A Cikin Rayuwa Page 8 Complete - Abokiyar Hira Novels


_Bossladieswriters_

_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q

WhatsApp Group

https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*    

    _By Zainab Bature_   

  _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

Page 8

Bayan mom ɗin Deen ta koma hamshaƙin katafaren ɗakinta da ya sha royal furniture kai kace wani ɗakin ƴar hamshaƙan masu kuɗi ko masu sarauta ne, a bakin gadonta da ya sha lafiyayyar katifa da shimfidar zanen gado mai kyau ta zauna, hayewa ta ƙarasa yi sama ta zauna tare da jingine bayanta da kan gado sai faman cika take tamkar zata fashe, bata da wani buri a cikin ranta face ta ga ta raba tsakanin Deen da Fahad, sam ta tsani ta gan su tare gani take kamar juya mata ɗa Fahad ke yi yana cin dukiyarsa son rai, ta ɗauki tsawon minti talatin a haka tana ta faman yin tufka da warwara, jin motsin shigowar mutum ya sa ta ɗaga ido ta kallo kofar shigowa, dad ɗin su Deen ne ya shigo yana sanye riga da wando na bacci, ya fito a babban mutum, cikin ɗakin ya nufo idanunsa akanta yana kallonta da ɗan yanayin mamaki, tun ɗazu yana a part ɗinsa yana jiranta, har kiranta ya yi a waya ba a daɗe ba ta sanar da shi tana zuwa tana yin wani abu ne, da ya ji shiru shine yanzu ya biyo bayanta don har sake kiran wayarta ya yi bata ɗaga ba, ganinta zaune ba tare da tana yin wani abu ba ya sa shi yin mamaki. Daga bakin gadon ya tsaya yana kallonta ita kuma tun da ta kalle shi sau ɗaya ta kauda idonta gefe, daga yanayin fuskarta ya gane tana cikin fushi, jikinsa ne ya ɗan yi sanyi don ya san idan tana a cikin irin halin bata saurarar shi, ƙoƙarin zama ya yi daga gefenta idonsa akanta, 


"Gimbiyata, ashe kina nan zaune kin ce mani kina zuwa ina ta jira." Ko kallon shi bata yi ba sai ma ta ƙara juyar da fuska tare da ɗan tura baki, jimm ya yi yana ta kallonta, ya san in dai yana son ta saukko to dole sai ya lalla6ata, 


   "Ya aka yi ne my love? Mi ya faru na ga bacin rai a tattare da ke bacin bada jimawa ba mun yi magana lafiya lau. Pls tell me idan wata damuwar ce zan yi maganinta, in sha Allah." Ya ƙarasa maganar cike da tabbatar mata da abun da ya faɗa, sai lokacin ta ɗan juyo ta kalle shi amman bata saki fuska ba, hannu ya kai ya kamo nata ɗaya ta sigar lallashi ya ce mata yana jin ta minene matsalan, 


  

 "Deen ne! Ban san mike damun shi ba, sam bai jin maganata, ban isa in nuna mashi abun da nike ganin shine daidai ba ya ji, abun da ransa ke so shine zai yi!" Ta ƙarasa a hasale. 


"SubhanAllah! Wai Deen ɗin? To ya aka yi haka, a yadda na sani Deen yana jin maganarmu sosai har ma ya fi duk sauran ƴan'uwan shi, ba laifi yana yi mana biyayya..." Da sauri ta katse shi ta ce, "Idan ba akan ɗan lelensa ba ko? Ai ba a isa a yi mashi magana ba idan dai ta shafi Fahad ya ɗauka." Shiru dad ya yi yana kallonta, dama ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, matuƙar aka ce Fahad ya zo gidan dama aka zatai ta taƙalo abubuwa tai ta faman maganganu, yar ajiyar zuciya ya yi ya ce mata wani abu Fahad ɗin ya yi, kaman tana jira ta hau faɗa mashi ƙabli da ba'adi ta ce wai ta je ɗakin ta iske shi Deen a zaune har yana ɗan gyangyaɗi amman shi Fahad ɗin yana baje saman gadonsa sai sharar baccin shi yake, kuma ta san saboda Fahad ɗin na kwance ne yasa Deen bai kwanta ba ga gajiya a tattare da shi, shine daga ta kira shi a waje don kada ma Fahad ɗin ya ji ransa ya 6aci, ta yi mashi magana kan mi zai hana Fahad ya tafi part ɗin baƙi ya kwanta shima ya fi sakewa ya kwanta sosai, shine fa ya hau yin maganganu yana faɗin wai ta tsani Fahad bata son su a tare, shi dai ta bar su su yi zumuncin su...haka tai ta faɗi ma dad ɗin karya da gaskiya, bayan ta gama maganar shiru dad ya yi yana ɗan jinjina kai, sam bai yarda da maganganun nata ba, idan ba neman abun magana ba tun farko mi zai kaita part ɗin Deen a lokacin bayan ta san yana jiranta, sanin halinta in har bai goya mata baya ba to kuwa ba zai samu ta sauko ba har ta kula shi ya sa shi nuna mata bai ji dadin abun da Deen ya yi ba, 


