_Bossladieswriters_
_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q
WhatsApp Group
https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 7
......Sanye da rigar bacci robe irin mai buɗaɗɗen gaba wadda ake ɗaurewa tsawonta iya gwiwa Deen ya fito daga cikin walk-in closet ɗin shi ya nufo cikin ɗakin yana tafiya a nutse da alama ya gama yin shirin kwanciya sai ƙamshi jikinsa ke saki, gadonsa ya nufo ya zauna daga gefe idon sa akan Fahad dake a kishingiɗe shima ya yi shirin kwanciya jikinsa sanye da pajamas, waya ce riƙe a hannunsa yana lallatsawa, a hankali ya ɗago idanunsa ya sauke su akan Deen suka yi ma juna murmushi,
"Na yi zaton zan iske ka ka yi bacci saboda gajiyan dinner." Deen ya faɗa yana gyara zaman shi ya ɗan haye saman gadon kafarsa guda na a ƙasa, idon Fahad akan shi da ɗan murmushi ya ce, "Ba wani gajiya ai, kaine ma ke da gajiya an sha fama da mutane, yakamata by now ka yi bacci ka samu hutu sosai." Hannu Deen ya kai ya shafi yalwatacciyar sumarsa dake ta salƙi da alama a daren ma sai da aka gyara ta,
"Da muka dawo ya ɗauke ni time ina duba saƙonni, amman yanzu zan kwanta ɗin." Kai Fahad ya jinjina mashi.
"Gobe zamu tafi Funtua tare ina son je in ga sweety hajjanah." Ya faɗa da ɗan faffaɗan murmushi,
"Da wuri haka, na yi tunanin zaka bari sai bayan kwana biyu in ka huta sosai." Fahad ya faɗa yana kallon shi.
"No, gara mu tafi kawai, ko na tsaya ba wani hutun da zan yi, I received a lot of invitations from different football clubs, duk suna son in je mu tattauna game da yadda suke wasa. So, ina son in yi honour wasu daga cikin invitations ɗin kafin na koma." Kai Fahad ya jinjina masa, jin alamar shigowar mutum ya sa gaba ɗaya suka kai idanunsu kan ƙofar shigowa, mom din Deen ce ta shigo cikin ɗakin jikinta sanye da jar silky doguwar rigar bacci da ta fito da ƙirarta sosai kanta ta yafa ƙaramin baƙin gyale, nufo cikin ɗakin ta yi tana tafiya cike da isa yanayin fuskarta a ɗan ɗaure, tun kallo ɗaya da Fahad ya yi mata ya ɗauke idonsa tare da mayar da su akan wayar hannunsa, idon Deen na akanta cikin ransa yana ayyana ko miye dalilin zuwan ta ɗakin shi a irin lokacin, daga gefen shi ta tsaya ta bi Fahad da wani irin kallon rashin arziƙi wanda shi bai ma san tana yi ba idon shi na akan wayarsa,
"Mom, baki yi bacci ba?" Deen ya tambaya yana kallonta, maido idonta ta yi kansa ta ƙara ɗaure fuskarta.
