GINSHIƘIN DUTSE...
_True life story._
*BOOK 1*
UMMU AFFAN
*Page 7-8*
Cikin fushi kuwa ya amshi bulalar da Mardiyyah ta miƙa masa ya fara lafta mata a jiki. Ko motsi bata yi ba, sai da ya buga mata sau biyar sannan ya tsaya.
"Ina ki ka je daren jiya?"
Ya kuma tambayarta, banza ta kuma yi masa, Mardiyyah ta riƙe baki cike da mamakin ƙarfin hali irin na Surayyah da taurin zuciya sai ka ce ba mutum aka duka ba. Ta ce,
"Yaya Salis gidan kallo fa take zuwa."
"Barni da ita da bakinta nake so ta faɗa ko yau na karya 'yar banza."
Haka yaci gaba da bugunta amma taƙi maganantuwa. Innana ce ta shugo tana tambayarsu lafiya take juyo maganganu a ɗakin, ganin yadda Salis ke bugun Surayyah kuma tana zaune ko motsi yasaka ta riƙe bulalar.
"Salisu lafiya, me kuma ta maka da safiyar Allahn nan har an fara jibgarta?"
Cikin haki ya ce, "Innana Surayyah bata ji, jiya fa kusan sha ɗaya da rabi ta shugo gidan nan, lokacin ina ƙofar gida ina shan iska naga dawowarta, kuma na tambayeta ina taje amma taƙi magana saboda yanzu ta raina kowa a gidan nan, ubanwa zata nunawa taurin kai?"
"Sha ɗaya kuma na dare? Na shiga uku ni Hauwa Kulu, Surayyah ina ki ka je."
Murgyuɗa baki tayi tare da miƙewa kamar zata bige Yaya Salis ɗin ta nufi hanyar fita.
"Surayyah ina tambayarki shine zaki fita?" Cewar Innana dukansu suna bin ta da namujiya.
"Yo ba dole na fita ba Innana tunda gidan nan duk an tsane ni, komi ace ni ce to ina kuwa zanje don Allah ni wallahi sai in bar muku gidanku ma."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!"
Innana ta rafka salati.
"Don ubanki kina da inda yafi nan ne? Surayyah ki kuka da duniya."
Salis zai ƙara bugunta Innana ta riƙe shi.
"Ki bar ni najiwa shegiya ciwo tunda ƙaryar rashin kunya take, don ubanki ki bar gidan duniya ce mai ido a tsakarka wallahi wanda ba a haifa ba ma jiransa take balle ke."
Ƙunƙumai ta fara Innana dai ta tura Salis waje tana faɗin.
"Ka fita ni dai kawai Salisu."
"Ai daman ke ce ke ɗaure mata gindi Innana, wallahi da kin bar ni da ita sai na nakasa 'yar banza naga ƙaryar iskanci."
Haka dai Innana ta dunga tura Salis har zaure sannan ta dawo suka yi kicimis da Surayyah hannunta ɗauke da hijabi.
"Ina kuma zaki?"
Banza tayi mata tana girgiza da gunaguni. Riƙe baki Innana tayi ta ce,
"Nikam wallahi Surayyah kin fita zakka a cikin yaran gidan nan ke wacce irin shaiɗaniyar kan ta ce?"
"Ai dole ki ce haka tunda ba me ƙaunata daman, kuma wallahi na kusa bar muku gidanku."
Fuuw! Ta koma ciki ta bar Innana da ruƙon baki. Mardiyyah kuwa tana ƙofar ɗaki tana rubutunta a ranta tana nemarwa 'yar uwar tata shiriya don abin nata ya girmimi kwandila.
Ko da tazo saitin Mardiyyah ta take ƙafarta da ƙarfi ta shige ciki, da mugun ƙarfi kuwa ta jefar da pensir ɗin hannunta ta fasa wata rikitacciyar ƙara.
A rikice Innana tayo kan Mardiyyah jin irin ƙarar da tayi. Da sauri ta kamata tana furta.
"Oh ni Kuluwa, wannan yarinya kina neman albarka kuwa?"
Ja mata ƙafar ta fara ita kuma tana cigaba da kukan tare da furta "Wash-wash!"
Alamar ba ƙaramar takewa Surayyah ta mata ba, Innana ta miƙe taje ta ɗauko man zafi ta shafa mata tare da mulmula mata ƙafar tana sake bata haƙuri.
"Don Allah Mardiyyah kar ki biye mata kuyi ta faɗa kamar tumakai a gida, wallahi ba na jin daɗin faɗan nan da kuke sai kace ba ciki ɗaya kuka fito ba."
Mardiyyah na hawaye ta ce,
"Amma Innana kina fa gani laifinta ne, yanzu don Allah ta mini adalci ita bata cin tsoran kowa a gidan nan?"
"Ai dai na ce kiyi haƙuri ko, ita kuma ai kanta take mawa baka yi ba ammaka ina kuma da ka aikata? Allah dai ya shirya mana."
