GINSHIƘIN DUTSE...
_True life store._
*BOOK 1*
UMMU AFFAN
*Page 11-12*
Hindu ta ɓata rai da cewa, "Gaskiya Sabitu tare zamu zo, idan na sayar zuwa yamma sai mu zo.."
"Yawwa nima haka nayi tunani Hindu kamar hakan zai fi."
Surayyah tayi saurin tarar numfashin Hindu, gyaɗa kai Sabitu ya yi ba tare da ransa yaso ba ya ce,
"Haka ne kuma, to Allah ya kai mu goben."
Sallama suka yi ya ɗauki ɗari biyar kuɗin tuwon da ya sayawa almajirai don kar Hindu ta koma da kwantai, godiya tayi mishi, Surayyah ta tayata ɗaukar kayan suka nufi hanyar gida.
Suna zuwa ƙofar gidansu Hindu ta ciro wata baƙar leda ta ce, "Riƙe mini wannan kar ki fito da shi sai idan mun fito."
Da "To." Surayyah ta amsa suka shiga cikin gidan.
Mamar Hindu har da buɗa ganin cikinikin tuwo kusan dubu biyu ta ce, "Allah ya miki albarka Hindatuwa mai goshin arziƙi, zo kici abinci."
"A'a Inna na ƙoshi, bari muje kallo gidan Maman Ummi."
"To mai goshin arziƙi a dawo lafiya."
Su Hindu suka fice ya yin da Innarsu ta buɗe kwallarta ta ajiya ta ajiye kuɗin ranta fes tana ƙara alfahari da 'yar tata, a cewarta duk yaran gidan Hindu tafi kowa goshi da kan kasuwa kuma bata ɓatar da kuɗi.
Suna fitowa kusa da gidan kallon suka zauna saman wani dakali Hindu ta buɗe ledar sai ga gasasshiyar kaza rabi sai robar juice na Fanta.
Surayyah ta zaro ido da cewa,
"Kai Hindu wa ya baki kaza har da lemun roba?"
Dariya Hindu ta saka da cewa, "Ke banza, wallahi wani sabon saurayi nayi mai suna Lawan har mota fa gare shi, yana sayen abinci gurina kuma idan kuɗi ma sun ƙaru bar mini yake jiya ma kifi ya kawo mini yau kuma kin gani dai."
Da sauri Surayyah ta yagi tsoka ta kai bakinta, tana taunawa ta ce,
"Amma na tayaki murna Hindu gaskiya wannan yafi Sabitu sonki ma."
"Ke dai bari, ai ni yanzu nafi son Lawan kawai dai ina kula Sabitu ne saboda shi ne saurayina na farko shima kin ga ba laifi yana mini juye idan tuwo bai ƙare ba shi ya sa ma dai muke tare."
Nan suka cinye kaza rabi suka kora da lemun fanta. Surayyah na cewa,
"Wallahi ashe gara da banci ƙadararren tuwancen ba na kullum ba fashi ashe rabon zan ci kaza."
Dariya suka saka Hindu ta ce "Ai ni na kwana biyu bana cin tuwan gida, a waje nake ciye-ciyena wajen tallah har in cika cikina." Tafawa sukayi tare da ƙarasawa gidan kallo suna cigaba da hirarsu.
Wajen goma da rabi yau nepa suka ɗauke ga film ya kusan ƙarewa kamar zasuyi kuka suka fito gidan Maman Ummi ko wacce ta nufi hanyar gida. Yau ba a rufe gidan ba da alamar Yaya Salisu bai shugo ba don mafi akasari shi ne mai rufe gida don mayen kwallo ne na game a tv irin wanda ake yi da romote haka yana zuwa kwallon ma. Shurun da taji a ɗakin zaure yasa ta ce ƙilan suma su Yaya Auwalu sun yi bacci.
Buta ta ɗauka tayo fitsari sannan ta shige ɗaki don ko ina shuru da alamar duk sun kwanta bacci.
Tayi mamakin ganin Mardiyyah idonta biyu tana sallar nafila akan dadduma, jan tsaki tayi tare da ajiye hijabinta da tun a tsakar gida ta cire, kwanciyarta tayi amma sam bacci ya kasa ɗaukarta sai tunanin yadda za a ƙare take a film ɗin yau don sosai film ɗin ya yi ƙyau.