"Ai kai zan ma wannan tambayar, mi kake baka yi bacci ba, kai da ka kwaso gajiya amman wani ne a kwance saman gadon kai a zaune!" Yadda ta yi magana ya bayyana ta ji haushin ganin Fahad da ta yi a kwance saman gadon, kallo Deen ya bita da shi ya ɗan yamutsa fuska ganin ta kafe shi da ido alamar amsar shi take jira, kamar bazai ce komai ba don ya ji haushin maganarta sai dai gudun kada ta ƙara kwa6o wata baƙar maganar ya sa shi cewa,
"Ba wani dalili ya sa na zauna ba ni ke ra'ayin hakan, na tsaya yin wani abu, da kin zo bayan yanzu za ki iske ni a kwance ne." Daga yanayin yadda ya yi maganar ta fuskanci alamun bacin rai akan fuskar sa, ɗan ta6e baki ta yi ba tare da ta ce komai ba ta fara tafiya zata bar ɗakin, sai da ta yi taku biyu zuwa ukku ta dakata tare da juyowa ta kalli Deen da ya bita da kallo, cike da bada umarni ta furta, "Fallow me, I want to talk to u. " Daga haka ta ci gaba da tafiyarta, ɗan jim ya yi kaman ba zai tashi ba, kallon Fahad ya yi da har lokacin bai ɗago ba, shiru ya ɗan yi ya ma rasa mi zai ce mashi don duk da bai ga yanayin fuskarsa ba ya san dole maganar da mom ɗin ta yi ta 6ata masa rai, hannu ya kai ya ɗan ta6a ƙafar Fahad dake gefen sa ya furta, "Ina zuwa ya Fahad." Kai kawai Fahad ya jinjina masa ba tare da ya kalle shi ba, zuro gudar ƙafarsa ya yi ya sauka daga gadon ya bi bayanta. A hankali Fahad ya ɗago ya bi hanyar fita daga cikin ɗakin da kallo yanayin fuskar sa da ɗan alamun bacin rai, a cikin ransa yana jin ɗacin irin abubuwan da matar take mashi, shi dai ya san bai ta6a yi mata wani laifi da ya cancanci wannan tsanar ba daga gare ta, duk da ya san halinta ne bashi kaɗai take ma hakan ba amman nashi ya fi tsanani, sam bata son shi da Deen ga shi Allah Ya saka masu ƙaunar junan su kuma ga zumuncin da Allah Ya halarta a tsakanin su, ba don haka ba ai da tuni ya rabun mata da ɗa. Maida akalar tunaninsa ya yi kan Leemarh, daga abun da ya faru yau a wurin dinner ya tabbatar mashi da yarinyar son shi take kamar yadda yake hasashe, duk da shi bai ta6a tunanin ya yi soyayya da ita ba, amman in har ta bayyana mashi hakan to tabbas ba zai ƙi amince mata ba, duk da a yadda take ta yi mashi ƙaranta da kalar matar da yake son aura, a yadda yake so ya auri budurwa babba irin wadda ta gama karatun jami'a koma take aiki, amman duk da hakan yana jin zai iya auran Leemarh don tana da duk wani abu da namiji zai so a tare da mace, saidai ta ya hakan zai yuwu a tsakanin su a irin yadda mahaifiyarta ta tsane shi? Ana yin aure ne don samun farin ciki da natsuwa, amman baya tunanin hakan zai samu matuƙar aure ya kasance tsakanin shi da Leemarh, ƙarshe ya san madadin hakan ya ƙara masu danƙon zumunci yana iya lalata zumuncin wanda shi sam ba zai so hakan ba. Ahalin su babban family ne da suke da zumunci mai ƙarfi, suna da kyakkyawar alaƙa da kuma fahimta ba zai so a ce ta sanadiyyar auren su ba an zo an samu 6araka, don a yadda ya san rashin mutuncin mom Jameela to zata aikata abun da zai iya haddasa a samu babbar matsala matuƙar bata son hakan. Yin wannan tunanin ya sa shi fara tunanin hanyar da zai bi wurin ganin Leemarh bata furta mashi kalmar so ba duk da zai so a ce ya cika mata burinta, saidai baya tunanin hakan mai yuwuwa ne gara su haƙura kawai ko don a zauna lafiya. Bayan daukar ɗan lokaci yana tunane-tunane, saukowa ya yi daga saman gadon ya mike tsaye, cikin ɗakin ya nufa walking slowly, wurin da madaidaicin fridge yake ya nufa ya buɗe, bayan ya ɗauko lemu ya dawo cikin ɗakin riƙe da shi, a bakin gadon ya zauna har zai fara buɗe marfin lemun sai kuma ya dakata kamar yana ɗan tunani, wani abu yake son ɗaukowa a cikin motar shi sai dai yana tunanin ko su Deen na a cikin falon bai son ya je ya ratsa su suna magana, ɗan jimm yay can ya miƙe tare da ɗaura roban lemun a saman durowar gefen gadon, sai da ya buɗe durowan farko ya fiddo makullin mota kafin ya nufi ƙofar fita.
Cikin sa'a bai iske su a cikin falon ba, har ya nufi ƙofar fita ya tuna da akwai wata kofa ta cikin falon da zata fidda mutum ta bayan gidan ta fi sauƙi zuwa inda parking space yake, juyowa ya yi ya nufi ƙofar cikin sa'a da makulli a jikinta ya buɗe ya fita.