   "Ban ji daɗin hakan da  Deen ya yi ba, in baya ga abun shi ba don duk jin daɗin su saboda kada su takura ya sa kika bashi shawaran hakan ba, shine zai faɗi maganganu marasa daɗi haka. Ki ƙyale ni da shi, idan Allah Ya kaimu zan tsawatar masa kan hakan, ya kamata yana fahimtar abu yadda yake, kuma dama duk lokacin da Fahad ya zo gidan ba a part ɗin baƙin yake sauka ba..." Caraf ta amshe maganar, 



"Wataƙil ai kai in ka gaya mashi ya fahimta, ni dama a koda yaushe tawa zafi take balle har a fahimce ni, kuma ni kaina ai har da ganin a can din yake sauka yasa na ce ya koma can ba wani abu ba...." Matsawa ya fara yi kusa da ita har lokacin yana riƙe da hannunta guda, ɗan janyo ta ya yi zuwa jikinsa farko ta ɗan toge, saida ya ɗan sa ƙarfi sannan ya rungumo ta ta gefe cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ki damu gimbiyata, na ce zan tsawatar masa na san zai ji ba zai sake ba, kuma kin san Deen ba wasu shekaru ne da shi sosai ba kawai har da girman jiki, shiyasa wani abun ba zai yi nazari ba balle har ya fahimci abun da ake nuna masa." Tana jin ya faɗi haka ta samu damar amayar da wani abu daga cikin ainihin abun da ke a ranta,


   

"Har da hakan ya sa ni sam ban cika son ma yana samun kusanci da Fahad ɗin ba sosai wllh, ka dai san halin Fahad na shaye-shaye tsaf zai iya jan hankalin sa kan hakan tun da Deen ɗin yana ji da shi sosai yana ɗaukar maganar shi." Shiru ya yi yana juya maganarta a cikin ransa, ya san da Fahad na shaye-shaye don a can baya lokacin yana cikin yin karatu a Malysia abun ya fi yin ƙamari sosai, akwai lokacin da har saida ya samu matsala da karatunsa saboda hakan, har ta kai sun samu sa6ani tsakanin sa da mahaifinshi ya yi fushi da shi, har da shi cikin wanda suka yi kokarin ganin komai ya daidaita, amman a tunanin shi in da Fahad ɗin zai ja ra'ayin Deen har ya koya mashi shaye-shayen da tuni hakan ya faru tun da ba yau suke a tare ba,


  

 "Ki kwantar da hankalinki, In sha Allahu hakan ma baza ta faru ba tun da ai ba yau suke tare ba, kuma yanzu sai a dade ma basu kasance tare ba. Mu gode ma Allah, domin Deen nutsattsen yaro ne, a irin sana'ar da yake yi ta yawo ƙasashe daban daban, yana haɗuwa da mutane iri-iri daga masu tarbiya zuwa marasa tarbiya, amman babu abun da ya canza na daga kyawawan halayensa. Duk da ba a tare muke da shi ba in da halinsa ya gurbata zamu sani, har Maleek na kan yi mashi magana da ta shafi halayen Deen saboda kula, amman koda yaushe yana nuna mani halayen shi lafiya lau ba matsala kuma yana yabon Deen ɗin kan yadda ya tsare mutunci bai bari ɗaukakar da Allah Ya yi mashi ta ruɗe shi ga aikata sabon Allah ba, kamar yadda da yawa waɗanda suka ɗaukaka suke yin amfani da damar wurin gurbata rayuwarsu. Mu ci gaba da yi mashi addu'ar neman shiriyar Allah har da ma shi Fahad ɗin, saboda zumuncin Allah da ƴan'uwantaka ba zai yuwu a raba su ba." Shiru ta yi ta ɗan tura baki tana ƙara jin bacin rai ganin haƙarta bata cimma ruwa ba, a rashin tunaninta yadda ta so dad din ya goya mata baya su raba tsakanin su.