Zuwa can kuma ta gangaro kan saurayinta Malaminta Nura tana son shi sosai, amma yau ɗaya taji ya bata haushi tunowa da tayi da yadda saurayin ƙawarta Hindu Sabitu ke mata hidima ga kuma sabon da tayi Lawan wanda ta bata labari yau.
'Me yasa ita Malam Nura bai mata kyautar kuɗi ko abin ƙwalama?'
Tambayar da ƙwaƙwalwarta tayiwa zuciyarta kenan, nan take ta tashi zaune daga kwancen da take. A fili ta furta.
"Nafi Hindu ƙyau fa, me yasa samarinta ke bata kuɗi haka?"
Mardiyyah wacce ta kammala addu'o'inta ta ce,
"Yanzu kamar Hindu har tana da wasu samari? Ita ce ke buɗe miki ido ko Surayyah? Ace tun ɗazu ki fita sai yanzu kika shugo gida a matsayinki na 'ya mace?"
"To fa! Sa'idinawa, wai shin Mardiyyah ba na ce miki ki fita sabgata ba ne? Nifa yadda ki ka tsane ni nima haka na tsane ki, don Allah ki rabu da rayuwata."
"To Allah ya ƙyauta, idan ki ka biyewa samarin zamani wallahi su lalata ki a banza, daman Hindu kowa ya san ballagaza ce ko wanne banza kulata yake a layin nan kamar wata tunkiya."
"Mtsuww!" Surayyah taja tsaki tare da ce.
" 'Yar baƙinciki, don kin rasa mashinshini har zaki yiwa wasu sharri. To a kanki baƙin jini zai ƙare." Dariya Mardiyyah tayi har da tafa hannu ta ce,
"Allah na tuba duka nawa nake da za ace na rasa mashinshini? Ai da kina ga a gidan nan ko Kubrah da take samana bata zance balle kuma ni ƙasanta. Ke dai da ki ka ɗaurawa kan ki Allah ya ƙyauta miki."
Tana faɗa ta nunke daddumarta tare da kwanciya, Surayyah ta dunga zaginta da mata gorin baƙin ciki take suna da samari ita kuma ko kashi bai kulata..
Washe gari da safe suna kari koko da ƙuli-ƙuli, dukansu sunyi shirin boko amma ban da 'yar gogar daman jarabawarta ta shiga Jss1 bata fito ba. Appa ya dubeta ya ce,
"Surayyatu ke da Mardiyyaah malaminku ya kira ni a waya ya ce kuje ku amso jarabawarku." Gabanta ya faɗi sosai domin ta tsani ace wata makarantar zata shiga yanzu, ta ce,
"Appa naci kuwa?"
"Ki bari idan kin amso sai ki duba."
Ranta ɓace ta miƙe da kofin kokonta ta shiga ɗaki, duka suka bita da kallo. Mardiyyah kuwa sai murna take jarabawarsu ta fito domin ta ƙosa daman ta fara zuwa secondary ɗinta.
Surayyah kuwa ba ita ta fito ba sai wajen tara da rabi na safe zuwa lokacin duk yaran gidan sun watse makaranta, hatta Sani dake Jami'a ya tafi, Yaya Salis ma ya wuce kasuwarsu tunda a shekarar ya kammala secondary yana neman Admishion ne, Auwalu ma da yafi ƙarfi a kasuwanci ya kama gabansa. Shi kam Rabi'u daman ba a lissafinsa yana makarantar kwana yanzu yake SS2 acan, bata ga Mardiyyah ba hakan na nuna mata ta tafi amso tata jarabawar, ɗakin Innana ta leƙa ta iske ta tana cin ɗumamen tuwo Appa da alama ya fita tunda yanzu baya zuwa aiki sai gona, ya yi ritaya amma yana amsar fanshonsa sai ya mayar da hankalinsa katsokan ga noma daman kuma tun baya shiɗin babban manomi ne.
"Surayyah sai yanzu ki ka fito? Ai inajin Mardiyyah ta kusa dawowa ita."
Tura baki tayi da cewa,
"Wallahi na tsani jarabawar nan Innana, wai karatun nan dole ne?"
"Ba dole ba ne, amma yana da matuƙar muhimmanci, baki ga yaran da ke zuwa makaranta da waɗanda basa zuwa akwai banbanci ba?"
Ƙarasawa Surayyah tayi ciki tare da samun guri kusa da Innana ta zauna ta ce,
"Ni wallahi Innana da zaki dinga dafa mini abinci ina miki tallah da yafi."
