Masarautar Alhamra Page 32 Complete

 

Masarautar Alhamra Page 32 Complete

*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* 


_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_


✍🏽 By ASMEETAH WRITER

~Hasken Jajirtattu~



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️


   ```JARUMAI WRITERS TEAM``` 


▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇

🔗 WhatsApp Channel:

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


📚 ArewaPen:

https://arewapen.com/u/asmeetahwriter


📖 Wattpad:

https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter


📲 Contact:

09065443871


📅 FARA TURA BOOK:

🔥 01 — 01 — 2026 🔥


📘 BOOK ONE 

           ```MATAKIN FARKO``` 


CHAPTER  3️⃣2️⃣


 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



Sarki ya ɗaga hannu, "Za ku iya tafiya, Allah ya muku albarka. Zayana kuma... Allah ya shirye ta."


​Maayah ta fita tana rarraba ido, tana jin daɗin yadda ta wayance, a tunaninta ta ba da amsa daidai... yayin da Ayat take tafiya tana danne dariyarta, Yumna kuma tana satar kallon Sheikh Shureim kafin ta fice daga fadar...


​Bayan ficewarsu, fadar ta dawo shiru. Sarki ya kalli Malam Mubarak da Sheikh Shureim..


​"Ina son ku haɗa kai," in ji Sarki. "Tunda Ayat da Yumna duka sun kammala hadda, ina son walimar nan ta zama abin koyi a duk faɗin ƙasar nan. Ina son a raba kyaututtuka ga marasa ƙarfi, kuma a gayyato manyan malamai su shaida wannan nasara."


​Malam Mubarak ya jinjina kai, "Ranka ya daɗe, wannan babban ra'ayi ne. Za mu tsara yadda za a yi gasar karatun a ranar, domin kowa ya ga irin ƙoƙarin da suka yi."


​Sheikh Shureim, wanda fuskarsa ke nuna natsuwa, ya ƙara da cewa, "Zan fara tsara tsarin jadawalin taron, tare da zaɓar ayoyin da za su karanta waɗanda za su ratsa zuciyar jama'a. Wannan taro zai zama haske ga masarautar nan."


​Bayan malamai sun gama bayanan su, Sarki ya yi shiru na ɗan lokaci, yana tunanin Maayah. 

   Maganar Suratul Musa ta nuna masa cewa Maayah ba ta san komai ba game da karatun da take ikirarin yi a makaranta..


​"Akwai matsala," Sarki ya faɗa ƙasa-ƙasa. "Maayah tana ɓata lokacinta ne. Kuma wannan rashin tarbiyyar ta Zayana, ba zan bar ta ta shafi Maayah ba."


​Nan take Sarki ya ƙira babban hafsan hadimansa..


​"Maza ku shirya motoci ku tafi makarantar su Maayah. Ina son ganin Principal da kuma malamin ajinsu, a nan fada yanzun nan. Ina son jin hakikanin gaskiyar abin da Maayah take yi a makaranta, domin ba na yarda da sakamakon da ake kawo min na first class.."


​Hafsan hadiman ya duƙa, "An gama Ranka ya daɗe."


​Cikin ƙanƙanin lokaci, jerin gwano na motocin fada suka tashi da gudu zuwa makarantar, wanda hakan zai zama babban tashin hankali ga Principal...


✨✨


Babban Hadimin ya wuce kai tsaye zuwa ofishin Principal ba tare da neman izini ba. Principal yana zaune yana lissafin kudin da yake samu na gyara sakamakon jarrabawa, ya ga mutane sun daka masa tsawa..


​"Sarki yana ƙiran ka yanzun nan a fada!" In ji Hafsan...

 "Kai da malamin dake koyar da ajin Gimbiya Maayah..."


​Principal ya shiga in-ina, zufa ta fara keto masa duk da sanyin AC dake ofishin.


 "Lafiya... lafiya dai ko? Ko wani abin ne ya samu Gimbiya?" Ya san cewa idan asirinsa na ba ta First Class na ƙarya ya tonu, to kashinsa ya bushe.