  

 "Don't worry my queen, na ce zan tsawatar masa ba zai sake ba ehen..." Ya yi maganar yana cusa fuskarsa tsakankanin wuyanta, ganin yana ƙoƙarin haɗe fuskokinsu ta yi saurin janye tata fuskar ta fara ƙoƙarin cire jikinta daga na shi, dakatawa ya yi daga abun da yake ƙoƙarin yi ya kalle ta fuskar shi da ɗan yanayin bacin rai, a marairaice ya ce mata miyasa take haka...fuska a yamutse ta ce mashi ya yi haƙuri an 6ata mata rai she isn't in the mood ya bari wani lokacin ko zuwa gobe da safe ne,


  Bin ta ya yi da kallo yana jin ran shi ya fara ƙuna, ya gaji da irin wannan halin nata, sau da yawa haka take hana shi hakkinsa idan ya nema, ba dama ai mata abun da ranta zai baci shike nan sai ta hana shi hakkin shi kuma sau tari ita ke janyo a yi abun da ran nata zai baci, da yawan lokutta yana cutuwa da hakan kawai daurewa ya ke. A can baya akwai lokacin da ya gaji da irin wannan halin nata har ta kai ya kai ƙararta wurin Hajiyar shi wato Hajiyar ambasada domin ta bashi shawara, a lokacin ta nuna mashi zaman tare dama sai an yi haƙuri balle kuma an ɗauki shekaru ana tare an tara zuria, ta faɗi hakan ne don bata son shiga cikin sha'anin gidan yaranta amman sarai ta san yana cikin matsala a gidan shi don sam bai yi dacen mata ba, ba kamar yayansa Alhaji Sa'ad ba wato mahaifin Fahad. A lokacin ya roƙi hajiyar kan ta sama mashi wata wadda zai aura, ya yi hakan ne da tunanin idan ya je ma mom ɗin su Deen da zancen cewa mahaifiyarsa ce ta sa shi ya ƙara auren zata yi haƙuri ta bari, don ya sha yin yunƙurin cewa zai ƙara aure ƙarshe ba a wanyewa lafiya tsakanin su har sai ya janye maganar, hajiya ta so bijire ma buƙatar shi don ta san ba lalle a kwashe ta lafiya ba, ta nuna mashi idan yana son ƙara auren shi to ya je ya nemi matar da kan shi, a marairaice ya nuna mata saboda ya yi hakan da farko ya nemi auren Jameela da kansa, gashi yanzu bai jin daɗin zama da ita shiyasa yanzu yake son ta zaba mashi wataƙil ya dace, dama sai da suka ƙalubalanci auren shi da ita, tun farko saida Hajiya ta nuna mashi ga mata nan a familynsu waɗanda an san su an san asalin su amman ya bijire lokacin idon shi ya rufe mugun son Jameela yake kamar me. Aikuwa ƙarshe ba a kwashe ta lafiya ba bayan da hajiya ta nemo mashi mata a cikin family ɗinsu wadda bazawara ce haihuwarta ɗaya mijinta ya rasu, ko da mom ɗin su Deen ta ji aikuwa ta daka tsalle ta tuma ta ce wllh bai isa ba duk da ya faɗi mata hajiya ce ta sa shi, amman hakan bai sa ta saurare shi ba, ƙarshe ma sai cewa ta yi ai dama ƴan family ɗinsu sun tsane ta har da hajiyan shiyasa ta saka shi ya ƙara aure inda tana sonta baza ta sa ba Ƙarshe har Funtua ta je gidansu matar ta ja musu kunnen kada su sake su bari a yi auren in ba haka ba ta sha alwashin sai ta halaka ta in ya so itama ai mata hukunci, har gidan hajiya ta je itama ta gaggaya mata magana kan wai ta tsane ta shiyasa zata sa a yi mata kishiya, itama hajiyar sai da ta sha mata alwashin in dai aka sake aka yi auren to sai ta kashe yarinyar wllh. Lokacin jin abun da ta aikata dad ɗin ya ce ma hajiya sakinta zai yi, hajiyar ce ta hana ya yi hakan ta ce mashi ya haƙura da ƙara auren a lokacin ya bari sai ya fara gyara gidan shi tukunna. Ba don Allah Ya sa shi ɗin mai tsoron Allah bane yana tsoron aikata zina saboda sanin hukuncin ta da tuni ya afka ga aikata hakan, ba kamar yadda Allah Ya hore mashi yana da hali da matsayin da duk kalar macen da yake so za a kawo mashi har in da yake.



