Masarautar Alhamra Page 33 Compl

 

Masarautar Alhamra Page 33 Compl

*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* 


_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_


✍🏽 By ASMEETAH WRITER

~Hasken Jajirtattu~



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️


   ```JARUMAI WRITERS TEAM``` 


▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇

🔗 WhatsApp Channel:

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


📚 ArewaPen:

https://arewapen.com/u/asmeetahwriter


📖 Wattpad:

https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter


📲 Contact:

09065443871


📅 FARA TURA BOOK:

🔥 01 — 01 — 2026 🔥


📘 BOOK ONE 

           ```MATAKIN FARKO``` 


CHAPTER 3️⃣3️⃣ 


 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*




Bayan ya dawo daga masallacin dake can gefen babban filin fadarsa, iskar asuba mai sanyi tana bugun fuskarsa. Chief Onyx ya shigo babban falon inda ya tarar da Gely, PA ɗinsa kuma tsararriyar Robot mai basira, tana hidimar haɗa karin kumallo cikin natsuwa..


​“Good morning, Boss,” Gely ta gaishe shi da muryarta mai sanyi da madaidaicin sauti.

​Chief ya amsa a nutse, ya zare agogonsa na alfarma ya ajiye, sannan ya tambaya,  “Shin Ching-Ching ta tashi ta yi sallah?”


​Gely ta gyara tsayuwa, “Eh Boss, ta tashi ta yi sallah, amma ta koma bacci saboda yanayin sanyin safiyar.”


​Chief ya ɗan yamutsa fuska, ya bayyana asalin Boss ɗin nasa...

 “Jeki tashe ta yanzun nan. Yau za ta fara zuwa makarantar The Royal Valorant Academy... Bayan kin tashe ta, ki zo ki karɓi jakunkunanta da sabbin kayan makaranta da litattafan da na haɗa mata. Komai ya zama ready.”

​Yana hawa saman ɗakinsa bai fi mintuna biyar ba, agogonsa mai tsadar gaske dake ɗauke da fasahar zamani ya fara girgiza a hannunsa. Gely ce ke kiransa ta na’urar sadarwa..


​“Boss... akwai matsala. Ching-Ching ba ta da lafiya.”


​A ruɗe Chief ya sauƙo ƙasa, har yana kusa tuntuɓe a kan matakala. Ya garzaya zuwa ɗakin Ching-Ching, ya tarar da ita kwance, duk da sanyin A.C  dake ratsa ɗakin, jikinta duk ya jike da gumin wahala..


​“Mene ne ya faru da ita?” Chief ya tambayi Gely cikin murya dake nuna damuwa..


​Gely ta duba bayanan dake cikin na’urarta ta lafiya, ta ce,  “Na gama bincikar jikinta. Mararta ce ke mata ciwo sakamakon First Period da za ta fara. Yau ne karon farko da ta zama budurwa.”


​Chief ya zaro ido, a ɗan ruɗe... “Kina nufin... yanzu jini yana kan zuba mata ne?”


​Gely ta yi ɗan murmushi na inji. “Wannan ba abin damuwa ba ne Boss, dabi’ar kowace mace ce. Shekarunta sun kai yanzu. Abin da ake buƙata shi ne abin tare jinin don kada ta ɓata jikinta...”


​“Okay... Stay here!” Chief ya juya da sauri ya fita, ya shiga motarsa ya nufi babban shago cikin gaggawa..

​Bayan ya dawo, ya miƙa wa Gely wata baƙar leda. Gely ta buɗe, ta kalli abin ciki sannan ta kalli Chief da mamaki..


​“Boss... wannan ai Pampers ne na jarirai, na tarewa yara kashi ne... Wancan kuma Pad ne na mata.”


​Chief ya shafa kansa cikin jin kunya. “Yanzu dai ya jikinta? Wancan kiyi amfani da wanda ya dace.”

​Kafin Gely ta kai ga amsawa, sai suka ga Ching-Ching ta buɗe ido tana rarraba su...

 “Fitsari zan yi...” ta faɗa cikin murya mai rauni, ta miƙe ta shiga toilet...


​Shiru na ɗan lokaci... can kuma sai aka ji wani firgitaraccen ihu! “WAYYOOO!”


​Ta fito a guje tana ihu, fuskarta cike da firgici. Chief ya cafko ta da sauri kafin ta fice daga ɗakin, ta ƙanƙame shi tana kuka da ƙarfi..


​“Wayyo Allah, Uncle! Na mutu na lalace! Jini! Jini! Wallahi na ji ciwo a ɗuwawu naaa! Wani ya soka min wuƙa ban sani ba!”


​Ta cigaba da kwarara surutai, tana ƙara matse Chief, fuskarta ta yi ja saboda tsoro. Chief Onyx wanda damuwa ta lulluɓe shi, sai da ya ji dariya na neman kufce masa saboda jin abin da ta faɗa..


​“Yi shiru, babu wanda ya soke ki,” ya faɗa yana ƙoƙarin danne dariyarsa, yayin da yake shafa kanta don rarrashi. “Ƙaruwa kika yi, kin zama budurwa.”