​A ɗayan ɓangaren kuma, Uncle Jalal yana cikin aji, yana gyara wasu takardu. Hadimin ya iske shi ya gaya masa saƙon Sarki. Sabanin Principal, ba tare da ya firgita ba, ya gyara kwalar rigarsa, ya rufe jakarsa cikin natsuwa...


​"Madalla," Jalal ya faɗa cikin murya mai kwarjini. "Dama akwai maganganun da ya kamata a ce Sarki ya ji su tun can baya."


​Principal dake tsaye a bayansa yana rawar jiki ya yi masa kallon lallai Jalal zai kaimu ya baro mu, amma Jalal ko kallo bai nuna yana jin tsoro ba.


​Yayin da ake jiran isowar su Uncle Jalal, Malam Mubarak da Sheikh Shureim sun fito zuwa wajen fadar, inda suka zauna a karkashin wata inuwar bishiyar flowers don tattauna maganar walimar..


​Malam Mubarak ya dube Sheikh Shureim da murmushi,

 "Sheikh, lallai Gimbiya Yumna ta samu malami nagari. Natsuwar da ta nuna a fada yau abin sha'awa ne."


​Sheikh Shureim ya sunkuyar da kansa, muryarsa cike da girmamawa. "Duk godiya ta tabbata ga Allah. Amma maganar gaskiya, kalaman Gimbiya Ayat sun ba ni mamaki. Burinta na zama sojan sama ba ƙaramin abu ba ne. Shin kana tunanin Sarki zai amince?"


​Malam Mubarak ya yi ajiyar zuciya. "Ayat mace ce mai zurfin ciki. Ta daɗe tana karance-karancen littattafan bincike da dabarun tsaro... Ni kaina na san cewa ranta ba ya kan likitancin nan, sai dai kawai tana biyan burin mahaifinta ne. Amma yanzu da ta fito fili, ina jin za a yi gumurzu a masarautar nan."


​Sheikh Shureim ya jinjina kai, "Allah ya tabbatar da alheri. Amma batun walima, ina son mu tsara yadda su biyun za su fito su yi tilawa a gaban kowa, domin a ga banbancin dake tsakanin hasken Alkur'ani da duhun jahilci, musamman ga sauran 'yan uwansu."


​Malam Mubarak ya amince, "Hakan ya yi. Bari mu fara rubuta sunayen manyan malamai da za mu gayyata kafin taron."



Maayah tana can sashenta, duk ta fita a hayyacinta. Jin cewa an je kiran Principal da Uncle Jalal ya sa ta san asirinta ya kusa tonuwa. Ta lallaɓa ta koma sashen fadar sarki kafin su iso ta laɓe a bayan labulen, 

Zuciyarta tana dukan uku-uku, tana jin inama Uncle Jalal bai taɓa zama malamin su ba...


Can sai ga motocin sun faka, aka shigo da su.. Principal yana taku yana tanga-tanga, jikinsa har rawa yake yi, yayin da Uncle Jalal yake tafiya cikin natsuwa da kwarjini, kai kace shi ne mai masarautar...


Lokacin shima Sarki ya fito ya zauna akan karagarsa, fuskarsa ba annuri..


 "Principal, na ƙira ka ne domin in ji dalilin da ya sa kake yaudarata da sakamakon ƙarya na Gimbiya Maayah."


Principal ya zube a ƙasa, "Ranka ya daɗe... kuskure ne... muna dai ƙoƙarin ƙarfafa mata gwiwa ne..."


Sarki ya dakatar da shi da hannu, ya kalli Uncle Jalal..


 "Kai ne malamin ajinsu, ko? Faɗa min gaskiya, yaya Gimbiya take a karatu?"


Uncle Jalal ya gyara tsayuwa, ba tare da ya duƙa ba...


 "Ranka ya daɗe, magana ta gaskiya ita ce.. Gimbiya Maayah ba ta san komai ba game da karatun da nake koyarwa. Ba ta yin rubutu, ba ta karatu, kuma tana tunanin sarautarta za ta sayi ilimi. Sakamakon da kake gani na ta ɗaya, duka na bogi ne. Maayah tana matakin 'yan Nursery ne a fannin ilimi."