Zaro ido Innana tayi ta ce, "Rufa mini asiri Surayyah, abinci, tallah kuma? A'a ba da ni ba gaɗa a hurumi. Kin san Appanku bai son tallah karatu yake so kuyi kuma bakin gwargwado bai rage mu da komi ba a gidan nan. Ƴan kayan miyan da nake sayarwa su kuka, kuɓewa, barkwono, daddawa da sauransu ma sun wadata. Babu ruwana ni kaina ba zan so ki zamo 'yar talla ba."
Ran Surayyah ya ɓaci sosai da jin furucin Innana, miƙewa tayi tana zumɓura baki ta bar ɗakin.
"Ba zaki ci ɗumamen ba?"
Innana ta tambayeta da ƙarfi, tana ji tayi mata banza ta ɗauki hijabinta tayi waje, ko da ta isa makaranta har class mate ɗinta sun gama amsar jarabawarsu, sai da Hedimaster ɗin ya dinga mata faɗa sannan ya bata ya ɗaura da cewa,
"Darajar mahaifinki ki ka ci har kika sami wannan, wallahi ba domin shi ba sai kin ƙara maimaita aji, daƙiƙiyar banza kawai."
Tunda ta fito take zagin hidimaster ɗin, har ta iso gida bata daina ba.
Inda ta iske Mardiyyah nata murna taci makarantar kwana ta Kabomo Bakori Local goverment. Innana da Appa da ya dawo suna tayata murna, sosai Surayyah taji baƙinciki a zuciyarta na samun makarantar kwana da Mardiyyah tayi, balle da taji Appa na cewa ita kuma ta sami Kwaminiti ne makarantar 'yan mata ta jeka ka dawo dake cikin garin na Katsina.
Su Kubrah na dawowa Mardiyyah ta tare su da murnarta tana sanar da su ta samu Kabomo. Ita da Kubrah suka rungume juna cike farinciki.
"Gaskiya Sister na tayaki murna kin sami abinda ki ke so." Cewar Kubrah cikin murna.
"Bari kawai, Allah dai ya taimake mu ya ba mu sa'a a karatunmu."
"Amin dai 'yar'uwa."
Surayyah taja tsaki tare da komawa cikin ɗaki, suka bita da kallo tare da taɓe baki irin ko a jikinsu ɗinnan.
Ita daman Kubrah Day take zuwa, makarantar mata da maza ne jeka ka dawo ta 'yan mata, sai dai ɓangaren maza daban na mata daban. Tayi farinciki lokacin da taji cewa Surayyah Kwaminity taci ba Day ba ko ba komi idan taje Day idanuwanta zai buɗe ne saboda maza duk da dai kowa da ajinsa kuma ba ɓangare ɗaya ba ne, amma ana haɗuwa sosai har soyayya sai kaji an kulla tsakanin ɗalibai musamman idan jss3 ka ke ko ss3, shi ya sa tayi farinciki da makarantar mata zallah Surayyah taci.
Ita kuwa safa da marwa kawai take a ɗakinsu tana jan tsaki, sosai take jin takaici na makarantar kwanan da Mardiyyah taci, duk da bata sha'awar makarantar kwana amma sam bata so ace Mardiyyah taci ba. Kuma yadda taga Appa da Innana na murna ta san sun bada goyan baya kenan akan zuwanta. Ta san ko ta zuga Innana aikin banza zata yi tunda har Appa yana so, shikam magana ɗaya yake baya sauya wata.
Gauda da miyar taushe Innana yau tayi da rana, su Kubrah naci cikin nishaɗi amma Surayyah ta buga uban tagumi a tsakar gidan. 'Su kenan cin dawa masara ba sauyi, 'yar shinkafar nan ko taliya Appa baya saya sai abinda ya noma ake ci a gidan.' Abin da take faɗa kenan a zuciyarta ba don ranta ya so ba ta jawo robar da Autah ta ajiye mata nata wanda Innana ta saka mata, tun ɗazu yake ajiye sai yanzu ta jawo har ya fara hucewa.
Da ƙyar ta iyacin guda biyu, domin tunowa da tayi anjima nan zasu je gurin Sabitu saurayin Hindu kuma alƙawarin gurasa ya mata wacce ita ce sana'arsa. Wani murmushi ne ya subuce mata, da sauri ta miƙe tare da leƙa ɗakin Innana agwogwon bangonta ta kalla uku har ta kusa, da murna ta ƙarasa rariyar tsakar gidan ta wanke hannu ko mayar da ragowar gaudan da ta rage madafa bata yi ba ta figi hijabi tayi waje. Da yake su kaɗai 'yan matan gidanne a tsakar gida.
