Falasɗinawa za su fara tsallaka iyakar Rafah bayan kwashe shekara biyu a rufe

 

Falasɗinawa za su fara tsallaka iyakar Rafah bayan shekara biyu a rufe
Asalin hoton, Khames Alrefi/Anadolu via Getty Images

A yau, Falasɗinawa za su fara tsallaka iyakar Rafah tsakanin zirin Gaza da Masar, wadda aka rufe kusan shekaru biyu bayan sojojin Isra’ila sun karɓi wasu sassa na Gaza.

Sake buɗe mashigar Rafah, wanda aka dade ana jinkirta shi, wani muhimmin sashe ne na yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaba Trump ya tsara a Gaza.

Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta ce za a bar marasa lafiya 50 tare da iyalansu biyu su tsallaka iyakar kowace rana, sannan wasu mutum 50 daga cikin waɗanda suka bar Gaza a lokacin yaƙi za a ba su izinin komawa.

Yanzu haka, dubban Falasɗinawa marasa lafiya da masu rauni na jiran damar barin Gaza domin neman magani.

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post