Principal ya so yin magana, amma Jalal ya cigaba..


 "Hasali ma, na zo ne da wasu littattafanta don ka gani da idonka. Wannan shi ne abin da ake kira cin mutuncin ilimi a makarantarka."


Sarki ya karɓi littattafan da Jalal ya miƙa masa. Ganin rubutun Maayah ya sa Sarki ya fusata. Ya buga hannunsa a hannun kujerarsa, 


"Ina Maayah take?! Maza a fito min ita yanzun nan!"


Maayah dake laɓe ta ji ƙafafunta sun ɗauki karkata. Ta san idan ta fito yanzu, kashinta ya bushe. Ta fara kuka a hankali a bayan labule, tana tsinewa ranar da Uncle Jalal ya fara shiga ajinsu...


                 ✨✨✨


A ɓangare guda kuma, Ayat ta kasa samun nutsuwa akan ganin yadda Zayana ta ci mutuncin mahaifinsu...daga part ɗinta ta fito zata fita.

    Ta sa aka kawo mata tsararren dokinta wanda ya sha kwalliya da kayan ado masu tsada...


Masu tsaro suka dakatar da ita ganin bata juma da shigowa ba kuma za ta ƙara fita...

     Ba ta tsaya sauraronsu ba ta nufe su da dokin tana shirin bi ta kansu.. da gudu suka matsa mata tare da faɗin "zan je wurin sarki..."


Da ga nan ta nufi sashen Zayana akan dokinta...


Masu tsaron sashen Zayana ne suka buɗe mata ganin Gimbiya ce.



Ayat ta shiga falon Zayana cikin takun fushi, mayafin fuskarta yana kadawa...


Cikin ɗaga murya ta furta.

     "Ina Zayana take?"


Wata daga cikin bayin dake goge falon cikin kunfar baki ta ce,


 "Haba Gimbiya, ai kya girmama sunan nata ko? Babbar gimbiya ce fa..."


Ayat ta watsa mata kallon raini,  "Ban ga dama ba! Duk wanda ba ya mutunta mahaifina, to shima babu sauran mutunci a idona. Kuma ki kiyaye ni, kafin in yanke miki harshe! Ba wurinki nazo ba, wawaye kawai waɗanda ku ma ba'a  ɗauke ku mutane ba."


Mimi ta sauƙo daga bene tana kallon Ayat cikin  idanun nan nata na kyanwa...


"Ke mai rufe fuska! Me kika zo yi mana? Ba ma sonki, ki bar mana fadar mu!"


Ayat ta tsaya dambar tana kallon yarinyar, sannan ta furta.

 "Ai kuwa kun mutu da ni! Domin wannan fadar mahaifina ne, ba wai gidan agolar masarauta ba."


Ayat ta dakata tana jin takaicin amsar da ta bawa Mimi domin tana ganin girmanta ya zube da ta tsaya biye wa ƙaramar yarinya...tana cikin tunani sai ta ji..


Mimi ta ce cikin muryar yara "Ƙarya kike yi! Masarautar mu ce!"


Ayat ta duƙa har matakin idon yarinyar... Ba tare da wata-wata ba, ta ɗauki almakashin dake gefen table ta yanke tulin gashin Mimi mai launin ruwan ƙasa, ta mika mata a hannu...


 "Gashi nan, ki kai wa mahaifiyarki kice ni na bayar."


An raba tsakiyar gashin biyu, rabin gashi a hannun Mimi, sai na kanta da ya zamo short hair..


Mimi ta fashe da kuka mai sauti,  "Wayyo gashina! Mommy! Gashina ya tafi!"


Zayana ta sauƙo bene a guje, idanunta sun yi jawur saboda bacin rai....tin farkon shigowarta ta sani already..


Cikin ɗaga murya tana daka wa Ayat tsawa...


 "Stop it! What is wrong with you?!"

ta kai wa Ayat wani zafafan mari...


Ayat ta dafe kuncinta, sannan cikin zafi ta mayar mata da nata marin, har sau biyu....


