Alh. Nura Gwaska ya bada tallafin kudin magunguna sannan yayi Alkawarin sanya security Light Don Inganta Tsaro a Asibitin Afaka

Alh Nura Gwaska

Alh. Nura Isma'il Gwaska Foundation: Alh. Nura Isma'il Gwaska Yabada Tallafin Siyan Magunguna ga Marasa lafiya, Yaba kowanne Ma'aikaci N20,000, sannan N100,000 ga Ma'aikatan Sakai tare da yin Alkawarin sanya security Light a Asibitin Afaka Domin Inganta Tsaro Karkashin Gidauniyarsa.

A ranar Juma'a, 1 ga Watan Agusta Alh. Nura Isma'il Gwaska tareda Shugaban Gidauniyarsa Comr. Ahmad Ashir dakuma tawagarsa ya ziyarci Asibitin Afaka inda ya gana da Shugaban Asibitin. 

A zantawarsu, Shugabar Asibitin, ta shigar da korafin rashin hasken wutan lantarki  Wanda hakan Yazama barazana ga tsaron Asibitin idan dare yayi.

Daga bisani, Alh. Nura rabawa dukkanin marasa lafiya dake asibitin tallafin kudin sayen magani. 

Bugu da Kari ya yabawa ma'aikatan asibitin Kyautar Kudi Naira N20,000 sannan Kuma yabawa mata masu volunteer wato ma'aikatan da kai Naira dubu ɗari (N100,000) domin Kara musu kwarin gwiwar cigaba da wayar da ka al'umma.

Daga karshe, Alh. Nura bayan yagana jagororin Gidauniyar Reshen Afaka Karkashin Umar Saraki yabayyana Asibitin cewa wannan shine na farko Kuma maganar haske in sha Allah za'a samar dashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post