GINSHIƘIN DUTSE...
_True life story._
*BOOK 1*
UMMU AFFAN
*Page 9-10*
Ɗaya daga cikin yaran ta ce, "Kema tsinto duwatsunki 'yar goma-goma ce."
Har ta miƙe ta tuno abin da ta gudarwa sai ta koma ta zauna.
"Habi naga naki da yawa, ɗan ara mini kafin na samo nawa."
Wacce aka kira da Habi ce ta 'yirga duwatsu goma ta miƙawa Surayyah. Amsa tayi aka fara bugawa da ita, tun biyu da rabi ita ce har huɗu suna yi, daga ƙarshe ba a rabu ta daɗi ba domin bata biya Habi duwatsunta goma da ta ara ba.
"Daga yau mun daina wasa da ke tunda baki da mutumci." Cewar Habi ranta a ɓace.
"Rashin mutumci biki ne kowa ya yi sai ka rama masa, ni har za a gayawa rashin mutumci? To nayi ɗin ko zaki dake ni ne?"
Ƙawar Habi mai suna Sa'adatu ta miƙe tare da riƙe ƙugu ta ce,
"Mune muka fiki da muka yi wasa da ke amma anyi na farko na ƙarshe, taya zaki ari 'ya'yanta kuma kiƙi biya saboda ke ga isassa."
Surayyah ta miƙe a harzuƙe tare da cin kwalar Sa'adatu ta ce,
"Ko zaki dake ni ne? Na isa ne wata ma tayi ta ga idan za ta ci riba."
Habi ta fara ɓanɓare hannuwan Surayyah jikin Sa'adatu tana cewa,
"A'a mu ba ma faɗa da mara jin maganar iyayenta, ke da har ƙofar gida Babanki ke biyoki yana bugu ai ƙarshen rashin mutumci."
Ai Surayyah ba ta san lokacin da tayo kukan kura ta shaƙi wuyan Habi ba.
Cikin hargagi take cewa, "Eh ɗin ba na jin maganar tasu, wani idan ya yi rawa kuɗi ake liƙi, wani kuwa ɗan karen duka zai sha wallahi." Nan dambe ya rikice, ganin ana ƙwarar Habi sai Sa'adatu ta shigar mata. Amma duk da haka Surayyah bugunsu take ko ta ina don Allah ya bata ƙarfi ga yakushi.
Ihunsu da Matar malam Sa'idu kuma mamar Habi da take juyowa ne ya sakata fitowa zauren.
Salati ta ɗauka tana ƙoƙarin raba faɗan.
"Ni ki rabu da ni, sai na fasa bakin rashin kunyar tasu na ga ƙarshen magana."
Surayyah ta faɗa tana fincike ruƙon da Innarsu Habi ta mata.
"Yau naga ikon Allah! Kefa Surayyah daman baki da mutumci, wai uban me ya haɗaku?"
Habi tana kuka ta korawa Innarta komi, Sa'adatu ta ɗaura da cewa,
"Tabbas haka ne, maimakon ta biya kuma ta fara aika mana da na maguzawa, har da duka saboda gata isassa."
Gyaɗa kai Innar tayi a ranta tana ayyana 'In dai Surayyah ce zata aika, a unguwar uban waye bai san halin yarinyar ba.' A fili kuwa cewa tayi.
"Ke Surayyah ashe ke ce baki da gaskiya, ina ki ka taɓa ganin anyi haka? Maza ki sake su ki bar gidan nan tunda baki da mutumci."
Surayyah na tura baki ta ce, "Ai dole ki faɗi haka tunda iya ta bakinsu ki ka ji, kuma sharia ba ta ce haka ba, yadda suka faɗa miki nima ya kamata ai kiji ta bakina amma saboda tsabar son kai ni baki tambaye ni ba, to wallahi idan na riƙe su sai sun gane kuɗarsu wawaye kawai. Gida kuwa ai daman dole na fitar muku tunda ba ni da gado a cikinsa."