Cikin fashin murya Zayana ta furta, 

 "Ni kika mara? You slapped me?!"


Ayat ta ce,  "Ni ɗin gunki ce da zan tsaya ki mare ni? Idan kin saba dukan bayi, to kinyi kuskuren taɓa jinin sarki!"


Zayana ta fara magana da hausa dake gauraye da turanci cikin raunin lafazi, dake ba ta wani kware sosai a Hausa ba... 


"You are nothing! Ke ba komai bace! Mahaifina ma tsorona yake yi, balle ke!"


Ayat ta ce, 

 "Mahaifinki ba tsoronki yake ba, yana kyaleki ne don girman kansa! Amma ki sani, duk wata izzah da kike takama da ita, a karkashin inuwar sarautarsa take. Amma yau kin nuna cewa baki da tarbiyya, baki da asali, kuma baki da godiyar Allah!"


Cikin fusata Zayana ta daka tsawa 

"Shut up! You have no right to come into my house and........"


Ayat ta katse ta da kakkausan murya, 

    "I have every right! Wannan gidan mahaifina ne. Kuma bari kiji, rashin kunyar da kika yi masa a fada yau, ita ce ta karshe. Idan kika sake wulaƙanta shi, to ba zan tsaya a gashin 'yarki ba, zan ruguza muku dukkan izzarku! Ke baturiya ce a jini, amma kin rasa ko da ɗan mutuncin turawan ma, kin koma tamkar dabba mai cin naman wanda ya rene ta!"


Zayana tana huci ta ce,


 "Zan ga abin da zaki iya yi..."


Ayat ta ce, 

   "Kin riga kin gani! Ga gashin 'yarki a ƙasa, ga kuma marin fuskarki. Wannan gargadi ne na farko. Next time, it will be worse. Ki kiyaye mahaifina!"


Ayat ta juya cikin takun alfarma, ta bar Zayana tana tsaye tana karkarwa saboda tsananin fushi, yayin da bayin falon suka yi tsuru-tsuru suna kallon ikon Allah...



✨✨


A can fada kuwa, Hadimin da aka aika ya ƙira Maayah ne ya dawo, ya sanar da ba ta nan, 

Maayah jin haka yasa ta fito daga bayan labule, fuskarta duk ta jike da hawaye, idanunta sun yi jawur. Ta tsaya tana karkarwa, sannan ta wurga wa Uncle Jalal wata uwar harara mai cike da kiyayya...


Uncle Jalal, maimakon ya fusata, sai ya saki wani ƙasaitaccen murmushi, yana kallonta kamar yadda malami yake kallon ɗalibi waton kallon shashasha da asirinsa ya tonu...


Sarki ya kalleta ya ce, "wato laɓe kike mana ko? Me ya sa ba ki koma sashenki ba?..."


Maayah tayi shiru kanta a sunkuye...


Cikin muryar takaici Sarki ya kuma cewa,


 "Maayah, wannan ƙwaƙwalwar takin ba irin ta mahaifiyarki bace. Ke kin fita daban! Duba irin rubutunki, duba irin yaudarar da kuke yi min da wannan Principal ɗin."


Daidai lokacin, Master Ibrahim shugaban tsaro na musamman ya shigo fadar cikin takunsa na jarumta...

 Ya gaishe da Sarki cikin girmamawa...


Sannan ya furta "Ranka ya daɗe ka aika na zo..."


Sarki ya dubi Ibrahim sannan ya ce, 


"Master Ibrahim, yanzu nake son ka je ka koya wa Zayana hankali. Ka hukunta ta yadda ya dace, sannan ka tafi da ita ka kulle ta a Dark Room No. 2 na tsaro. Ba na son jin wani bayani har sai ta san darajar mahaifinta."


Master Ibrahim ya ji zuciyarsa ta buga. Ya san ɗakin duhu na biyu, ɗaki ne da ko ɓera aka kulle a ciki sai ya firgita, balle Zayana mai izzah... Ya san kowa yana tsoron mahaifiyarta, amma umarnin Sarki ya fi karfin kowa..