​“A’a Uncle! Jini ne fa! Na mutu, kaga yadda yake zuba!” ta ƙara sa da ihu, tana ɓuya a ƙirjinsa.



Bayan an gama wannan guje-guje na firgici, Chief Onyx ya samu nasarar dawo da Ching-Ching kan gado. Ya zauna a gefenta, ya sa hannunsa duka biyu ya kamo nata, yana kallon yadda take kuka tana shashsheka kamar wadda aka yi wa mutuwa...


​“Yi shiru na ce miki, babu wani abin tsoro,” Chief ya faɗa cikin muryar lallashi, yana ƙoƙarin danne dariyar da take taso masa duk lokacin da ta ambaci ciwon ɗuwawu...

​Chief Onyx ya gyara zama, ya dube ta da idon gaske don ya yi amfani da damar ya ba ta ilimin zamantakewa, amma cikin sigar tsoratarwa irin ta manya...


​YA ce murya ƙasa-ƙasa 

“Saurara min nan Ching-Ching. Daga yau fa kin zama babbar mace, ba yarinya ba. Kuma ki buɗe kunnenki da kyau, daga yau, kada ki kuskura ki bar wani namiji ya taɓa ki. Ko hannunki namiji ya riƙe, to fa za ki iya ɗaukar ciki nan take!”


​Ching-Ching ta zaro ido, ta daina kukan lokaci guda. Ta kalli hannunta ta kalli na Chief dake riƙe da nata.


​Sai kuma ta turo baki ta ce, 

 “Da gaske Uncle? Yanzu kenan zan iya haihuwa? Amma gaskiya ni bana son jinin nan, jini ne he kace wanda aka yanka akuya!”


​Ta ƙara sautin kukan, “Kaiii nifa ban yarda ba! Dole wani ne ya zo ya caka min wuƙa a wurin fitsarina don mugunta. Ko ma hala Gely ce ta soka min!”


​Gely, wadda ke tsaye kamar gunki a gefe, ta juya kanta zuwa ga Ching-Ching, idanunsa na Robot suna ba da hasken bayani, 

 "Ni ban taɓa taɓa ki da wani abu mai kaifi ba, Shugaba Ching-Ching... Wannan tsari ne na halitta.”


​Ching-Ching ta harare ta duk da yanzu suna shiri, ta ce,  “Rufe min baki! Ke dake da hannun ƙarfe ai ba kya jini. Ni dai Uncle kaji na gaya maka, wanda ya yi min wannan muguntar sai na rama...”

​Chief Onyx ya girgiza kai, ya da fa kuncinsa yana kallon wannan dambarwar..


​DAga bisani ya ce, 

  “Ban da surutu. Sannan kuma tun da jinin nan ya zo, duk abin da kika yi na rashin jin magana, za a fara rubuta miki zunubi. Mala’iku sun shirya takarda yanzu...”


​Ching-Ching ta tsaya cak, ta yi tunani na daƙiƙa biyar. Sai kuma ta washe haƙora, ta matso kusa da Chief har tana gogar hancinsa...


​“To Uncle, tunda kace idan namiji ya taɓa ni zan yi ciki... yanzu kai ai namiji ne, kuma kana ta riƙe ni. Kenan yanzu zan haifi baby Chief?”


​Chief Onyx ya ji gabansa ya faɗi, ya ji kamar ya tashi ya gudu... 

“A’a! Ni... ni daban ne! Ni ai Uncle ɗinki ne.”


​Ta ce,  “Hmm! Uncle ne ko baban baby ne? To ni dai gaskiya idan zan haihu, ba zan haifi baby boy ba, sai baby girl kamar niiii...”


​Chief ya tashi tsaye yana gumi, ya kalli Gely..

. “Gely, koya mata yadda za ta yi amfani da kayan da na kawo. Ni dai zan fita, kafin wannan yarinyar ta haukatani da maganganunta.”


​Yana fita, ya ji ihun Ching-Ching daga ciki.. “Uncle! Zo ka tafi da Pampers ɗinka, ni ba jaririya ba ce!”..


Washegari da komai ya lafa...


Chief ya tambayi Gely game da school ɗinta tinda tana wannan yanayin...


Gely ta sanar cewa "ba matsala zata iya zuwa, saboda da haka mata suke rayuwa a cikin jini kuma babu mai gane wa..."


A lokacin ya sanar da a shirya ta..

Bayan wasu mintuna Ching Ching ta wankanta tayi brush...


Tana zaune a gaban babban madubin dake dakinta, Gely ta gama baje basirarta na Robot. Ta gyara mata gashinta, ta yi masa wani irin lallausan design a gaba wanda ya fito da tsantsar kyan fuskarta. Ta saka mata kyakkyawan uniform ɗin The Royal Valorant Academy, riga fara mai dogon hannu, da tie dake wuyanta, sannan aka dora mata ɗan short riga mai kalar navy blue da ya tsaya dai-dai gwiwarta...


A karshe, aka dora mata hular beret mai launin rigar  din. Ching-Ching ta goya jakar makarantarta a baya, ta fito kyakkyawa kamar balarabiya, sai dai tana turo baki alamar ba ta saba da wannan shigar ba...