Lokacin da Deen ya fito ya yi tunanin zai ga mom ɗin ta shi a cikin falonsa amma sai ya ga akasin hakan, hanyar fita ya nufa da tunanin ko bangarenta ta koma, tsaye take ta ɗaura hannuwanta a saman ƙarfen bene idanunta na kallon cikin ƙaton falon na su dake a ƙasan bene ta haɗe rai,
"Mom..." Ya furta bayan ya ƙaraso ya tsaya daga gefenta, shiru bata amsa ba bata kuma juya ta kalle shi ba, "Kin ce kina son magana da ni." Ya sake faɗa yana mai kallon ta ta gefe, a hankali ta juyo da fuskarta ta kalle shi kafin ta ƙarasa juyowa gaba ɗaya tana fuskantar sa,
"Wai mike damun ka ne Deen?? Ta faɗa da amon bacin rai, ɗan buɗa idanunsa ya yi alamar rashin fahimta, ba tare da ta jira cewar sa ba ta ci gaba, "Har sai yaushe ne zaka dawo cikin hankalinka ne ka rinƙa yin abu yadda ya kamata?Yaushe ne zaka daina cutar kanka ka daina prioritizing buƙatun wasu fiye da naka? Yaushe zaka gane cewa wasu mutanen ba kamar yadda kake ɗaukar su bane, ba don Allah suke tare da kai ba face don amfanin kan su ba kamar saboda baiwar da Allah Ya yi maka, da zarar sun gama cin moriyar ka za su guje ka ne. I have been trying to make you understand all these things over and over again, but you just don't get it! Yakamata ka dawo cikin hankalinka, Deen!"
Idanunsa akanta har ta gama maganganun nata, sai dai shi sam ya rasa gane kan maganganun balle ya fahimci akan mi take faɗan,
"Mom, kina magana akan miye ne? I don't get u..."
A ɗan fusace ta ce, "Dama ta ya zaka fahimce ni tun da an riga an makantar da kai, baka ji baka gani balle ka fahimta. Ina magana ne akan wancan mutumin mara tunani." Ta yi maganar tare da yin nuni da kofar part ɗin sa, da yanayin mamaki ya ce, "You mean ya Fahad! Minene ya yi na rashin tunani?"
"Idan ba rashin tunanin ba ta ya yana ganin yau fa ka zo ƙasar nan, baka samu ka huta ba sosai maimakon ya taimaka maka ka kwanta ka huta amman shi ne a kwance a saman gadonka ɗare-ɗare ba ko kunya kai kuma bawansa a zaune!" Yanayin fuskarsa ne ya sauya zuwa yanayin bacin rai, bin ta ya yi da ido a ransa yana mai mamakin yanzu miye wani abu a cikin hakan da har zatai ta yin faɗa,
"Oh, baka da ma abun da zaka ce mani ke nan? ka wani bi ni da ido ga mahaukaciya na magana ko?"
Ɗan yamutsa fuska ya yi cikin alamun bacin rai ya ce, "To mi kike so in ce ne? Yanzu mom don Allah miye abun tashin hankali a ciki da zaki ta faɗa? I think i have already told you, ni ne ban kwanta ba na tsaya yin abu, ko kuwa ni ƙaramin yaro ne ban san ciwon kai na ba da sai wani ya faɗa mani in kwanta kafin na yi hakan? Idan shi yana buƙatar ya kwanta ya huta sai ya ƙi yin hakan saboda ni ban kwanta ba? Ko kuwa don yana gadona sai ya zama ya yi laifi don ya kwanta a sama? Dama abuna ba na shi bane, har akwai wani bambanci a tsakanin mu....?