Master Ibrahim ya ce, 

 "An gama, Ranka ya daɗe."


Ya juya jiki a sanyaye, yana tunanin yadda zai fuskanci Zayana wadda kowa ya san ba ta da mutunci..


Bayan ficewar Master Ibrahim, Sarki ya mayar da hankalinsa kan Maayah da Uncle Jalal..


 "Ke kuma Maayah, tunda kin ce kina Suratul Musa, kuma kina Suratul Isabul Maryama, yanzu za ki nuna mana abin da kika sani...

      Malam Jalal, ina son ka ba ta jarrabawa a nan gaba na yanzun nan. Idan har ta kasa amsawa, to ke ma hukuncinki yana jiran ki."


Maayah ta ƙara fashewa da kuka, tana kallon Uncle Jalal kamar tana roƙonsa da ido, amma Jalal ya riga ya buɗe littafinsa yana neman tambayar da zai wanke mata lissafi...


Sarki ya gyara zama, fuskarsa cike da ɓacin rai amma kuma yana son ya tabbatar da abin da Uncle Jalal ya faɗa... 

  Ya kalli Uncle Jalal ya jinjina masa kai alamar ya fara...


Cikin muryarsa mai natsuwa dake cike da izgilanci ya fara...


"To Gimbiya Maayah, bari mu fara da abin da kika sani a fannin ilimin addini tukunna."


Maayah ta tsaya tana karkarwa, hawaye suna ɗigowa daga idanunta, tana kallon Uncle Jalal cikin kiyayya...


 "Faɗa mana, guda nawa ne rukunnan Musulunci? Kuma rukunin farko menene shi?"


Maayah ta goge hancinta, ta kalli Sarki sannan ta kalli Uncle Jalal. Ta yi shiru na kusan minti biyu, kafin can ta buɗe baki...


 "Rukunnan Musulunci ai... ai guda talatin ne!"


Duk hadiman dake wurin suka kalli juna. Sarki ya dafe goshi, yayin da Uncle Jalal ya ɗanyi murmushin nan nasa na gefen baki..


Uncle Jalal ya ce,  "Talatin? To madalla. To gaya mana ko guda daya a ciki."


Maayah cikin kuka ta ce, 

   "Eh mana! Akwai rukunin yin rubutu, da rukunin zuwa makaranta, da rukunin cin abinci... sannan kuma rukunin farko shi ne yin Biyayya ga Gimbiya'!"


Sarki ya kasa cewa uffan, ran sa na kan ɓaci matuƙa. Uncle Jalal bai tsaya nan ba, ya buɗe littafinta na makaranta wanda babu komai a ciki sai zanen furanni da rubutun yara...


Ya ce,  "To bar wannan. A darasin lissafi na Maths, idan aka ce ki lissafo 10 + 10 nawa ne?"


Maayah ta fara ƙirga yatsun hannunta, ta ƙirga ta ƙirga har ta kai karshe, ta kasa... Ganin Sarki yana kallonta ya sa ta ƙara ruɗe wa...


"Ai... ai goma sha tara ne! Idan aka cire ɗaya kuɗin motar da zan ba bodyguards ɗina, sai ya zama goma sha tara!"


Sarki ya kasa daurewa, ya miƙe tsaye daga kan karagarsa. Principal dake gefe ya ƙara dukunkuyewa saboda tsoro...


Sarki ya ce,  "Wannan wane irin hauka ne Maayah? Wannan shi ne abin da kika iya? Wannan shi ne first class ɗin da kike taƙama da shi? Kin mayar da kanki abin dariya a gaban kowa!"


Maayah ta durƙusa ƙasa tana kuka sosai...


 "Abul, wallahi shi ne! Shi ne Uncle Jalal yake koya mana haka a aji! Shi ne ya ce 10 + 10 goma sha tara ne!"


Uncle Jalal ya kalli Sarki, ya girgiza kai kawai...

 "Ranka ya daɗe, ka ga irin dalibar da kake da ita. Ba jahilci kadai ne ke damunta ba, har da son ƙago ƙarya don kare kanta."