Da "Amin." Mardiyyah ta amsa tare da ɗaukar pensirinta tana ƙarashe rubutun Hadis ɗin da Malam ya ba su.
Innana miƙewa taje tayi ta fara hada-hadar ɗaura abincin rana. Ɗanwake zata yi, haka taƙi kiran Surayyah da ke ɗaki sai da Mardiyah ta gama rubutunta sannan ta ɗauki niƙan garin ɗanwaken ta tafi inji kaiwa. Ko da ta dawo Innana tankaɗewa tayi ita kuma tayi sauran wanke-wanken da suka karya na safe sannan ta amshi barkwono tana daka yaji.
Wajen ƙarfe sha biyu na rana Surayyah ta fito daga ɗakin ba wacce ta kalla ta nufi hanyar waje.
"Sai kuma ina da tsakar ranar nan hamshaƙiya?"
Cewar Innana da ke jafa ɗanwake, Mardiyyah dake dakan yaji ko ɗagowa ba tayi ba.
Fuska a kumbure ta ce,
"Zanje in dawo ne?"
"Ai shi ne na tambayi inda zakije ɗin hamshaƙiya mandiya."
Tana tura baki ta ce, "Gidansu Hindu zan amso abuna."
Ko kafin Innana ta kuma magana har ta fice daga gidan. Girgiza kai kawai Innana tayi taci gaba da aikinta.
Mardiyyah ta ce, "Amma Innana da Appa zai fita fa ya ce idan ba aikenmu kika yi ba bai san yaga wata a waje."
"To ya zanyi kuma Mardiyyah, ina ce kina gani a gabanki fa komi ya faru."
Hmmm! Mardiyyah taja dogon numfashi kafin ta ce, "Wallahi wani lokacin har da ke Innana, yo bazaki taka mata burki ba kamar kina jin tsoranta ince ai kece Baabarta ba ita ta haife ki ba."
Daina saka ɗanwaken Innana tayi tana kallon Mardiyyah kafin cikin faɗa ta ce, "Eh kema kin fara tafasa kenan, ni ki ke faɗawa magana haka?"
Shuru Mardiyyah tayi amma aranta tana jin kamar Innana ɗin tafi ƙaunar Surayyah ne shi ya sa komi tayi bata ganin laifinta, ga shi ƙiri-ƙiri ita daga faɗin gaskiya ta fara faɗa, abin da kuma bata yiwa Surayyahn.
Haka har ta kammala saka ɗanwaken ta rufe tare da kallon Mardiyyah.
"Ki dinga duba mini idan ya tauso ki buɗe." Ta ɗauki buta zuwa bayi.
Sai ƙarfe ɗaya Auta ta dawo gida, lokacin an fara sallah ita da Mardiyya suka yi sallah anan ta ɗauko aikin gidan da aka bata ta nunawa Mardiyyah cewa ta koya mata. Kasancewar tana da ƙoƙari sosai Mardiyyah boko da Islamiiyya don ko Kubra da take secondary ba zata nuna mata ƙoƙari ba, ita ce tayi hedgirl lokacin a aji shidda shi ya sa Appa ke bugun sonta sosai saboda ilminta. Amma Surayyah kam bata da wani ƙoƙari sosai hausa ma da ƙyar take iya rubuta komi don wasiƙar da take rubutawa Malam Nura idan ba ka da ganewa sosai ma ba iya karantawa zaka yi ba.
Haka Mardiyyah ta koyawa Autah Mufidah aikin da aka bata lafiya sannan ta duba littattafan nata tana ƙara koya mata wasu abubuwan, da haka har biyu tayi Kubra ta dawo saboda ita sai biyu ake tashinsu. Bayan tayi sallah ne suka haɗu suna cin ɗanwake suna hirarsu ta 'yan'uwantaka har da Innana.
Surayya kuwa bayan fitarta kai tsaye tsohuwar kasuwa ta nufa inda Hindu ke kai tallar abinci saboda ita tana tallah, nan ta zauna suna hira har ta kusan sayar mata da abincin maza suyi ta tsokanarsu wasu har taɓa jikinsu suke a wayance ko wajen amsar kuɗi su miƙo hannu sai su damƙe hannun su ƙi basu kuɗin, sai sun gama taɓa su sannan su miƙa musu, Surayyah ko a jikinta daman haka take so, ƙyautar da wasu ke mata a gurin yafi faranta mata rai shine dalilin da yasa ma take biyowa gurin tallar Hindun, sai da ta tara kuɗi kusan nera sittin don hamsin da biyar ta samu aiko tana murna ta ƙulle kuɗin a ɗan kwalinta ta ce,
"Hindu naga biyu ta kusa, Malam Nura ya kusan tashi a makaranta bari naje kar ya wuce gida ba mu haɗu ba."