   

"Miyasa a duk lokacin da kika san ina tsananin buƙatar ki sannan zaki fara kawo wani uzuri mara dalili kina ja mani rai Jameela?" Rai a 6ace ya faɗi hakan tare da sakin jikinta, ita kanta ta san ran shi ya 6aci tun da har ya kira ta da ainihin sunanta.


  

Ashe ba daɗi? Kai ma ai ka iya ja ma mutun rai idan yana son abu a wurin ka ko?" Wani kallo mai cike da takaici yake mata, ita kuwa sai wani jujjuya ido take tana yamutsa baki, 


   "Wani abu kika nuna mani kina so na ja maki rai? Bana tunanin akwai abun da zaki buƙata a wurina ba tare da na yi maki ba..." Tarar numfashinsa ta yi, "Ai dama ban ce baka yi ba, amman wani lokacin sai ka ja ma mutum rai saboda yana nema a wurin ka, sai ran mutum ya gama 6aci.." Ta ƙarasa idon ta na kallon gefe ta ɗaure fuska, shiru ya yi yana ta kallonta ya ɗan ƙanƙance idanu, wannan halin nata na kawo tata buƙatar a lokacin da ya buƙaci hakkinsa ya tsane shi wllh.


 "Yanzu miye kike so?" Ya tambaya bayan ya sauke yar ajiyar zuciya,


   "Ka san mi na tambaye ka ai, maganar kuɗin da na yi maka zan tura ma Ammi." Wani kallon takaici yake wurga mata, wani lokacin har mamakin irin son kuɗinta yake, a koda yaushe cikin kawo masa buƙatun kuɗi take, duk da yana bata kuɗaɗe ba yan kaɗan ba, ban daAa kuma Deen da shima tana samun kuɗi a wurinsa bana wasa ba.


   

  Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "In don wannan ne ai kin san zan baki tun da duk kika kawo mani wata buƙata da ta shafe su ina yin bakin ƙoƙari na, na ce ki ɗan jira ni kaɗan, yanzu babu isassun kuɗi ne a wuri na, cikin satin nan na tura ma injiniya da suke mana aikin gidanmu na Funtua kuɗi, aikin gidan yana da cin kuɗi sosai saboda gidan da kika nuna kina so ne ake yi duk don in faranta maki." Yamutsa fuska ta yi, "Amman dai ai baka cewa kwata-kwata baka da kuɗi, ko rabi ne sai ka bani." Kallonta yake yayin da ransa ke suya, ta saba haka nan ta kawo mashi buƙatar danginta ta kuma sa rigima idan ya nuna baya da hali, ba zata bar hankalin shi ya kwanta ba har sai ya yi mata abun take so, Allah kaɗai ya san adadin buƙatun kuɗin da ya yi ma danginta tun daga kan iyayenta zuwa ƙannanta. Sanin idan fa bai yi mata yadda take so ba to shima ba zai samu yadda yake so ba ya sa shi ce mata su tafi part ɗinshi zai tura mata rabin wayan shi na can, tare suka sauka daga saman gadon suka tafi tana ta cika tana batsewa, ni kam dai mai rubutun na ce 'A Juri Zuwa Rafi...'. Allah Ya kyauta Ya raba mu da son zuciya.



LONDON


Belgravia,  (unguwar da aka fi sanin ta masu arziƙi a London...)