Sarki ya nuna Maayah da yatsa..

"Daga yau, babu wani sakamakon makaranta da zan ƙara amincewa dashi. Kuma ke, Uncle Jalal zai kasance malamin ki na gida wato Home Tutor,  kuma za ki cigaba da zuwa  makaranta.... Duk inda kike zai riƙa biye dake har sai kin san me kike yi. Idan kuma baki canza ba, to ke ma Dark Room No. 2 zaki haɗu da Zayana!"


Maayah ta ji kamar duniyar ta ruguje mata. Tunanin cewa Uncle Jalal ne zai riƙa biye da ita har gida ya fi mata zafi fiye da komai. Ta kalli Uncle Jalal, shi kuma ya sakar mata wani kallo dake nufin... 

"Yanzu aka fara wasan, Gimbiya."


                      ✨✨✨


Master Ibrahim ya isa sashen Zayana tare da wasu zaratan sojoji guda hudu. A kofar shiga, ya tarar da bayin Zayana suna ta magana ƙasa-ƙasa, bayan ya shiga babban falonta ya tarar da Mimi  zaune a kasa tana faman taɓa gajeren gashin da Ayat ta yanke mata, tana ihu...


Cikin muryar soja Master Ibrahim ya furta 

 "Gimbiya Zayana! Kina ina? Umarni ne daga Sarki, kina bukatar biyo mu yanzu zuwa ɗakin tsaro."


Zayana dake kan dinning zaune ta kifa kanta akan table tana tunanin irin hukuncin da za ta ɗauka akan Ayat...


Jin muryar Master ya sa ta ɗago tare da fito falon, fuskarta yayi jajur saboda marin da Ayat ta mata, abunka da baturen mutum...

 ganin yadda Master Ibrahim ya yi mata magana ya sa ta ƙara harzuƙa...


 "Who do you think you are? Ibrahim, ka fita daga nan kafin in sa a cire maka wannan kakin sojan naka! You have no right to enter my private section!"


Master Ibrahim ya ce,


 "Gimbiya, kiyi hakuri ki biyo mu cikin ruwan sanyi. Umarnin Sarki ne, kuma kin san ba a musa masa. Kin wulakanta shi a fada, kuma yanzu lokacin hukunci ya yi."


Zayana ta kalli Master Ibrahim da waɗannan cat eyes ɗinta, ta ɗauki wata kwalbar turare mai tsada ta kwada masa, amma cikin zafin nama ya kauce...


Ta cigaba da magana 

"I am not going anywhere! Idan ka taɓa ni, Mom ɗina za ta sa a datse maka hannaye!"


Ganin ba za ta bi shi ba, ya ɗaure fuska. Ya san idan ya tsaya rarrashi, lokaci zai ƙure.. 

"Ina neman gafararki Gimbiya, amma aikina zan yi."

Cikin zafin nama, ya nufi Zayana....

 Ta fara kai masa naushi da yakushi, tana ihu tana kiran sunan mahaifiyarta. Amma Master Ibrahim ya kama hannayenta ya murde su ta baya cikin kwarewa, sannan ya sa mata ankwa...


Haka Zayana take ta zagi da maganganu..

 "Let me go! You filthy soldier! I will kill you! Mimi, call your grandmother!"


Sojojin suka kewaye ta yayin da Master Ibrahim yake jan ta da karfi. Mimi ta biyo su a baya tana kuka tana jifan sojojin da kayan wasanta. Bayin sashen kuwa kowa ya laɓe, suna kallon yadda ake jan babbar Gimbiya kamar kura...


Suna isa kofar Dark Room No. 2, Master Ibrahim ya bude kofar dake fitar da wani irin sanyi da duhu mai ban tsoro..


Ya ce,  "Gimbiya, anan zaki zauna har sai ranka ya daɗe ya bada umarnin fito dake. Kiyi tunani akan abinda kika yiwa mahaifinki."


Ya tura ta ciki, ya rufe kofar da wani babban kwaɗo. Sautin kukanta da dukan kofar da take yi ya gauraye wajen, amma Master Ibrahim ya juya abinsa cikin sanyin jiki, yana addu'ar kada mahaifiyar Zayana ta bayyana a cikin masarautar nan....