Riƙe baki Innarsu Habi tayi ta ce, ''Oh rashin kunyar taki yau har a kaina, kin daɗe kinawa wasu yau kuma kaina abin yazo? To bazan ce miki komi ba domin nima ina da 'ya'ya Allah ya shiryaki."
Duƙawa tayi ta kwashi duwatsun da suka yi 'yar carafken duk da ba nata ba ne, Sa'adatu ta ce, "Amma fa 'ya'yan da take kwasa duka namu ne?"
"Don Allah ku bar ta ta kwasa kwa tsuntu wasu, zata haɗu da daidai ita."
Surayyah kuwa banza tayi da su amma tana ta zagin Innar Habin a gungunai haka ta kwashe 'ya'yan tsaf sannan ta nufi hanyar fita duk suka bita da kallon, sai dai bata fice daga zauren ba suka ji ruwan duwatsuna a kansu, ba shiri dukansu suka dare suka yi ciki Sa'adatu da Habi na zaginta.
Ita kan 'yar dariya tayi ta ce, "Kaɗan ma kuka gani ai ni wallahi duk wanda yaci tuwo da ni miya kawai zai sha. Kuma na riga na zamarwa kowa Ginshiƙin dutse, duk wanda ya ce zai yi karo da ni shi ne da faɗuwa wallahi" Da haka ta tafi da sauran duwatsun tana tafiya tana zubdawa, tare da rera waƙarta har ta isa gida, lokacin da ta ƙaraso cikin gidan har biyar na yamma tayi.
Babu kowa tsakar gidan, hakan yasa kai tsaye ɗakinsu ta nufa, suma basa ciki nasan suna islamiyya ne don lokacin tashi bai yi ba. Kan katifarsu ta faɗa tana sakin numfashin gajiya. Ɗago kan da zata yi taga Innana tsaye kanta, gyara kwanciyarta tayi ba tare da ta ce komi ba. Cike da takaici Innana ta ce,
"Surayyah yanzu wuni guda ina ki ka ke? A matsayinki na 'ya mace ki fita gida tun hantsi sai yanzu zaki dawo?"
Tura baki tayi cike da rashin kunya, wanda wannan ma ya riga da ya zame mata jiki ta ce,
"Innana gurin fa Hindu naje na tayata tallah."
"Tallah!"
Innana ta furta da ƙarfi kafin ta ɗaura da cewa.
"Yanzu haka ki ke ganin ya fiye miki Surayyah? Duka 'yan'uwanki babu mai mummunan hali irin naki, Allah ya gani ban yi wa iyayena haka ba shima mahaifinku mutum ƙyirki ne mai yasa ki ka fita zakka Surayyah?"
"Don Allah Innana ki bari wallahi duk na gaji ne, surutunki na hawa kaina."
Kasa magana tayi sai buɗe baki idanuwanta kuwa suka cika da hawaye, da sauri tayi ƙoƙarin mayar da su, amma sai da suka zubo. Hanyar fita tayi da sauri jikinta na rawa, Surayyah taga komi taɓe baki tayi tare da gyara kwanciyarta nan take kuwa bacci ya yi awan gaba da ita.
Bayan dawowarsu Mardiyyah suka iske tana bacci ba wacce tabi ta kanta suka cire uniform kowa ta fara harkar gabanta.
A daren ranar Appa yana cin tuwo ya dubi Innana da tayi nisa a tunaninta, bayan ya kai loma bakinsa ya gyara murya tare da zungurinta, da sauri ta dawo hayyacinta ta saka hannu kwanan tuwan dake gabanta.
Sai da ya kammala cin tuwonsa ya wanke hannunsa yasha ruwa sannan ya dubeta a tsanake ya ce,
"Kuluwa kamar akwai abin da ke damun ranki amma kina ɓoyewa."