Suna saukowa falon a jere ita da Gely, Chief Onyx ya dago kansa daga jaridar da yake karantawa. Ya tsaya turus, idonsa ya kasa ɗaukuwa daga kan Ching-Ching. Gaba daya kyan da tayi yanzu ya ninka na baya sau goma

Duk da kyan da ta yi, abu daya ne ya sa Chief ya dafe kai....Tafiyarta.


Ching-Ching ta fara takowa, amma kafafunta a ware suke, ba sa haɗuwa. Tana tafiyar ne kamar agwagwa, tana wani nishi-nishi...


Cikin mamaki ya tambaye ta  “Meye haka kuma? Wane irin tafiya ce wannan? Kin kakkarya ƙafafun ne?”


Ching-Ching ta tsaya tana hararar sa daga baki har hanci, 

 “Yooo! Baka ga abinda aka danna min a gaban mafitsara na bane? Taya zan iya tafiya normal kuma?”


Chief ya ce,  “Kowace mace idan tana cikin wannan yanayin ai tana sa Pad, kuma tana tafiyarta normal ba tare da kowa ya gane ba. Maza gyara tafiyar nan!”


Tana turo baki ta ce, 

“A’a Uncle! Ni nawa daban ne, ƙarami ne ai! Kuma haka kawai sai in bari wurin ya yi ta ji min ciwo a cinyoyina? Ni dai haka zan tafi, idan kaga dama ma ka turo ni a wheel-chair!”


Chief ya girgiza kai, ya san idan ya tsaya ja-inja da ita to ba za su bar gidan ba yau. “Muje to. Idan aka fara miki dariya a makarantar ai dole zaki gyara da kanki.”


Ching-Ching ta kalli kanta a madubin falon, ta kalli rigar din dake iya gwiwarta, sai kuma ta danna tsalle ta dire...

“Yanzu saboda Allah a haka zan fita tsargal-tsargal kamar arniya? Dubi rigar a iya gwiwa ta fa! Babu ko mayafi, gashina a fili? Anya Uncle ba kana so in shiga wuta ba ne?”


Yana ƙoƙarin tura ta waje tare da faɗin “Muje makarantar zaki ga wasu ma babu hular, gashin ma a hargitse yake. Haka Uniform din yake, babu mayafi a ciki.”


Ta ce,  “Tabbb! Ni dai gaskiya Uncle kawai ka mayar da ni arniya. Idan na haɗu da mala’iku zan ce kai ne ka ba ni wannan kayan.”


Haka suka fita suna dambarwa, tana tafiyarta ta agwagwa tana murguda baki. Suka shiga cikin wata zafafan bakar mota, Gely ta zauna a gefen drive wanda ya kasance bodyguard ne mai tuƙi, ita kuma tana lura da dukkan motsinsu..


A bayansu kuma, wasu zafafan bakaken motoci guda hudu ne shake da Bodyguards dake dauke da makamai suka mara musu baya. Ayarin motocin ya dauki hanyar makarantar dalar Amurka, inda kowa ke kallon wannan tafiya ta ban-mamaki...


Ayarin motocin Chief Onyx ya tsaya kyam a kofar makarantar. Bodyguards suka fito da sauri suka shimfida Red Carpet..


 Daliban makarantar, wadanda dukansu 'ya'yan sarakuna ne da attajirai, suka tsaya cirko-cirko suna jiran ganin wace Gimbiya  ce za ta fito...


Chief Onyx ya fito cikin taƙama, sannan ya miƙa hannu ya taimaka wa Ching-Ching ta fito...


 ta turo kafa ɗaya waje... sannan ɗayan ya biyo baya... nan take ta fara tafiyar nan tata ta Agwagwa, kafafu a ware, tana rarraba ido...


Ganin yadda kyakkyawar yarinyar nan take tafiya kamar wadda ta koyo a gidan kaji, sai wasu gungun 'yan mata dalibai suka kwashe da dariya..


“Oh my God! Dubi tafiyarta! Is she a duck?” daya daga cikinsu ta fada tana nunawa..


Ching-Ching ta tsaya cak, ta murguda baki har ya kusa taɓa hancinta...

   “Uban wa kuke yi wa dariya? Kun taɓa ganin inda agwagwa ta saka riga da tie ne? To jini nake yi, taya zan haɗe ƙafa? Arna kawai!”


Chief Onyx ya runtse ido, ya ji kamar ya nutse a ƙasa don kunya. Gely kuwa tana gefe tana daukar bayanan yadda bugun zuciyar Chief yake karuwa saboda ɓacin rai.. 


A daidai wannan lokacin, wani kyakkyawan matashi, Yarima Leonardo daga daular kasar Italiya, wanda ya ga abin da yake faruwa, ya taho da sauri don nuna Gentlemanliness...


Yana zuwa, bai san asalin matsalar ba, ya ɗauka ko tawayar ƙafa take da shi. Ya miƙa hannu da sauri ya riƙo damtsen hannunta don ya taimaka mata ta daidaita tafiyar...


“Easy, Princess. Let me help you...” Leonardo ya faɗa cikin muryarsa mai daɗi...


