Ginshikin Dutse page 5&6 Complete by Ummu Affan

Ummu Affan Novels

GINSHIƘIN DUTSE...

      _True life story._

*BOOK 1*


       UMMU AFFAN


*Page 5-6*

Kubra ta dubi Surayyah ta ce,

  "Yanzu ke saboda Allah Surayyah wankan ne ba zaki yi ba, yau fa kwana na biyar kenan."

  "Wai jikinku ko nawa? To bazan yi ɗin ba."

Kubra zata yi magana tayi shuru sakamakon shugowar Innana tana faɗin.

  "Surayyah yau ma ba zaki yi wankan ba?"

Mardiyyah ta amshe da cewa,

  "Haka ta ce, kuma gaskiya wari take zan faɗawa Yaya Salisu ya ce ta shimfiɗa tabarma don wallahi warin jikinta yana cutata."

  "Uban warin nake ba wari ba, idan ma mugunya ce a jikina ba ɗan iskan da ya isa ya hanani kwanciya a katifa wallahi."

Innana ta rafka salati.

  "Innalillahi ni Kuluwa, wai Surayyah sai yaushe zaki samu natsuwa, ƙarya tayi ne? Ko ni nan ina jin warin da ki ke saboda rashin wanka ga balaga kin fara da gashin hammata ba dole ki dinga wari ba ace wanka ma ba zaki yi shi a gidan nan ba."

  "Ni fa sanyi nake ji gaskiya a bari gobe mana nayi, haka kawai ayi ta takura mutum, ni babu wanda ya taɓa cewa ina wari sai ku."

  "Ah lallai kin riƙa 'yar nan, to ke kika sani."

Innana na faɗa ta juya Mardiyyah ta ce,

  "Innana ba zaki tilasta ta tayi wankan ba zaki tafi, wallahi tana wari."

  "To munafuka ba za a tilasta nin ba, ke sai ki tilasta ni tunda haihuwata ki ka yi."

  "Ah'ah wace ni, ai naga wacce ta kawo ki duniyar ma baki bayar da ita bakin komi ba balle ni, ni kuma a suwa ɗanwake a hotal."

 "Mtsuwww! Aikin banza taka wuƙar zakara, Sai dai ki tsaya a hakan amma kin san ni na wuce da saninki."

Kubra miƙewa tayi tare da ninke daddumarta da hijabinta, ita ma Mardiyyah hakan tayi tare da fita a ɗakin bata kuma kulata ba, tuwonsu ta ɗauko musu ita da Kubra suka zauna sai ga Mufidah ta kawo musu ruwa ita ma ta zauna gefensu tana cin nata.

Surayyah tana waƙenta ta miƙe tare da nunke takardar da ta kammala rubuta wasiƙarta, ta saka a jakar bokonta ta mayar ta rataye a jikin ƙusar da take rataye jakar sannan ta fita ɗauko nata tuwon.

 Su Yaya Sani duk suna wajen duk suna cin tuwo haka Appa ma duk tare suka shugo daga masallacin, Innana na gefensu tana zubawa Appa miya. A ɗarare ta ɗauki tuwonta ta ajiye kusa da Innana ita ce ta zuba mata miya sannan ta koma ɗaki, tana shiga ta ce, "Mutane sai ka ce sojoji kowa ya zuba mini na mujiya ƙilas ake jira aci mutumcina."

Ba wacce ta kulata har ta zauna cin nata tuwan sai tsaki take ja, kullum duk daren duniya tuwo sai anyi sa abin ya zamowa gidan nasu Farilla. Sojojin gidan sun dawo da wuri da gidansu Hindu ƙawarta zata ce suyi macanje domin su ba kullum ne ake musu tuwo ba kamar nan da ya zamo jaraba, wataran dambu ake musu ko ɗan wake, amma nan kuwa tuwo kullum kamar jidali.

Tana ci tana ɓata rai a haka har taci rabi ta mayar tare da wanke hannuwanta, lokacin duk Yayun nasu sun koma ɗakinsu na zaure, Appa kuma ta juyo muryarsa a ɗaki yana karatu ita ma Innana ta shiga banɗaki tana wanka, tana ganin haka tayi waje daman ta ɗaure hijabinta a ƙugu, kicimis suka yi da Hindu wacce ta biyo mata zuwa kallo da sauri suka tafa, ta ce, "Na godewa Allah da baki kai da shugowa ba don Appa na juyo shi yana karatu."

Hindu ta ce, "Kai Appan nan naku ba dai takura ba. Ni kam zo muje kar ayi nisa don tun ɗazu Saliha ta biyo ta faɗa mini an fara kallon ga shi film ