Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa mutum 80 daga cikin wadanda aka sace daga coci uku a Kurmin Wali, Kajuru, sun dawo gidajensu lafiya, makonni bayan aukuwar lamarin.
Mutanen na cikin mutum 177 da aka yi garkuwa da su. Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansur Hassan, ya shaida wa manema labarai cewa wadanda suka tsere sun yi hakan ne a ranar da aka sace su, yayin da ’yan bindigar ke ƙoƙarin kwashe su zuwa wani wuri.
Bayan tserewar, mutanen sun ɓuya a wasu ƙauyuka na kusa tsawon makonni har sai sun ga cewa wurin lafiya ne kafin su dawo gida. An tantance lafiyarsu sannan aka haɗa su da iyalansu.
DSP Mansur ya kara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutum 87 da har yanzu ke hannun masu garkuwa.
Harin na Kurmin Wali ya zo ne a lokacin da matsalar tsaro ke addabar arewacin Najeriya, inda hare-haren ’yan bindiga, sace-sacen mutane, da kashe-kashe ke yawaita. Hukumomi sun ce suna ƙara tsaurara matakan tsaro da haɗa kai da al’umma domin rage irin waɗannan hare-hare.
Tags
Labaru