Ching-Ching ta kalli hannunsa dake kan nata, sannan ta kalli Chief Onyx. Nan take idanunta suka zaro, ta fara tsalle tana ihu kamar wadda aka zare wa rai!...


  *“WAYYO UNCLE! KAGA NAMUJI YA TAƁA NI!.. NA SHIGA UKU, NA MUTU! UNCLE KAGA YA RIƘE MIN HANNU, ZAN YI CIKI! GOBE ZAN HAIHU!”*


Leonardo ya saki hannunta kamar ya taɓa wuta, ya koma baya yana zare ido..


 “What? No! I was just helping!”


Ching-Ching ta je ta taɓe a bayan Chief Onyx da gudu  tana kuka tana nuna Leonardo...


 “Mugu! Azzalumi! Kaga yadda yake kallo na? Uncle maza mu tafi asibiti a cire cikin nan tun bai girma ba! Shikenan na zama uwa ba tare da na gama karatu ba!”


Chief ya juya ya kalli Leonardo da wani irin kallo na kisa. Kishi, kunya, da fushi suka haɗu suka yi masa dumu-dumu a zuciya..

Muryarsa tana rawa saboda bacin rai..


 “Leonardo... idan baka ɓace daga nan ba yanzun nan, zan sa a rufe makarantar nan yau! Kuma ke ya kalli Ching-Ching... maza shiga ciki kafin in haɗiye ki!”


Ching-Ching tana turo baki. cikin shagwaɓa ta ce, 

“Ba zan shiga ba! Taya zan shiga ina da juna-biyu? Uncle ka taɓa ganin inda mai ciki take zuwa aji ɗaya?”


Masu kallo suka sake fashewa da dariya,. Chief Onyx ya cafko damtsenta ya fara jan ta zuwa cikin makarantar, tana tafiyar agwagwa tana kukan karyar cewa cikinta ya fara girma...


Bayan wannan dambarwar ta waje, Chief Onyx ya rasa yadda zai yi. Ching-Ching ta ƙi zama, ta riƙe masa riga tana kuka tana cewa cikinta na ciwo tun bayan da Yarima Leonardo ya taɓa mata hannu..


Dole Chief Onyx, babban mutum mai kwarjini, ya zauna a kan wata ƴar ƙaramar kujerar ɗalibi a gefenta. Ya haɗe rai, idanunsa a waje kamar zai cinye kowa, yayin da sauran ɗaliban ajin kowanne ya rufe baki yana dariya ƙasa-ƙasa...


Mr. Sterling wato malamin da yake koyar da ajin cikin rawar murya,  


"Uhm... Welcome, Chief. Please, we are about to start the lesson."


Duk ajin ya yi tsit, banda mutum ɗaya, wato Ching-Ching..

 Ta fara rarraba ido tana kallon kowa...


"Uncle, kalli waccan yarinyar, gashinta kamar na dokinmu na gida. Ke, baki da mai ne? Kuma Uncle, kalli malamin nan, me ya sa kansa yake sheƙi kamar kwanon Gely? Ko shima robot ne?"


Chief cikin raɗa yana daka mata tsawa,  "Ching-Ching! Yi shiru! Kowa ya yi tsit ke ce kawai kike wannan surutun kamar an kunna rediyo!"


Ching-Ching ta turo baki 

 "Yoo! Taya zan yi shiru? Ai shi ma malamin nan surutu yake yi. Kuma nifa ba zan iya yin wannan rubutun ba, ciki gare ni fa! Uncle ka faɗa masa cewa mai juna-biyu hutu take yi, ba ta aiki!"


Duk yadda Chief yake ƙoƙarin danne fushinsa, sai da ya kai bango. Musamman ma lokacin da Mr. Sterling ya tambayi ajin..


 "Who can tell me the capital of France?"

Ching-Ching ta ɗaga hannu tana tsalle, kafin ma malamin ya bata dama, ta fara..


"Capital of France? Ai na sani! Shi ne inda Uncle ya sayo min kayan wasa, sunan wurin Shoprite! Kuma ma, me ya sa kake tambayar mu? Kai baka sani ba ne?"


Ajin ya kaure da dariya. Chief Onyx ya miƙe tsaye da sauri, fuskarsa ta yi ja wur. Ya cika ya yi fam kamar zai fashe..


"Ya isa! Na gaji! I'm done!"


Ya juya ya kalli Gely dake tsaye a ƙofa. "Gely, ki tsaya a nan! Idan ta ƙara surutu ki rufe mata baki da tape! Ni kam na tafi kafin hawan jini ya kashe ni!"


Chief ya fice a fusace, yana huci kamar zaki. Ching-Ching ta turo baki, ta bi bayansa da ihu..


"Uncle! Ka tafi ka bar ni da juna-biyun wani?..."


Malamin ya kalle ta cikin bacin rai, 

"Ching-Ching, please sit down and write."


Ching-Ching ta ce, 

 "Ba zan rubuta ba! Rubutu ai zunubi ne ga wadda take da ciki a ranar farko. Kuma ma, wannan fensirin naku ba shi da daɗi, gara in riƙa tsara gashin Gely da shi!"