                ✨✨✨


Ganin Sarki ya fi ce daga fadar yasa Maayah ta tashi daga ƙasa inda take kuka, ta goge fuskarta, ta gyara mayafinta tana wani yatsine fuska. Ta kalli Uncle Jalal daga sama har kasa, sannan ta koma kan wata kujera ta alfarma ta zauna tana jijjiga ƙafa...


Cikin ƙasaita ta furta.

 "To Malam Jalal, ko ince  Uncle? Ai kaga nan ba makaranta bace ko? Nan gidan ubana ne, kuma ni ce Gimbiya Maayah. Don haka, kada ka sa ran zan raba kaina da ƙasa ina baka amsa kamar yadda nake yi a aji."


Uncle Jalal ya ajiye littafinsa a hankali, ya zura hannayensa a aljihu yana kallon yadda yarinyar ke kokarin nuna isa, alhalin ko 10+10 ta kasa sani..


Yana murmushi ya furta,

"Zama ko tsayuwa ba shi ne zai baki ilimi ba, Maayah....Kuma idan har baki manta ba, Abul dinki ne ya ce in zama inuwar ki har sai kin san me kike yi. Don haka, mu fara darasinmu na yau."


Uncle Jalal ya yanke shawarar saukowa matakin kwakwalwarta domin ya ga iyakarta..


Ya ce,  "To, tunda ke 'yar boko ce, gaya min, Daga ina ruwan sama yake fitowa? Kuma me yake kawo shi?"


Maayah ta danyi shiru, ta kalli silin din fadar, sannan ta taɓe baki cikin rashin sanin komai da kuma nuna ilimi...


"Wannan ai tambayar yara ce. Ruwan sama a tankin gidanmu yake fitowa! Idan aka bude fanfo a sama, shi yasa yake zuwa. Kuma idan hadimai sun manta basu rufe ba, sai ayi ta ruwa kenan har sai ya cinye ƙananun flowowi 😏...."


Ita kanta bata sani ba amma ta faɗi haka ne don ta ƙular da shi...


Uncle Jalal ya runtse idonsa na dakika biyar, yana neman hakurin da zai cigaba da wannan zama.


Ya ce, "To, bar batun tankin ruwa. Gaya min, ina ne babban birnin kasar Saudiyya...?"


Maayah ta hure iska daga bakinta, tana wasa da zoban hannunta...


 "Saudiyya kuma? Ai tana nan, ƙasar su mahaifiyar Ayat da Ching Ching ne... Na taɓa jin ana cewa can ne ake sayo turaren wuta, yanzu haka ƙamshin turaren da kake ji a fadar nan, na Saudiyya ce, to Saudiyya tana karkashin wannan masarautar tamu ne. Birnin kuma sunansa Birnin Turare..."


Wannan karon kam ta zaƙe, tsakaninta da Allah take gaya masa gaskiyar saudiyyar da ya tambaye ta..


Uncle Jalal ya matso kusa da ita, ya kura mata ido yadda ta ji jikinta ya danyi sanyi, amma ta dake ta ƙara gimtse fuska...


A hankali ya furta 

  "Maayah, kin san me nake gani idan ina kallon kwayar idonki? Ba girman kai nake gani ba, wani ƙaton duhu nake gani na jahilci wanda kike son rufe shi da gadara. Amma ki sani, muddin ina nan, sai na fasa wannan duhun. Yau zan barki ki tafi ki huta, amma gobe... gobe zamu fara da koyon haruffan 'A, B, C' da kuma 'Alif, Ba, Ta'. Kuma za ki rubuta su a gaban kowa...."


Maayah ta miƙe tsaye cikin fushi, 

 "Ni ce zan rubuta Alif Ba? Wallahi ka da ka kuskura! Ni ba 'yar Nursery bace! Kuma idan ka matsa min, zan ce wa Abul duka na kake yi!"


Uncle Jalal ya yi murmushi kawai, ya juya ya bar falon,  ya bar ta da huci tana buga kafa a ƙasa...