Have you forgotten that he is my brother? A gidan nan fa ya taso da har zaki ce wai da wani dalili yake tare da ni, idan ya gama cin moriyata zai guje ni. Ok mu dauka ma haka ne, to me, it's fine, zan yi faran ciki a ce ina da abun da ɗan'uwana zai amfana, koda ni zan rasa hakan bai dame ni ba, what would really hurt me is if he ever turns his back on me...that’s what would matter." A hasale ta katse shi,
"Enough Deen! Saboda ina faɗa maka gaskiya zaka tsaya akai na kana mani wannan surutan! I'm your mother, dole na damu da kai na baka kulawa daga abun da nike ganin zai cuceka saboda tunanin mu ba ɗaya bane kai ba zaka gane abun da nike hango maka bane, sannan sam ni bani son tarayyarka da shi don zai iya saka ka ka lalata rayuwarka kamar yadda ya lalata tashi rayuwar da shaye-shaye..." Ɗan jujjuya kai ya yi jin abun da kuma zata fake da shi, yanayin idanunsa har sun ɗan sauya kala, wllh ya gaji da wannan halin na mahaifiyarsa, son kanta ya yi yawa, bai san mi yasa ta tsani Fahad haka ba wanda sam hakan bai mashi daɗi don kuwa idan akwai mutumin da yake jin shi a cikin ransa bayan su iyayensa to kuwa Fahad ne,
"Mom, in kin san a in da nike rayuwa kin san da suwa nike tarayya? Kin san inda nike shiga a cikin duniyar nan? Kin san wani kalan mutane nike haɗuwa da su? Kin san irin abubuwan da idanuwana suke gani kunnuwana suke ji mom? Duk wannan basu lalata ni ba sai ya Fahad? Mutumin da zan iya rantsuwa akan ban ta6a gani ya sha wani abu da sunan ƙwaya ko abun maye a gaban idanuna ba, kuma kema na tabbata baza ki ce kin ta6a ganin hakan da idon ki ba. Mom, don Allah ina son in tambaye ki, and I don't want you to hide the truth from me, ya Fahad ya taba maki wani laifi ne da ya sa kika tsane shi, baki son shi a kusa na?" Fuska a yamutse ya yi mata tambayar, harara ta watsa mashi ta ce, "Yaushe mu ka yi da kai cewa na tsane shi? Kawai ni ina baka kariya ne daga duk abun da na hango zai cuce ka, ni ban yarda da shi ba, ba don Allah yake tare da kai ba kuma ban son tarayyar ku don zai iya jan ra'ayinka tun da kafi jin maganarsa akan ta kowa har mu iyayenka...." Ta ƙarasa maganar tana ƴan kame-kamen rashin gaskiya, ɗan murmushi wanda ya fi kama da a kira na takaici ya yi, kafin ya furta, "To na gode da kariyar da kike bani, amman Allah shi zai kare ni daga duk wani cutarwa ina roƙonsa hakan kuma ina da yaƙinin yana amsar addu'ana, don haka ina roƙon ki da ki ƙyale mu mu yi zumuncin da Allah Ya halatta a tsakanin mu..."
Ni na tabbata ba don wani abu ya Fahad yake tare da ni ba, mutumin da tun da nike da shi bai ta6a buɗe baki ya ce na bashi kuɗi ba ko na siya mashi wani abu, ko kuma ya ga wani abu nawa ya ce na bashi. Duk abubuwan nan babu wanda ƴan'uwana basu tambayana har da ma wasu da ba ƴan'uwana ba, ke nan suma sai a ce duk cutata suke saboda ina basu abu? Dama idan Allah Ya buɗa maka don ka yi amfani kai kaɗai ya baka ne? Don ka ba wasu ne shi yasa yake ƙara baka, kuma idan kana badawa baka ta6a rasawa. If there’s nothing else you want to tell me, please allow me to go."
Ya ƙarasa idanunsa na kallon gefe ya ɗaure fuska, bin shi da kallo ta yi ta lura da ran shi ya 6aci sosai, ta san yana da sauƙin kai da kauda ido, ba kowane abu ne ke saurin 6ata mashi rai ba, amman fa yana da zuciya idan ransa ya 6aci yana iya ɗaukar lokaci bai sauko ba, kuma zai iya yanke hukuncin da kowa zai iya shiga cikin damuwa, tunanin zai iya ma ya ce zai koma ne ya zo a ranta hakan yasa ta saki fuskarta, ɗan guntun murmushin da ba har zuci ba ta yi ta ce, "Ka yi hakuri yalla6ai na ta6a ɗan lelenka, wanda ya fi kowa muhimmanci a wurin ka gashi har na 6ata maka rai, watarana na san zaka fahimci abun da nike nuna maka."