Numfashi Innana ta sauke da cewa, "Bari kawai abin na Surayyah ya fara damuna Malam, anya ba zamu kaita gurin malaman ruƙiyyah ba? Domin na fara tunanin ko dai yarinyar nan tana da jinnu ne."
Murmushi ya yi wanda kana kallo kasan na takaici ne kafin ya ce,
"Kuluwa kenan! Ai idan zaki cigaba da biyewa Surayyah to kaɗan ki ka fara gani daga halayenta. Sai nayi magana kiga kamar bana sonta ne, to ai yanzu kema kin fara gani ai."
Yana niyyar tashi tayi saurin tarar numfashinsa.
"Malam bai kamata ka ce haka ba, nima kasan ba wai ina goyan bayan rashin kunyarta ba ne."
"Ke ɗin? Wanne dare ne jemage kuma bai gani ba, ni dai abinda zan ce shine ki cigaba da bin ta da addu'a nima abinda nake mata kenan, domin bazan wahalar da kaina gurin kaina gurin wasu malamai ba, don tsabar iskanci ne da rashin kunya nata wasu ma 'yan ƙarya ne idan anje haka zasu ce tana da su kin ga rashin mutumci kuwa sai ta ƙara ɗaura ɗammara idan taji an ɗaure mata ƙugu, yanzu ma ya aka ƙare balle taji ance aljanu ne ke sakata, haka kawai a ɗaurawa bayin Allah."
Innana kasa maganantuwa tayi har Appa ya shige ciki, tuwon da take ci ma sai taji duk ya fita a ranta. Allah ya gani tana fara tunanin Surayyah Aljanu ne ke sakata duk abinda take, domin yawanta na yau ya yi matuƙar tsoratar da ita, tsoranta kar taje a lalata mata rayuwa tana 'ya mace. Wannan ne idan ta tuna yake ƙara jagula tunaninta. Haka ta tsame hannu daga tuwan taje ta ajiye tare da wanko hannunta.
Ɗakin yaranta maza ta fara leƙawa, Auwalu ne kawai a ciki, Sani yana ƙofar gida da abokinsa suna hira yayin da Salisu ya tafi kallon ball. Dawowa ciki tayi tare da shiga ɗakin 'yan matan, sai lokacin Surayyah ta tashi har anyi isha'i, kallonta tayi tana mutsutstsuke idanu ta ce, "Ba dai yanzu ki ka tashi ba?"
Mufidah tayi charaf ta ce, "Sai yanzu ta tashi Innana."
Harararta Surayyah tayi kamar zata kai mata duka. Innana ta ce,
"Shine kuma ba wacce ta tada ta cikinku har ke Kubrah bayan kun san baccin yamma ba shi da ƙyau?" Kubrah zata yi magana Mardiyyah ta rigata.
"Haba Innana, sai ka ce baki san halin Surayyah ba, wata cikinmu ta tasheta cibi ya zama ƙari? Da dai ta san mutumci ne."
"Eh ban sani ba, daman kuma ban ce wata shegiya ta tashe ni ba."
Cewar Surayyah kamar tana jiran Mardiyyah tayi magana, ita kam gyaɗa kai tayi da cewa.
"To kinji ko? Wa ya aike ni balle ya ga na daɗe, ai bikin magaji bai hana na magajiya."
Nan fa Surayyah ta miƙe tare da nuna Mardiyyah da yatsa.
"Duk gidan nan na san daman ke ce baki ƙaunata kuma har abada bazan manta da hakan ba, wallahi Mardiyyah da ni kike faɗan sai na nuna miki kin taɓo wutar ƙaiƙayi wallahi ni gobarar mata ce za kuma ki faɗa ne."
"Innalillahi wa'inna ilahir raju'un!" Cewar Innana tare da riƙe kanta.
Kubrah ta ce, "Kin san komi Innana da kin sani ma kwanciyarki kika yi kika huta."
