Sufuri: Kungiyar NURTW ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gyara hanyar Unguwar Bawa- Zuwa Kwanar Dangora

Lalacewar Hanyar

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gyara hanyar da ta hade Unguwar Bawa da Kwanar Dangora mai tsawon sama da mil dari da hamsin.

Wani mai fada a ji a kungiyar Direbobin Manyan Motoci ta kasa NURTW reshen Unguwar Bawa, Alhaji Abdulmumini Yusuf Baragoji ya yi wannan kiran a lokacin da yake tsokaci game da halin da hanyar ta shiga na matukar lalacewa.

Ya ce hanyar mai tsawon sama da mil Dari da Hamsin da ta hade Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna da kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada da kuma Kiru a Jihar Kano ta zama tarkon mutuwa ga masu ababen hawa da suke bin hanyar a kowacce rana musamman a lokacin damina, lamarin da ya zamanto abin takaici.

D'Tigress


Alhaji Abdulmumini Yusuf Baragoji ya ce yin kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yawan motocin da ke kara-kaina a hanyar suna jigilar kaya daga Kudanci zuwa Arewaci, sannan daga Arewa zuwa yankin Kudancin kasarnan.

Da yake cigaba bayani ya ce kungiyar NURTW reshen Unguwar Bawa- tana mai  kyautata zato da tsammanin cewa gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaban Kasa Bola Tinubu za ta kawo musu dauki ta gyara hanyar domin kawo sauki ga masu ababen hawa tare da inganta yanayin sufuri a yankin.

Kungiyar ta yi alkawarin cigaba da goyon bayan manufofin gwamnatin tarayya a kudurinta na kyautata yanayin sufuri domin bunkasar taltakin arziki kasa dana jama'a

Post a Comment

Previous Post Next Post