"Can I go?" Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba, ɗan yamutsa fuska ta yi ta ce, "Yanzu ke nan ku biyo zaku kwanta a saman gadon? Amman zaka iya takura ai, why not shi ya koma bangaren baƙi tun da akwai komai a can kowa ya fi sakewa..." Kafin ta rufe baki ya furta, "Shi ba baƙo bane, ba wani abu zamu kwanta tare. Gud nyt." Ya bata amsa a taƙaice tare da wucewa ya nufi komawa part ɗinsa yana tafiyarsa mai cike da natsuwa, bin shi da kallo ta yi ta tamke fuska tamau sai ka ce bata ta6a yin dariya ba har ya shige ciki ya maido ƙofa ya rufe, ɗan cije le6enta na ƙasa ta yi na ɗan lokaci kafin ta saki ta yi ƙwafa da ƙarfi ta furta, "Mu zuba ni da kai Deen!" Nufar sauka daga benen ta yi a cikin ranta tana saƙa cewa duk hanyar da zata bi sai ta ga ta raba tsakanin su, ba tun yanzu ba ta sha yin yunƙurin hakan lokutta daban- daban amman ta kasa yin nasarar hakan.
Cikin falonsa ya shigo ya nufi kujera ya zauna, ransa a 6ace ya ɗage kansa sama tare da rufe idanunsa, ya yi hakan ne don ya samu sassaucin 6acin ran da yake ji kafin ya koma cikin ɗakin gudun kada Fahad ya fahimci wani abu. A hankali ya shiga tunano lokuttan baya irin yadda ta rinƙa yi ma Fahad izaya da yana a gidan amman duk da irin abubuwan da ta yi mashi hakan bai sa ko sau ɗaya ya janye masu ba a matsayin su na ƴan'uwansa, tunanin hanyar da zai bi ya ga ya yi maganin abubuwan da take yi ma dangin mahaifinsu ya shiga yi don hakan baya mashi dadi sam, a ganin sa har da laifin dad ɗinsu, shi yakamata a ce yana taka mata burki kan hakan amman baya ɗaukar matakin da ya dace shi yasa abun nata har ya girmama haka.
Bayan ya ɗan ji sassaucin ransa ya mike ya nufi cikin ɗakin, yana shiga Fahad dake zaune a gefen gado ya jingina bayansa da jikin gadon ya ɗago idonsa ya kalle shi, nufar shi Deen ya yi yana ƙoƙarin daidaita yanayin shi gudun kada ya fahimci wani abu, a bakin gadon gefen shi ya zauna yana masa ɗan murmushi ya ce, "I thought zan iske ma ka yi bacci." Ɗan girgiza masa kai kawai Fahad ɗin ya yi ba tare da ya furta mashi komai ba, bin shi da kallo Deen ya yi ganin yadda ya yi shiru ya ɗan lumshe ido, tunanin ko ran shi ne ya 6aci kan abun da mom ta shigo ta faɗa ya shiga yi, a hankali ya kai hannu ya dafa cinyar Fahad ɗin fuska a ɗan marairaice ya ce, "Pls ya Fahad ka yi haƙuri akan abun da mom ke yi maka, na san hakan na 6ata maka rai sosai kawai kana kauda kai ne saboda zumuncin dake a tsakanin mu. Wllh sam bana jin daɗin abubuwan da mom ke yi ba tun yanzu ba, kawai na rasa yadda zan yi maganin abun, kuma ni ina ganin duk laifin dad ne, yakamata a ce yana tsawatar mata sosai..." Shiru ya yi yana kallon gaban sa fuskarsa da alamun baccin rai, sai da Fahad ɗin ya ɗan ɗauki lokaci kaman ba zai ce komai ba can ya ɗan yi yar ajiyar zuciya ya ce mashi ya daina damun kansa ai duk sun riga sun san halinta ne hakan, yadda ya yi maganar slowly ya sa Deen tunanin ko bacci yake ji, kallon shi ya yi ya ce mashi ya kwanta mana, shiru ya yi masa tare da lumshe idanunsa, kai idanunsa ya yi kan sauran lemun da ya sha ya rage, tunaninsa