Shinkafar ta saya ta nera ashirin taci sannan ta mayar da talatin ɗinta a ɗankwali biyar kuma ta ba Hindu kuɗin da ta ranta mata jiya da dare na amsar film ɗin kallonsu da za a yi.
(Note Kar kuji na ce shinkafar ashirin a mini cha yarda abinci ke tsada, tun farko dai a labarin nan kar ku manta 2010 ne lokacin duniya a kwance take abinci dafaffe har na nera goma akwai.)
Da gudu ta bar gurin sai tsamin rana take wacce ta haɗu da dauɗar jikinta ga kayanta ma duk sunyi dauɗa haka hijabin jikinta sai a hankali amma ba ruwanta bata damu da kowa ya ganta a hakan ba.
Cikin sa'a tana ƙarasawa taga 'yan makarantar suna ta wucewa, nesa kaɗan ta zauna har lokacin da taga Malam Nura ya fito da sauri ta ƙarasa ta bayansa tare da taɓa ƙeyarsa.
Ya tsorata kam ya juyo karaf suka haɗa ido, murmushi ya yi da cewa,
"Ai ni nasan duk garin Katsina ba mai mini haka sai Surayyahta."
Tafin hannunta ta saka tana rufe fuskarta da cewa.
"Ai nima nasan zaka gane don malamina ba shi da tsoro."
"Haƙƙun kuwa, daga ina haka?"
Ya tambaya yana karkaɗe chukk ɗin hannunsa tare da ƙare mata kallo.
Ta rausayar da kai, "Daga gida mana. Kasan idan ban zo na ganka ba bazan iya wuni lafiya ba."
""Hahahahahh! Ya saka dariya kafin ya ce,
"Surayyah kenan 'yan mata adon gari. Nima ai hakan ne, sai dai ba yadda na iya da hukuncin Appanku ban san me yasa baya ƙaunata ba."
Ya ƙarashe a marairaice, tare da fara takawa, Surayyah ma tabisa suka jera ta ce,
"Baka fahimci Appa ba ne, shifa ba sonka ba ne baya yi, wai ka bari sai na ƙara girma to wanne girma wannan girman nawa bai yi ba a haka ko so yake nayi masa kwantai a gida oho!"
Dariya malam Nura ya ɓaɓɓaka..
"Amma ke kam Surayyah baki da dama, ta nan fa yana da gaskiya shekarunki fa sha biyu ya ce mini, nima da ban yarda ba gani nake kin fi haka, amma wautarki ta nuna mini baki fi hakan ba girman jikin ne Allah ya baki."
Tsayawa tayi cak daga tafiyar da suke, da sauri ya juyo yana dubanta.
"Ah lafiya naga kin tsaya?"
"Yanzu kai ma daman duban yarinyar ka ke mini Malam Nura, ni gaskiya ba yarinya ba ce."
Ta fara buga ƙafafuwa a ƙasa. Da sauri ya ƙaraso gabanta tare da riƙe kunnuwansa.
"Allah ya baki haƙuri 'yan matana nima tsokanarki nake, ai ko gobe ne Appa ya aura mini ke."
Hahhhahaha ta saki dariyar jin daɗi.
"Yawwa ko kai fa, ai bana so ana mini kallon ƙarama, ni yanzu jina nake babba."
Murmushi kawai Malam Nura ya yi da haka suka ƙara so santan layinsu ya ce,
"To kije gida kiyi wanka ki huta ko?"
Gyaɗa kai tayi kamar gaske da cewa, ''To sai anjima, amma zaka zo ko?"
"Gaskiya bazan zo ba saboda Appanku ya ja mini kunne ba sau ɗaya ba, ba na son nazo mu haɗu da shi kin ga ba daɗi ko ba komi nima ai Ubana ne ko?"
Ɓata rai tayi.
"To a haka zamu yi ta zance kenan, saboda me zaka ji tsoransa shi ba Allah ba?"
"A'a Surayyah ai shi uba ne dole aji maganarsa, ko saboda ke ai na girmama shi balle Appa ba dai ƙwarjini ba."
Ba haka taso ba sai dai bata kuma cewa komi ba ta juya ta fara tafiya, sai da zata sha kwanar gidansu ta jiyo tare da ɗaga masa hannu, shima daman ita yake kallo ya ɗaga mata hannun sannan ta wuce.
Chak ta tsaya cike da zullumi lokacin da ta hango Yaya Sani ya taho, cikin shigar ƙananun kaya kafaɗarsa rungume da ƙatuwar jakar goyo ta 'yan jami'a. Da alama daga makaranta ya dawo. Don shi a Turai 'yar Adua University yake karatu, azamar barin gurin tayi tare da faɗawa gidan Malam Sa'idu dake kusa da ita, numfashi ta sauke lokacin da taga alamar ta tsira. Zaunawa tayi a zauren gidan inda ta iske yara na 'yar carafke.
"Zan yi."
Ta faɗa tare da zama daɓas a cikin jar ƙasar da ke zauren....