Ta juya tana kallon wani ɗalibi a gefenta,

 "Kai kuma me kake kallo na? Ko kana so ka taɓa hannuna ne kai ma ka ba ni wani cikin?"



Chief onyx kai tsaye babban office ɗin malaman da ake interview ya nufa...


Yana shiga ya fara musu faɗa akan cewa sun shanya shi a washe, bayan sai anyi interview aka ba da ajin da ɗalibi zai shiga...


Haƙuri suka shiga bashi sakamakon shine shugaban ƙasar gaba ɗaya.... Dan ma wasu lokuta yana da sauƙin kai...


"Please Chief kayi haƙuri, principal ne bai iso ba, shi ya sa ka ga bamu neme ka ba..."


Chief ya ce,  "Oh daman zan zauna ne ina jiransa?..." 


Sai ga principal wanda ya iso ba da jima wa ba..

Haka ya shiga roƙon Chief..


"Please am so sorry Chief, pardon me please, nayi kuskure..." 


Chief ya fita tare da nufan class ɗin da aka shiga da Ching Ching na ƴan primary...


Ya shiga ya damƙo hannunta cikin fushi, daga ita har malaman sun ɓata masa rai...

Ya fara jan ta, Gely na biye da su a baya..


Chief Onyx ne ya shigo da Ching Ching babban office na makarantar, inda manyan malamai da shugabannin bangarori suka hallara. Wannan shi ne ranar farko da za a tantance ta, domin a san ajin da ya dace a saka ta..


Ching Ching na tsaye gefen Chief, tana jujjuya ido, tana washe baki kamar ba interview aka zo yi ba, gana ganinta zaka san cewa bata san komai ba..😌


Tana sanye da uniform ɗin makarantar cikin tsabta, amma idonta na kan kayan  alatun da aka zuwa a office ɗin, ga wani tsararren ƙaton plasman...


Aka ba su wurin zama...


Shugaban makaranta ya fara da murmushi..


“Ching Ching, welcome. Don’t be nervous, okay?”


Ching Ching cikin dariya da shagwaɓa ta ce,

“Okay sir 😁 ni ba ma jin tsoro.”


Malaman suka kalli juna suna murmushi..


An fara da tambayoyin Basic General Knowledge..


Teacher 1 ya tambaya..


“What is your full name?”


Cikin tsalle ta furta

       “Ching Ching Onyx.”


Chief onyx ya kalli malaman ya ce  "Firdous Muhammad Nourdeen..."


Malamin Yana dariya ya ce,  "Eh mun gane, ga sunan natan a jikin allon mu, mu na so mu gwada ƙwaƙwalwarta ne...


Sannan aka koma kan Ching-Ching..


“How old are you?”


Ching Ching ta ce, 

“I am almost seventeen years old.”


“How many continents do we have in the world?”


Ching Ching ta ba da amsa,

“Seven continents.”


"Why do you want to join this school?..."


Ta amsa cikin confidence 

   “Because I love learning, and I want a place that will challenge my brain.”


Malamai suka kalli juna, suna murmushi...


Mathematics Question ⁉️ 


Malamin Maths ya matsa gaba, ya ɗauko biro.


“If 3x + 5 = 20, what is the value of x?”


Ching Ching bata ko yi tunani ba ta ce, 


“3x = 15, so x = 5.”


Malamin ya miƙa mata marker..


Solve: 24 × 6 − 18 ÷ 3.


Ching Ching ta kalli farin board sannan ta rubuta.

24 × 6 = 144

18 ÷ 3 = 6

144 − 6 = 138...


Wani question again..


If x + 7 = 20, find x..


Ta rubuta  “x = 13.”

Ba tare da jinkiri ba...


*English Language questions* 


English Teacher ya ce,


“Make a sentence with the word confidence.”


Ching Ching tana tsalle tana cakumar hannun Chief irin an bata tambaya mai sauƙi..ta furta


“I answered all the questions with confidence.”


Another question...


“Change this sentence to past tense:

She is going to school.”


Ching Ching tana gatsine ta ce, 

“She went to school.”


Malaman suka ɗaga gira cikin mamaki... 😮


*SCIENCE (Basic & Advanced)*


Science Teacher ya ce,


“What is photosynthesis?”


Ching Ching ta amsa.


“It is the process by which green plants make their own food using sunlight, carbon dioxide, and water.”


Other question

“What organ pumps blood in the human body?”


Ta amsa cikin yanga...

“The heart.”


Question 

Mention two types of energy...


Ta amsa da..

“Kinetic energy and potential energy.”


*CHEMISTRY*


Chemistry Teacher ya ba ta  tambaya..


“What is the chemical symbol for water?”


Ching Ching ta amsa da 

               “H₂O.”


Another question 

“What is an acid?”


Ching Ching ta amsa


“An acid is a substance that produces hydrogen ions in water.”


Question 

What is an atom?


Ching Ching ta ba da amsa

“An atom is the smallest unit of an element.”


*PHYSICS*


Question: What is gravity?