Gida ne bene hawa biyu na alfarma, yana da faɗi tare da ginin zamani mai ɗauke da gilasai. Ginin  gidan na da manyan tagogi da aka yi da gilasai masu nuni da tsari na zamani tamkar ginin kamfani. Kana shiga cikin gidan zaka tsinci kanka a cikin wani falo mai girma zubin na turawa cike da alfarma. Bangon gaba ɗaya fari ne mai sheƙi, an ƙawata bangon ta hanyar ɗora masa manyan zane-zanen fasaha na zamani. Ƙasan falon an rufe shi da Persian rug na Turai mai kauri da tsananin taushi a ƙafa wanda yake yin ɗan ƙyalli idan aka yi tafiya a kai. Kujerun cikin falon ɗuma-ɗuman leathers ne wato na fata kalar baƙi da ratsin golden mai haske, suna da tsananin taushi ko a ido. A saman falon akwai babbar fitila (chandelier) mai ƙyalli, girmanta tamkar zata rufto ma mutum, wadda aka yi da gilashin lu'ulu'u masu haske, tana kwaranya haske ta kuma bai wa falon kyan gani fiye da yadda ake tsammani, akwai kuma wasu ƙananun fitilun a can sama. A gefe ɗaya na falon an sa babbar talabijin mai siffar bango (wall screen) wadda a girma ta wuce inci ɗari, da sauran kayan sauti masu bada sautin gaske da ke sa mutum ya ji kamar yana a cikin cinema. Daga hannun dama kuwa akwai na'urar kula da gida (smart home system) da aka ɗaura a kan bango tana sarrafa fitilu, talabijin, sauti da ma kofar shigowa, duk ta hanyar danna madanni ko amfani da murya. Daga ƙasan tagogin falon akwai na'urar ɗumama iska da na'urar sanyaya iska, wanda suke aiki da kansu idan yanayi ya sauya. Duk in da ka kalla a cikin falon, zaka ga alamar zamani, daga na'urar ƙara haske (smart lighting) wacce take canza launi da dare, zuwa na'urar magana (voice assistant) da take iya amsa tambayoyi cikin harshen turanci. Tabbas gidan ya amsa sunan aljannar duniya, ko da gidan yake a Turai kana gani ka san bana ƙaramin mai arziƙi bane. Akwai bangaren cin abinci wato dining area dake cike da alfarma da fasaha, haka akwai bangaren karatu wato study corner mai ɗan  girma, akwai babbar shelf mai ɗauke da littattafai, nan ma bangaren an ƙawata shi da abubuwan fasaha irin su smart speaker dake amsa tambayoyi tana kula da smart home devices, kamar kunna fitilu ko sauran na'urorin lantarki, sauraran kiɗa, podcasts ko audiobooks, saita tunatarwa kamar alarm, kira da kuma aika saƙonnin murya. Zaune a saman kujerar fata mai mazaunin mutum biyu dake cikin ɗakin karatun, Maleek ne jikinsa sanye da farar jallabiya ƙal, idanunsa na a cikin farin gilashin screen, kana ganinsa ka ga mutum mai lafiyayyen jiki wanda ba zaka iya tantance ainihin shekarunsa ba, ƴar hurhurar dake a gashin gemunsa da kuma saman kansa ke ƙara bayyana manyantakarsa, fuskarsa na da cika mai nuni da kwanciyar hankali da arziki da kuma tsananin ƙwarjini, a saman teburin da ke gaban sa manyan litattafai ne tare da laptop sai wata fitilar karatu mai kyau, daga gefe wireless charging pad ne da ake ɗaura waya a sama ta yi caji, ya dukufa yana duba wani babban littafin fasaha, lokaci bayan lokaci yake ɗan dakatawa tare da kai hannunsa ya ɗan tatta6a kwamfuta ɗin kafin ya ɗaura da duba littafin. 