ya ƙoshi ne ya sa ya ajiye akan durowar, hannu Deen ya kai zai ɗauka ya ce bari ya ƙarasa shanyewa, yana kai hannu jikin robar ya ga Fahad ɗin ya yi saurin riƙe mashi hannu alamar hana shi ya ɗauka, da alamun mamaki Deen ya kalle shi sai kuma ya yi tunanin ko bai gama sha bane, fasa ɗaukar lemun ya yi ya ce mashi ya yi tunanin ya gama da shi ne tare da komawa ya zauna, bin Fahad ya yi da kallo ganin ya buɗe lemun ya kai baki, saida ya kwankwaɗe shi duka sannan ya cire robar ya maida marfin tare da mayar da ita saman durowan, a hankali yake ta lumshe idanunsa yana buɗewa, lokaci guda Deen dake kallon shi ya fara zargin kamar akwai abun da ke a cikin lemun shiyasa ma ya hana shi ɗauka kuma ya ƙi sakin jiki ya yi magana da shi sosai sai faman lumshe ido yake. Ya san da gaske ne Fahad na amfani da ƙwayoyi sai dai bai ta6a sha ba a gaban sa, haka idan ya sha bai sakin jiki sosai don kada ya gane, ya lura da irin kallon da Deen ke yi masa hakan ya sa shi ƙarasa hayewa saman gadon ya kwanta tare da ba Deen ɗin baya, jimm Deen ya yi na ɗan lokaci yana kallonsa kafin ya kai hannu ya ɗauko robar ya buɗe, kai bakinta ya yi saitin hancinsa ya ɗan sunsuna, daga ƙamshin da ya ji a ciki ya tabbatar masa da zargin da yake, mayar da robar ya yi ya juya yana kallon bayan Fahad, har cikin ransa tausayi yake bashi saboda shaye-shayen ƙwayoyin da yake yi, wanda a da sam hakan ba halinsa bane daga baya ƙaddarar ta haye mashi, hannu ya kai ya ta6a jikinsa tare da kiran shi a hankali, shiru bai amsa mashi ba ya san yana jin shi tun da bai daɗe da kwanciya ba, hakan yasa shi fara yin magana cikin kwantar da murya,
"Ya Fahad, ka yi haƙuri idan abun da zan faɗa maka zai 6ata maka rai, duk da this is not the first time da na fara maka magana kan hakan, kuma wannan ba shine karo na ƙarshe ba, zan ci gaba da yi maka magana akan haka har zuwa ranar da Allah zai amsa addu'ana in ga ka daina. Please ya Fahad, you really should stop using drugs, a matsayin ka na medical doctor ka san irin illar da suke yi ma lafiyan mutum, hakan kuma yana da matuƙar haɗari ga aikin ka. Ba zan boye maka ba abun yana damuna sosai bro. I wouldn't want this to jeopardize your future." Fuska a yamutse ya ƙarasa magana, shiru Fahad ɗin ya yi bai tanka masa ba idanunsa na a rufe. Koma ya yi bacci bai sani ba? Tunanin da Deen ya yi ke nan, sai dai yana kokonton in ya yi bacci saboda ya san a duk sanda zai mashi magana kan shan ƙwayoyin da yake yi bai cika tanka masa ba sai dai ya yi shiru, wani lokacin kuma yana bashi amsa da zai daina in sha Allah Ya taya shi addua. Matsawa ya ƙara yi kusa da shi a hankali ya kwantar da kansa a saman jikinsa, Fahad da yana jin duk abubuwan da ya faɗa jin shi a jikinsa ya sa shi runtse idanunsa sosai, har cikin ransa bai jin dadin ganin yana saka mutane damuwa saboda abun da yake yi, saidai duk yadda ya so ya daina abun ya ci tura saboda ya kama mashi jiki sosai.
"Ya Fahad, I think wannan teacher ɗin fa ya haukace, ya bani wannan assignment din ba daidai ba, that's why inata wahala amman ya ƙi ya yi daidai."