Ching Ching answer.


“Gravity is the force that pulls objects toward the earth.”


Question: State Newton’s first law.


Ching Ching answer...

“An object will remain at rest or in uniform motion unless acted upon by an external force.”


Question 

“What is the unit of force?”


Ching Ching answer...

“Newton.”


Nan fa murmushi ya ƙara faɗaɗa a fuskar malamai....



*COMPUTER STUDIES*


Question: What is a computer?


Ching Ching answer...

“A computer is an electronic device that accepts data, processes it, and gives information.”


Question 

 Mention two input devices...


Ching Ching answer..

“Keyboard and mouse.”


A nan fa, mamaki ya ƙara  cika dakin 😳..


Sai wani malami ya ɗan tsuke fuska ya ce..


Q: Explain the relationship between science and technology...


Ching Ching ta ɗan ɗaga gira, ta ce: 


“Science discovers knowledge, while technology applies that knowledge to solve human problems.”


Nan ne Chief ya girgiza kai yana cewa..


“Haba, she didn’t come here for advanced studies. Those questions are for degree or master’s level students. She is almost seventeen years old....”


Cikin burgewa, ɗaya daga cikin malamai ya dubi Chief Onyx...


“Chief, has she attended any formal school before?”


Kafin Chief ya buɗe baki..

Ching Ching ta miƙe tana faɗin..


“Laaa! Tun da nake Abul ɗina bai taɓa kai ni makaranta ba. Malam Musa ne yake koya min a gida. Kullum yana tsara darasin da za mu yi, ni kuma nakan tambaye shi har sai ya gaji da surutuna....”


Ɗakin ya kaɗu da murmushi..


A zuciyar Chief kuwa, farin ciki ya cika shi.

‘Wannan yarinya ba za ta ɓata lokacinta a banza ba... Kwakwalwarta tana ɗaukar abu nan da nan...


Sai aka ci gaba da wasu  tambayoyin da suka fi ƙarfin shekarunta..


Chief Onyx ya girgiza kai yana cewa...

“Please, remember she is not here for a degree program.

These questions are for university students and even master’s level....”



Daga nan Barista Kabir, babban lauya kuma malamin Islamiyya...


Ya kalli Ching Ching ya ce..


“Bismillāh. Let’s begin.”


Barista Kabir ya tambaye ta sunanta...Da sauri ta furta...


"Ching-Ching Onyx..."


Malam ya ce,


“To Malama Ching Ching, me ake nufi da Imani?”


Ching Ching ta amsa a sauƙaƙe..


“Imani shi ne gaskatawa da zuciya, furtawa da baki, da aiki da gabobi.”


Barista Kabir ya ƙara da cewa..


“Nawa ne Rukunan Musulunci?”


Ta amsa a taƙaice

“Biyar.”


Ya kuma tambayarta..


“Nawa ne Rukunan Imani?”


Ta ce, 

                 “Shida.”


Ya ce, 

“Me ake nufi da Ikhlasi?”


Ching Ching ta nutsu sannan ta fara faɗin..


“Yin ibada domin Allah shi kaɗai ba tare da nuna wa mutane ba.”


Tana amsawa cikin wasa, shagwaɓa da rigima, kamar an zuba mata ilimi a kwakwalwa...


Menene Tauhidi?


Tana dariya ta ce, 


“Tauhidi shi ne kaɗaita Allah cikin ibada, sunaye da siffofi.”


Yana jinjina kai ya ce.

 Menene sharuddan sallah?


Ta ce, cabb haba Malam me ya sa kake mun tambayoyi masu sauƙi haka? Sai kuma ta amsa..


“Tsarki, rufe al’aura, fuskantar alƙibla, lokaci ya shiga, da niyya.”


Malamin yayi dariya sannan ya ce,


Guda nawa ne surorin  Qur’ani...


Ta ce,

“Qur’ani yana da surori 114.”


Question 

Ma’anar ‘العلم نور’...


Ta furta..

“Ilmi haske ne.”


Ya ce, Ki yi jumla da kalmar ‘كتاب’.


Ta ce, 

“هذا كتاب مفيد.”


Ta faɗi tana ƙaramin murmushi tana wasa da yatsunta...


Malaman suka kalli juna cikin mamaki da gamsuwa.

A yau, kowa ya tabbatar cewa Ching Ching ba yarinya ce ta yau da kullum ba.


Barista Kabir ya jingina kai yana cewa..

 “Subḥānallāh… baiwa daga Allah...”



Bayan kammala interview, malamai suka sake komawa teburinsu... An ɗauki ƴan mintuna ana tattaunawa cikin ƙasa-ƙasa, ido na kai-komo zuwa ga Ching-Ching wadda ke zaune tana juya kujera tana wasanta kamar komai bai dame ta ba...


A ƙarshe, shugaban makarantar ya ɗaga kai ya ce..


“Miss Ching-Ching Onyx… after careful consideration, we’ve decided to place you in Senior Advanced Class.”