Mardiyyah ta ce, "Nikam yawon nan na Surayyah na ba ni takaici wallahi, ace Innana tana ganin abinda ke faruwa ta kasa ɗaukar mataki. Shi Appa ba kasafai yake wuni gida ba."
"Hmmm!" Kubrah ta sauke numfashi kafin ta ɗaura da cewa, "Ai fa Surayyah sai addu'a Innana kamar tana tsoranta."
Ran Mardiyyah ya kuma kai ƙololuwa wajen ɓaci, magana ma kasa cigaba tayi dayi, domin sam bata ƙaunar wannan mummunan halin da 'yar'uwar tasu, ita kuma ba kanwar lasa ba ce balle a bata shawara, bata ganin kowa da gashi musamman ma Mardiyyah.
Kai tsaye Surayyah gurin tallar Hindu ta nufa, taci sa'a ta kusa sayar da abincin sauran kaɗan. Hindu Tana ganin Surayyah ta saki dariya.
"Shegiya ƙawata nasan daman zaki zo."
"To me zai hana kuwa, ai Sabitu gurasarsa ƙarshe ce dole inzo."
"Kin ga kuwa yanzu Lawan ya bar gurin nan, ba rabon zaku gaisa."
Nan fa Surayyah ta fara dube-dube har da miƙewa tana ƙara hango hanya.
"Gaskiya naji takaici na so ganin Lawan ɗinnan."
"Kar ki damu ƙawata wataran zaku haɗu, in dai kina zuwa nan, yanzu ma ragowar abincin almajirai zan rabawa in tafi gida."
Surayyah ta ce, "To ga almajirar farko, zuba mini nima na dangwali arziƙi."
Ba musu Hindu ta zubawa Surayyah shinkafa da waƙe da miya har da nama yanka biyu.
Tana ci tana santi, "Innana yau gauda tayi wallahi kamar nasan zan sami garaɓasa ban wani ci ba."
"Kai ai kuwa gauda abin marmari."
"Nikam ban cika son shi ba, ko don ana yawan mana shi ne oho."
Miƙewa Hindu tayi ta fara kiran almajirai ai kuwa sukazo da gudu, mutum uku ta sakawa saboda abincin bai da yawa, bayan Surayyah ta gama ci, Hindu ta baiwa mai shagon jikin inda take zama ajiyar kayanta suka doshi unguwarsu Sabitu..
Da yake a ƙofar gida ne ɗakinsu Sabitun yake, ko ince shago, don cirani yazo garin suka kama shagon su uku shi da abokansa da duk sana'ar gurasa suke. Kasancewar ya san zasu zo da wuri ya dawo kasuwa, shi kaɗai suka iske a ɗakin.
A waje suka tsaya, don Hindu ta ce "Mu shiga mana." Surayyah ta ce, "A'a mu da zamu amshi saƙo mai ya kaimu shiga, mu bari dai ya fito idan munyi sallama." Haka kam suka doka sallama ita kam Hindu tura kai tayi ciki domin ba yau ta saba shiga shagon ba.
Ganin sune ya fito yana washe baki.
"To mene ne na tsayawa waje ku shugo ciki mana."
"Ai na ce mu shiga ko abokanka na nan sun sanni Surayyah ce taƙi ya."
"Haba ƙawarmu ku shugo mana sai kace zan sace ku."
Haka kawai Surayyah taji gabanta ya faɗi musamman da taga mutanen kan layin duk sun shige masallaci da ake tayar da sallar La'asar.
Hindu kuwa tunda ta ida magana tayi ciki, Surayyah sai waige-waige take, ya sake washe baki da cewa,
"Zo muje ai ba cinyeki zanyi ba, idan ma na samu da abinki zan barki iyakaci na kwashi rabona."
Ya ƙarashe maganar da lashe laɓɓansa kamar wani tsohon maye. Ganin yadda yake haɗa jikinsa da nata babu shiri ta antaya cikin shagon. Dariya Sabitu ya yi tare da tafa hannu, ya duba gabas da yamma ba kowa duk an shiga sallah, da sauri ya antaya shagon tare da datse ƙofar har da saka sakata...