikin falon da kallo har da Balaraba dake a can bakin kicin, tsaida idonta ta yi akan Deen daidai lokacin ya yi mata kallon ƙasan ido, da sauri ta kauda idonta don sai ta ga kamar ya harare ta, "Ina jin ki Salma.." Hajiya ta faɗa,


    Cikin rawar murya ta fara magana, "D...dama ɗazun ne lokacin da na dawo daga makaranta...shi..ne zan tsallaka titi na hango motar su can nesa, to..na yi tunanin har zan tsallaka basu ƙaraso ba..shine suka kusa buge ni da mota, to...shine ya leƙo yana mani magana...shi..ne..." Kasa ƙarasawa ta yi ta ci gaba da yin ajiyar zuciya tana murzar ido, hajiya ta so ta fahimci sa6ani ne ya shiga tsakanin su da abun ya faru shiyasa Salma ta kasa faɗi mata, miƙewa ta yi ta ce mata kada ta tafi ta jira tana zuwa daga haka ta nufi cikin hanyar da Fahad ɗin ya bi, gaban Salma ne ya ci gaba da bugu don ta gane wurin shi hajiyar zata je kuma ta san zai iya faɗi mata komai, ƙasa ƙasa ta ci gaba da yin kukan gyalenta a fuska,


  

  "Kina ma wa kuka? Ko wani ya sa ki ne ki yi mashi rashin kunyan?" Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Deen ya faɗi hakan, cire gyalen ta yi daga fuskarta ta kalle shi da jiƙaƙƙun idanuwa, ɗage mata gira ya yi ya sake cewa, "You caused it, so what's the point of crying now?" 


 Cikin muryar kuka ta ce, "Ai ni ba rashin kunya na yi mashi ba wllh, tun farko saida na bashi haƙuri amman shine ya ce mani dabba mara hankali, kuma farko ni bance mashi komai ba shine ya sake ce mani mara kunya..." Shiru ta yi tana kikkafta ido tana ɗan nishin kuka, 



    "Sai kika nuna mashi ke mara kunyan ne?" Ya ɗage mata gira, girgiza masa kai ta yi tana motsa baki, ta sa gyale tana goge ƙwallan da suka zubo mata ba tare da ta ce komai ba, ɗan ta6e baki ya yi ya ci gaba da ta6a wayan shi.......





*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post