Chief Onyx ya zaro ido.. “Senior… what?”


Shugaban ya murmusa. “Senior Advanced Class. It’s a class meant for students preparing ahead of university-level thinking.”


Ching-Ching ta ɗan turo baki. “Toh… zan yi lunch da wane aji?”


Duk office ɗin suka ɗan yi dariya...



Da rana, bayan an gama komai na rajista, aka raka Ching-Ching zuwa ajinta..

Aji ne babba, mai tsari, AC na aiki, ɗalibai kusan ashirin da...


kowa yana cikin nutsuwa, wasu suna karatu, wasu na muhawara cikin turanci.

Da aka buɗe ƙofar ajin…


Shiru ya mamaye wurin.

Idanu sama da ashirin suka sauƙa kanta lokaci guda..


Uniform ɗinta ya sha bamban da na sauran, domin uniform junior aka mata, yanzu sai an sake mata wasu uniform kala-kala na senior...


Malamin ajin ya ce,

 “Class, we have a new student. Her name is Firdos Muhammad Nou.....”


Malamin bai ƙarasa ba Ching Ching ta katse shi da faɗin..


"Ching-Ching Onyx ne..."


Wasu ɗalibai suka kalli juna.

Wata yarinya mai suna Elena ’yar Italiya ta raɗa..


“She looks too young…”


Wani saurayi ɗan attajirin Indiya ya ce..

“Probably another spoiled rich kid.”


Ching-Ching ta ji amma ta yi kamar ba ta ji ba..


Domin Chief ya yi mugun ja mata kunne akan yawan magana...sannan kar ta sake ce wa kowa, tana da juna biyu domin kowa zai ɗauke ta karuwa ce.... 

A lokacin ta nutsu domin tasan karuwai ne ƴan wuta..ita kuma ba ta son ana dangantata da shiga wuta..


TAMBAYA TA FARKO A AJIN...

Malamin ya ce..


 “Ching-Ching, please solve this on the board.”


Yayi hakan ne domin kawai da tunanin sauran ƴan ajin a kanta, kar su yi tunanin ko kuɗinsu ko dan ƙanwar shugaban ƙasar ne yasa aka ba ta ajin.... Yana so ya nuna musu cewa iliminta ne ya ba ta...


Ya rubuta tambayar Mathematics na Advanced Algebra...

Wasu suka yi murmushi na raini...


Ching-Ching ta miƙe, ta ɗauki marker. Ba tare da ɓata lokaci ba..


Tana magana cikin confidence da yanga da kuma shagwaɓa...

Ta warware tambayar daidai, tsaf, babu kuskure...


Ta juyo ta ce.. “Is that all, sir?”


Aji ya sake yin shiru...


Elena ta buɗe baki..

“Wait… how did she do that?”


Domin a ajin ita ke ɗaukan first class..


Wani saurayi daga China ya gyara gilashinsa...


“She skipped three steps… but still got the right answer.”


Malamin ya ce.. “Class, that’s correct, Please clap for her..."


Nan ajin ya ɗauki sautin tafi, a yayin da wasu suke jin haushin ta ya daga shigowarta zata yo sama....


Wasu fuska suka fara canzawa

daga raini zuwa mamaki...


Ching-Ching ta koma kujerarta tana faɗin ƙasa-ƙasa da murya,  “Kai… ashe ba wahala ma...”


Tun daga wannan rana,

sunanta ya fara yawo a makarantar...

“The new girl with the scary brain...”


Tun daga wannan rana, hankalin ajin ya rabu gida biyu.

Wasu daga cikin samari suna neman su samu damar zama kusa da Ching-Ching..


“Hi… can I sit here?”


“You’re really smart, where did you study before?”


Wasu ’yan mata kuma cikin ladabi suke kusantarta..


“Your accent is cute.”

“Please, teach me how you solved that question.”


Ching-Ching kuwa? Tana amsa wa kowa cikin sauƙi da sakalci, tana murmushi, tana wasa da alƙalami kamar karatu wasa ne a wajenta...

Wasu da aka basu assignment tin kafin ta zo, duk tayi mu su...


Tana mu su tana tunani a zuciyarta... “Kai… ashe mutane suna son ilimi haka?”



Da ƙarfe 2:00pm, an kammala boko.

A ƙofar makaranta, aka ga jiragen ɗaukar ɗalibai Kiristoci daga ƙasashen waje..

Turawa, Italiyawa, Chinese, Indiyawa

ana ɗaukar su zuwa gidajensu...


Yaran Musulmi kuwa suka nufi ajin Islamiyya na ƙarfe 2:30pm – 5:00pm..


Bayan sun yi lunch na rana..


Ching-Ching ta biyo su cikin mamaki..wasu suka fara faɗin

“Ashe har da wannan?”


Ching Ching ta shiga ta ga tsaruwar ajin da basu wuce 30 ba, domin christoci sun fi yawa a makarantar...


“Nice… I like this part.”

Ta furta tana washe baki..


