Sha'awada Jaraba Page 1&2 By Mom Islam - Abokiyar Hira Novels


Mom Islam: 💋💋💋

SHA'AWA DA JARABA

    (Love and Romantic story)

          💋💋💋

          Mom Islam 

Page 1-2


Gidane babba ƙerarre wanda ya kasance irin family house ɗinnan, kasancewar Akwai part part a cikin gidan,

Amma Babban parlor guda ɗaya ne,  wanda yake part ɗin Alhaji Basheer, duka ragowar part ɗin sunada parlon sai dai madaidaita ne basu da girman na, Alhaji Basheer shine babba, Alhaji Mustapha kuma ya kasance ƙani gareshi, ubansu ɗaya sun taso cikin so da ƙaunar junansu, kasancewar su biyu Allah ya bawa iyayayensu, bayan rasuwar mahaifiyar Alhaji Mustapha, Alhaji Mustapha ya dawo gurin mahaifiyar Alhaji Basheer, kwatsam Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa, sakamakon haɗarin mota, dukkansu biyun sun koka sosai da rashin gatansu wato mahaifinsu, daga nan ragamar kula dasu ta koma gurin mahaifiyar Alhaji Basheer, Hajiya Sa'adatu ta kasance mace mai adalci da sanin ya kamata, hakan yasa bata banban tasu, batayiwa wannan abu bata yiwa wancan ba, sun samu kulawa da kuma tsaftatacciyar tarbiyya gami da sana'a mai inganci, dukkansu sana'arsu iri ɗaya ce, wato sunada gidajen bredi, irin na zamani wanda ake sarrafa breadi da na'ura.


Alhaji Basheer yanada mata ɗaya, Hajiya Zulaiha, shima Alhji Mustapha matarsa ɗaya Hajiya Mariya, dukkansu sunje ƙasa mai Tsarki bayan aurensu, kasancewar a rana ɗaya aka ɗaura musu aure.


Zaune suke a babban parlon dake part ɗin Alhaji Basheer, parlon ya kasance haɗaɗe mai ɗauke da mayan manyan Sofa farare masu taushi, acan gefe kuwa Dinning area ne wanda aka yane shi da labule mai shara-shara irin na zamani, a taƙaice dai parlon haɗaɗe ne Masha Allah,


Musu sukeyi akan wani Film da ake haskawa, inda musun nasu yasa suke ta ɗaga murya har parlon ya kaure da hayaniya, wanda bai sani ba idan ya shigo zai ɗauka faɗa sukeyi, 


"Aslamu alaikum" 

Wani matashin saurayi wanda a shekaru zai yi 35yrs ya shigo cikin takunsa na ƙasaita kai kace Basarake, lokaci ɗaya parlon ya ɗauki shiru, kowanne ya ɗan firgita, sai ƙoƙarin miƙa gaisuwa suke suna cewa "Barka da safiya yah Muzaffar..."


Sai da ya ƙara taku ɗaya zuwa biyu kafin ya amsa da cewa "Barka" inda kasan wani mai koyon magana.


Da ɗaya da biyu suka zame suka barshi shi kaɗai a parlon, Best Smart watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kalla, kafin yaciro wayarsa dake gaban aljihun rigarsa, ajiye wayar yayi a hannun Sofa ya jingina kansa da jikin lallausar kujerar ya ɗaga kansa sama, wayarsa ta fara ringing, hannunsa yakai ya ɗauka kana ya duba mai kiran "Doctor Ashraf.."

Ya faɗa a fili yana ci gaba da kallon screen ɗin wayar da sunan Doctor Ashraf ɗin yake yawo,  amsa kiran yayi, kana yakai wayar kunnensa, kafin yayi magana daga can ɓangaren doctor Ashraf yace "Doctor Muzaffar Dan Allah kazo hospital yanzu wlhi akwai wata babbar matsala"

Ba tare da yaji wani ɗarrr ba, Doctor Muzaffar yace "matsala kamar ta me?"


Doctor Ashraf yace "kaidai kazo Please Emergency Surgery"


Dajin haka yace "naji zanyi breakfast tukunna"


Ya katse kiran.

Hajiya Zulaiha, wato mahaifiyarsa, fitowa  tayi daga kitchen hannunta riƙe da babban tray wanda yake ɗauke da warmers har guda uku, ta kawo Dinning area ta ajiye, kana ta dawo parlor tana dubansa, kafin tayi magana cikin ɗaga murya ya fara kiran "Diyana..Fateema..kuna ina?"

Da gudu suka taho suka durƙusa a gabansa ko wacce ƙirjinta na bugawa, sukace "gamu".


"Wato baku da hankali da tausayi, Momy ce zata yi muku breakfast sannan ta kai dinning ta ajiye, sannan ku gama cin abincin ta kwashe takai kitchen ta wanke, ita baiwarku ce?" Kowacce kanta na a sunkuye jikinsu na ɓari suke girgiza masa kai, cikin ɗaga murya yace "kowacce tayi tsallen kwaɗo daga yanzu har zuwa lokacin da zan gama breakfast"


Momy ta hangame baki tana dubansa, saboda tasan ko tayi magana ranta ne zai ɓaci ba saurararta zaiyi ba, wucewa tayi ta barsu a gurin, kowacce sai zazzare idanu takeyi, gashi parlon dogo ne,


Tsawar daya yi musu ne yasa ko wacce ta fara yi,  Diyana tanada shekaru 17yrs Fateema kuma 18yrs, suka fara tsallen kwaɗo idanunsu yayi jajir gasu farare sai shan majina sukeyi...!

Kuna ganin muci gaba...?

Mom Islam 08141799224

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post