Uncle Jalal ya nemi izinin ganin Sarki domin ya sanar da shi tafiyarsa. Sarki ya ba da izinin ya same shi har can sashensa na musamman. Jalal ya shiga, ya zauna a babban falon Sarki, falon da aka ƙawata shi da duk wata daular duniya..


​Ba jimawa, Sarki ya sauƙo daga saman bene, ya zauna fuskarsa cike da mutuntawa...


​Bayan gaisuwa, Uncle Jalal ya dubi Sarki cikin natsuwa ya ce..

​"Ranka ya daɗe, zan wuce, amma kafin nan ina neman wata alfarma. Shawarwari ne akan Maayah, idan har ana son ta sauƙo da kanta ƙasa, to dole sai an kiyaye wasu abubuwa. A koda yaushe tana ganin kanta a sama ne saboda waɗannan zabga-zabgan mutanen da ke kewaye da ita... Motoci manya guda biyar ne ke rakata makaranta, kowa yana mata abin da take so, shi ya sa ba ta ganin kowa da mutunci."


​Ya gyara zama ya ci gaba..

"Alfarmar da nake nema ita ce, a kullum zan riƙa zuwa har masarautar nan na ɗauke ta mu tafi makaranta tare a motata. Sannan akwai lokutan da zan riƙa zuwa ina koyar da ita a gida. Kuma gaskiyar magana, dole sai an mata repeat ɗin aji, an dawo da ita baya. Tana SS3 amma koda rubutu ba ta iya ba? Idan kuma ta je jami'a fa?"


​Sarki ya jinjina kai, maganar ta ratsa shi...


​"Wannan batun naka gaskiya ne," in ji Sarki cikin damuwa.. "Mahaifiyarta ta dage ne akan sai an kai ƴarta makaranta domin ta yaƙi jahilci. Mahaifiyar Maayah a baya malamar jami'a ce dake ƙasar Mumbai, har ta samu lambobin yabo masu yawa a fannin ilimi. Ina jin shakkar ranar da za ta ga ƴarta a haka. Na yi mata alƙawarin zan kai mata Maayah hutu nan ba da jimawa ba, amma yanzu na fara karaya. Domin na tabbata idan na kaita a haka, mahaifiyar za ta binciki ƙwaƙwalwarta ta ga babu komai."


​Sarki ya kalli Jalal sannan ya furta


"Shi ya sa yanzu, ko me kake buƙata, indai za ka dawo min da ƙwaƙwalwarta, to na amince. Ba ni da burin kaita jami'a yanzu, ina jiran ne ta kammala SSCE sai na musu aure gaba ɗaya, amma yanzu komai ya dawo baya... Jalaludden, zan ninka maka kuɗaɗen da ake baka a makaranta sau biyar don ka gyara ta. Za ka riƙa zuwa kana mata home lesson, sannan ka dage mata a makaranta. Idan ta ƙi ba ka haɗin kai, na ba ka izinin ka bulale min ita."


​Uncle Jalal ya girgiza kai cikin nuna rashin kwaɗayin abin duniya...


​"Zan yi iya ƙoƙarina Ranka ya daɗe. Amma ba na buƙatar kuɗin da za ka ƙara min don kawai kana so na gyara ƴarka. Nima ina so na gyara ta ne ta zama abin misali a fannin ilimin boko da na Arabic."


​Sarki ya yi murmushi, ya tambaye shi,  "Daga ina kake? Wato kai ɗan ina ne?"


​Uncle Jalal ya amsa. 

   "Ni ɗan Nigeria ne, daga yankin Borno State. Kuma a nan ina zaune ne a The Royal Palace Hotel..." 

 (Wani babban hotel ne mai tsada da kwarjini a birnin Alhamra)..


​Daga nan, Uncle Jalal ya yi sallama da Sarki ya miƙe ya fice daga sashen, ya bar Sarki cikin tunanin yadda wannan malamin zai fara jujjuya Maayah....



GA TAMBAYA

SHIN WANI SCENE NE YA FI BURGE KU? 

ZAYANA KO MAAYAH?....



 *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 


👍 Like

🔁 Share

💬 Comment

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post