Malamin Islamiyya, Sheikh Abdul-Kabir, mutum ne mai nutsuwa, cike da ilimi...


Ya fara da cewa... “Bismillah… yau zamu yi bitar Al-Kur’ani.”


Ya yi tambaya ta farko...

“Wace aya ce ta ambaci halittar Annabi Isa (A.S) da misalinsa?”


Hannu da yawa suka ɗaga.

Wasu suka amsa daidai, wasu kuma saɓanin haka...


Ching Ching itama ta ɗaga..


Malamin ya ce.. “Miss Ching-Ching, please.”


Ching-Ching ta miƙe cikin confidence, ba tare da rawar murya ba..


Bayan ta karanta ayar sai kuma ta fassara..


Allah Madaukakin Sarki ya ce, 


“Hakika misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adam ne,

Allah Ya halicce shi daga ƙasa, sannan Ya ce masa Kasance, sai ya kasance. .”


Ajin ya yi shiru..


Malami ya ce,  “Excellent.”


Malami ya ci gaba..

Tambaya ta biyu

“Wace aya ce ta yi magana akan cewa Annabi Isa bai mutu ba, Allah Ya ɗaukaka shi?”


Ching-Ching ta sake miƙe wa..

Ta ƙara da cewa


وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَٰكِن شُبِّهَ لَهُمْ


“Sun kashe shi ba, sun gicciye shi amma sai aka rikita musu tunani...”


Malamin ya tsaya yana dogon tunani akan fassarar amsar, amma ayar dai-dai ne...


Nan malamin yayi murmushi sannan ya ce,


"...Ba su kashe shi ba, kuma ba su kafa shi a kan cross ba wato giciye, amma dai an nuna musu kamanninsa ne..."

Malamin ya ci gaba da darasin..


Allah ya kare shi daga mutuwa a hannunsu...


Wannan yana karyata imanin da wasu suke da shi na cewa an gicciye shi a Crucifixion...


Mafi yawan malamai kamar su Ibn Abbas sun fada cewa, lokacin da sojoji suka shiga gidan da Annabi 'Isa yake, Allah ya canza fuskar wani mutum daban, wasu sun ce maci amanar nan ne Judas, wasu kuma sun ce ɗaya daga cikin almajiransa ne ya bada kansa ta koma daidai da ta Annabi 'Isa... Sai suka dauki wannan mutumin suka kashe shi, suna tunanin Annabi Isa ne...


Aya ta gaba ta ci gaba da cewa,  "A'a, Allah ya ɗaukaka shi ne zuwa gare Shi..."


Wannan ayar tana cikin Suran An-Nisa (Sura ta 4), aya ta 157. Tana daya daga cikin ayoyi mafi muhimmanci da suke bayyana gaskiyar abin da ya faru da Annabi Isa (AS) lokacin da Yahudawa suka yi ƙoƙarin kashe shi...


Ching Ching ƙare shi da kallo, duk tasan wannan domin Malam Musa akwai ranakun da yake ware wa don bayyana tarihi da ayoyin da suke cikin Alqur'ani...


Bayan ajin yayi shiru sai kawai ta yi wani kwafa mai ƙarfi tana faɗin 

"Allah yasa Arna su ji ka...don kashe ka zasu yi.."


Ƴan ajin ne suka yi dariya daga bisani 

Malamin ba tare da ya ce komai ba, ya sake jefa wata tambaya


“Wace aya ce ta nuna cewa Annabi Isa bawa ne na Allah?”


Wannan karon wata ce ta miƙe ta amsa

إِنْ هُوَ إِلَّا عَبْدٌ أَنْعَمْنَا عَلَيْهِ


(Suratuz-Zukhruf: 59)


Malami ya girgiza kai yana murmushi..


 “Alhamdulillah…”


Sai malami ya ce...

 “Yanzu tilawa zamu yi.”


Kowace ɗaliba da surar da take...


Malamin ya tambayi Ching-Ching surar da take..


Ta ce cikin tana juya ido.


 “Suratul Aal-Imran.”


Ta fara karatun tajwidi har ta zo yadda ta tsaya domin ba ta gama surar ba... 


Bayan an tashi..

Malami ya ce...


 “Miss Ching-Ching, who taught you all this?”


Ta turo baki tana murmushi..


“Malam Musa… but sometimes I argue with him.” 😌


Malamin ya ce 

"Ma sha ALLAH, duk Allah ya haɗa miki, boko da Arabic, ina ma ace ke ƴata ce..."


Ching-Ching ta turo baki ta ce, 

"Hu uhmmmmm! Ni fa ƴar sarki ce, ƙanwar sarki kuma amma kai na ga ba ka da wani sarauta..."


Haka malamin ya biye mata suka riƙa hira har aka zo ɗaukanta itama..


Iya bodyguards ne suka zo..

Tare da Gely...


Ganinsu ya sa Ching Ching ta fara murguɗa baki, ita tayi tunanin da jirgi xa'a zo ɗaukanta....


Kamar sauran...



 *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 


👍 Like

🔁 Share

💬 Comment

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post