Kaman daga sama Fahad ya tsinkayi muryar Deen a cikin kansa, duk da ya ɗan fita hayyacinsa amman komai na zuwa mashi a cikin kansa kuma yana fahimta, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa tunowa da can baya lokacin suna yara, duk aka ba Deen assignment ya kasa yi sai ya iske shi ya yi mashi wannan maganar da ya yi, da yake lokacin Fahad ɗin na yawan yi mashi faɗa kan yadda bai maida hankali sosai akan karatu ya fi mayar da hankali akan kwallo, to shine idan ya kasa yin assignment ya kawo mashi, gudun kada ya yi masa faɗan sai ya fake da cewa malami ya haukace ya bashi assignment ba daidai ba,
You are the one who has gone mad, shiyasa ka kasa yin shi yadda aka koya maka." Fahad ɗin ne ya faɗa slowly, faffaɗan murmushi Deen ya saki ya ji dadin yadda ya bashi irin amsar da yake bashi a lokacin, duk da a yanzu bai kama mashi kunne ba kamar yadda yake mashi a lokacin, ɗago kai Deen ya yi yana kallon fuskarsa ya ce, "I thought ka yi bacci da na yi magana na ji baka ce komai ba." Ɗan shiru Fahad din ya yi kaman ba zai ce komai ba,
"In sha Allah na kusa dainawa. Ka taya ni da addu'a Pls" Ya ji ya faɗa ba tare da ya juyo ba.
"Ina yi maka addu'a a koda yaushe, ba akan wannan ba kaɗai, kuma zan ci gaba da yi maka har ƙarshen rayuwana, In sha Allah." Kai ya ɗan jinjina masa tare da ce mashi ya gode.
"Ya Fahad yaushe zaka yi aure ne? Yakamata a ce zuwa yanzu kana da mata har ma mun samu baby, ka ga nima na samu wanda zan rinƙa nunawa a matsayin yaro na." Deen ya faɗa yana ɗan murmushi, ganin Fahad ɗin na kokarin juyowa ya sa shi gyara zaman sa, bin shi ya yi da kallo da lumsassun idanunsa a hankali ya furta, "Kai nike jira ka yi mani." Yar dariya Deen ya yi ya ce, "Serious, idan kana so sai in yi maka, ko gobe ma lafiya lau za a iya ɗaura maka aure. Who's the girl you want to marry?" Hannu Fahad ya ɗan yarfa ya ce mashi babu, amman tun da shi ne zai mashi auren sai ya samo mashi matar,
"Samun matan ba matsala bane ai, na san akwai babes dake son ka, ɗazun ma a wurin dinner ai na ga ka samu, a cikin gidan nan ma na ga alamun ka yi kasuwa..." Ya karasa yana sakin faffaɗan murmushi, shima Fahad ɗan murmushi ne akan fuskarsa, ya fahimci akan Leemarh yake magana, bin shi kawai ya yi da kallo still idanunsa na ɗan lumshewa yana buɗa su.
"Idan kana son Leemarh ka shirya ma auren ta let me know, zan sanar ma dad, tun da lafiya lau ta isa aure sai ta yi completing karatunta a gidan ka." Ɗan girgiza masa kai Fahad ya yi ya ce ba soyayya suke ba kawai shaƙuwa ce,
"Da alama dai so kake in riga ka yin aure tun da ni ina da wadda zan aura, ko kuma in ce wadda aka za6a mani in aura." Yadda ya ƙarasa maganar zaka fahimci abun ba da son ranshi bane, kallon shi kawai Fahad yake yi can ya ɗaga hannu ya dafa shi ya ce, "You should not worry about that, idan Allah bai ƙaddara ita ce matar da zaka aura ba baza ka aure ta ba."
"You're right. Idan ita Allah Ya za6a mani na kar6a, Allah Ya sa hakan ya zama alkhairi." Amsa mashi Fahad ya yi da Amin, suka ɗan yi shiru kafin Fahad ya ce mashi ya je ya kwanta dare ya yi gashi ya ce gobe tare za su tafi, miƙewa ya yi ya nufi ɗaya bangaren gadon, yana cikin tafiya yake tambayar Fahad gobe zai je wurin aiki ne, amsa ya bashi da ya so ya yi sammako don ya fara tsayawa wurin aikin to amman tun da tare za su tafi hakan ba zai yuwu ba, zai kira ya ƙara bada uzuri kawai sai su wuce Funtua, Deen ya ce kada ya yi haka goben idan Allah Ya kaimu da wuri za su tafi sai su fara tsayawa wurin aikin nashi kafin su wuce Funtua, Fahad ya amsa da ok, daga haka suka kwanta bayan Deen ya yi masu addu'a gaba ɗaya. Lumshe ido ya yi yana tariyo abun da ya wakana tsakaninsa da mom, a ransa yake raya gara ma ya yi tafiyar sa Funtua ya san a can zai fi samun peace of mind.
*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*