Mardiyyah dai kwanukan da suka gama cin tuwo ta ɗauka tare da fita bata kuma tankawa ba. Innana ta ce, "Surayyah ki tashi akwai ruwan zafi a tukunyar tuwo kiyi wanka kiyi sallah kafin kici abinci." Tana tura baki ta ce, "To." Innana bata kuma kulata ba tayi ficewarta. Komawa tayi ta zauna tana cewa, "Ni ba wankan da zanyi sai gobe tuwon ma ba ci zan yi ba balle a hana ni sai nayi wankan."
Kubrah dai bata tanka ta ba Mufidah ma tsaki taja ta fita wanke hannayenta...
"Kanku ake ji, ni dai riga na fito ta tsatsunku ba yadda kuka iya da ni, murucin kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya."
Surayyah ta kuma faɗa zuciyarta fes, Kubrah kam da suke ɗakin tare ɗago kai ba tayi ba balle ci kanki.
Bayan duk sun shugo kowa haramar kwanciya ya yi, domin daman sai sunyi sallahr isha'i suke cin abincin dare. Ita kuwa hamsahaƙiyar miƙewa tayi tare da chanza kayan jikinta don ita kanta taji sun fara damunta sun kusa sati jikinta. Doguwar rigar atamfa ta ciro cikin jakar bakkonta da duka kayan ba nunki wankin ma Innana ce da ta gaji ta tarin kayan wankin da Mardiyyah ke ta ƙorafin sun ishesu da tsami ta kwashe ta wanke mata, to ko da ta dawo ta saka ta kwashe kayan haka tazo ta cusa su cikin jakar ba nunkewa. Tana sakawa ta ɗauki hijabi a ciki ta saka, ko kallonsu ba ta kuma yi ba ta fice a ɗakin domin yadda aka haɗa kuɗin kaset na kallo gidan Maman Ummi ba zata bari yau a fara bata kusa ba musamman da ba su daɗe da kawo nepa ba. Don tasan ana kawowa ake fara taruwa kallo kuma kunnawa take yi ko dukansu ba su hallara ba. Tayi sa'ar ganin Sani ya koma cikin ɗakinsu don tana jiyo hirarsu shi da Yaya Auwalu, hamdala tayi tana ƙara waiwaye tare da addu'ar Allah yasa kar taga wannan ɗan nacin Salis, don ta lura shi tsanar nata da ya yi ta musammance, domin gani take duka gidan sun tsaneta ba sa ƙaunarta shi ya sa suke hantararta. Tana waƙenta ta doshi gidansu Hindu aka sanar da ita ba ta shugo gida ba daga wajen tallah, domin bayan shinkafa da ake dafawa Hindu da rana ta sayarwa da dare kuma tuwo ake mata shima tana fita da shi tallahr.
Kai tsaye Tsohuwar Kasuwa Surayyah ta nufa ta iske Hindu ta sayar da tuwon kawai ta tsaya ne suna ta zance da maza. Saurayinta Sabitu ne yajata gefe inda ba haske sosai sai taɓata yake yana matsa 'yan ƙananun nonowanta ita kam sai dariya take, zuwan Surayyah ne ya tsayar da Sabitu ga abinda yake cike da fara'a ya ce,
"Ƙawarmu-ƙawarmu."
Tura baki tayi da cewa, "Ai ni Sabitu faɗa muke tunda har ranar ka mini alƙawari ka kasa cikawa."
Yana dariya ya ce, "Yi haƙuri ƙawarmu ai ke ce da laifi na miki kwatancen inda zaki amsa baki zo ba."
Ta ce, "Haka ne fa, mantawa nayi Sabitu na Hindu amma gobe ya kamata Hindu ta rako ni sai na amsa."
"A'a fa ke kaɗai zaki zo domin Hindu ai lokacin tana wajen tallah."
"To shikenan goben zanzo." Washe haƙora ya fara yana lasar baki da laɓɓansa idanuwansa ƙur akan Surayyah...