Shigowa ta yi cikin babban falon tana sanye da riga da wando na bacci masu santsi kalar ruwan madara sai sakin kamshi mai ratsa zuciya take, ta rufe kanta da madaidaicin farin gyale da ya ɗan zame gaban kanta mai ɗauke da baƙar suma mai santsi ya bayyana, kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar da ita ɗin kyakkyawa ce ta gaske, tun daga fuskarta zuwa dirin jikinta masu ɗaukar hankali ne, bin cikin falon ta yi da kallo kamar tana neman wani abu, hanyar da zata kai ta study corner ta nufa tana yin tafiya dake bayyana nutsuwarta, tana zuwa bakin ɗakin idanunta suka yi tozali da wanda take nema, wani ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta mai ɗauke da jan labba tamkar ta shafa jan baki sai dai kuma haka halittar su take, nufar shi ta yi tana yin tafiya a hankali kamar sanɗa yadda ba zata yi sautin da zai gane ta shigo ba, ta bayan shi ta zagaya tana zuwa ta kai hannuwanta ta saƙalo su ta kafaɗarsa tare da ɗaura kanta a gefen wuyansa, a nutse ya ɗago da fuskarsa mai cike da haiba yana murmushi ya kallo ta ta gefe, cikin sigar jan hankali ta kashe mashi ido tare da furta, "Sanyin idaniyar Sapnah kana nan ke nan, ka bar ni ni kaɗai." Ɗan lumshe ido ya yi yayin da ɗumin bakinta mai tattare da daddaɗan ƙamshin mouth spray ɗin da ta fesa ya bugi fuskarsa, a hankali ya furta, "Baki yi bacci ba?" ƙoƙarin zagayowa ta yi ta dawo ta gabansa, a saman cinyoyinsa ya yi mata masauki suna kallon juna cikin ido fuskokinsu tamkar zasu haɗe ta bashi amsa da, "Ta ya zan iya yin bacci mai saka ni in yi baccin baya kusa da ni." Yar dariya ya yi, slowly ya matso da bakinsa ya yi kissing reddish lips ɗinta ta lumshe ido, "I'm sorry, ina wani bincike ne mai muhimmanci da muke buƙatar sa da gaggawa." Ta ɗan kashe masa ido tare da furta, "Don't worry honey, kana da amincewar Sapnah a koda yaushe." Ya lumshe mata ido can ƙasan maƙoshi ya furta, "Thank you mah luv." Ta kai bakinta ta sumbaci kuncinsa kafin ta sauka daga jikinsa ta zauna gefensa ta ce ya ci gaba da aikin.


A nutse take taka matattakalar benen yayin da take saukowa daga sama ƙafafunta na sanye da slippers masu taushi irin wanda ake yawo a cikin gida, cikin babban falon ta shigo tana sanye da nightgown iya gwuiwa da ta bayyana ɗan dirinta na matashiyar budurwa, kanta ta saka hula yalwatacciyar sumarta ta fito gefe da gefen kanta ta ƙulle ta da ribbom ta baya, kunnawanta na sanye da ƴar barimar diamond. A yanayin halitta ba za a kira ta fara ba, kana kallon ta ka san baƙa ce, sai dai daga yanayin fatarta yadda take sakin sheƙi ta fallasa ba ƙaramin hutu da jin daɗi take a ciki ba, sam ba wata kyakkyawar a zo a gani bace amman kuma ba za a kira ta da mummuna ba, tana da ƴar doguwar fuska mai ɗauke da ƙananun idanu da madaidaicin hanci da bashi da tsawo sosai, tana da ɗan babban baki mai ɗauke da manyan labba, yadda yanayin shape ɗin labbanta suka fita sun yi kalan ƴan gayu. Bin cikin falon ta yi da kallo sai kuma ta ci gaba da yin tafiya, bangaren mom ɗinta ta nufa, ɗan madaidaicin falo ta shigo da shima ya tsaru da kayan zamani, ganin bata a ciki ta wuce bedroom ta buɗe kofar ta shiga, nan ma wata aljannar duniyar ce guda, duk da ɗakin baya da hayaniya amman an zuba tsaddaddun kayan alatu a ciki, ganin nan ma mom ɗin bata nan ta nufi bakin kofar toilet ta ƙwanƙwasa tare da furta, "Mum, are you in there?" Jin Shiru ta ƙara kiran sunan mum ɗin, nan ma shiru hakan ya sa ta gane bata ciki ta juya ta nufi hanyar fita, babban falon ta dawo ta wuce kaitsaye zuwa study corner don ta san bata wuce tana can, tana shiga ta hango su zaune ta tsaya daga bakin ƙofa, cikin sigar shagwa6a ta furta, "Mum, dad..." A tare suka juya suka kalli direction ɗin da take, lokaci guda murmushi ya bayyana akan fuskokinsu ganin ɗiyarsu ɗaya tal da Allah Ya basu wadda ta kasance mafi soyuwa kuma sanyin idaniyarsu, hannu Maleek ya miƙa mata ta nufo su, a gefen shi ta zauna bayan ta kama hannun nashi, yana kallon ta ya ce, "Baby, haven't u slept yet?" Ta ɗan yamutsa fuska ta furta baccin ya ƙi zuwa, cike da kulawa idanunsa akan fuskarta ya ce ko wani abu na damunta? A hankali ta ɗan girgiza masa kai tare da kwantar da kanta a gefen kafaɗarsa, Sapna da ta maido duk attention ɗinta kan ɗiyar tata, tana ɗan murmushi ta ce, "Ko dai duk missing ɗin Deen ne?" Ɗan murmushi ne ya bayyana kan fuskar Basma ta maida idanunta ƙasa ba tare da ta ce komai ba, "Haka ne baby?" Maleek ya tambaya yana ɗan leƙen fuskarta, ɗago idonta ta yi da ɗan alamun damuwa ta ce har yanzu basu yi magana ba tana ta kira da daren nan but no response, kallon juna suka yi shi da Sapna, ba sai an faɗa masu ba sun san yadda take tsananin son Deen, hannu ya kai ya dafa kanta yana  murmushi ya ce kada ta damu ya san ya yi busy ne sosai shi yasa bai samu damar su yi magana ba, musamman da ya ɗan daɗe bai je Nijeriya ba gashi a daren nan aka yi masa welcome dinner, 


"Yakamata ma ki saba da hakan, tun da ko yana a nan ba wani cika samun lokacin kan sa yake ba." Nodding kai Basma ta yi jin maganar mum ɗinta, har da hakan nema ya sa take yawan yi masa uzuri tana ɗaukar rashin bata kulawan da yake har da lokaci da bai da shi sosai. "Na tura maki saƙo kin gani." Maleek ya tambayi Basma, ta ɗago tare da ɗaga mashi kai ta ce masa thank you, Sapnah ta tambaye shi saƙon miye, ya ce ba wani abu bane ta ce tana buƙatan kuɗi ne shine ya tura mata, wani kallo ta yi ma Basma da itama take kallon nata cike da kama kai, mamakin mi zata yi da kuɗi ne Sapna ta shiga yi don ba a fi kwana biyar ba da ta buƙaci kuɗi a wurinta kuma ta bata masu yawa, bayan haka duk ƙarshen wata kowa a cikin su ke tura mata kuɗi don yin buƙatun kanta. Tabbas ta san kashe kuɗin Basma yana yin yawa, amma sanin ɗiyar tata na da son yin gayu da tsadaddun kaya ga kuma kyauta da take da ita musamman ga ƙawayenta yasa bata damuwa ta san duk anan kuɗin ke tafiya, wannan tunanin ya sa ta share bata ce komai ba, itama ta yi ma Maleek godiya da fatan ninkuwar arziƙinsa, yana murmushi ya ce ai su nauyinsa ne komai ya yi masu hakkinsa ne don haka no need sai sun rinƙa masa godiya, Sapna ta ce duk da hakan ai an ce yaba kyauta tukuici to godiyan ne yake serving as tukuicin, murmushinsa na dattako ya yi kafin ya ce su je su sha coffee, Sapna ta ce "Amman ba ka ce aikin da kake mai muhimmanci bane kuma na gaggawa, ka ci gaba da aikin ka, bari in raka baby part ɗinta." ƙoƙarin miƙewa ya fara yi yana riƙe da hannun Basma ya bata amsa da, "All work and no play...." Basma ta ƙarasa masa karin maganar da faɗin, "....makes Jack a dull boy." Gaba ɗaya suka yi ƴar dariya, itama ta kama ɗayan hannun Basma ta yadda sun saka ta a tsakiyar su suka nufi ƙofar fita gwanin burgewa....





*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post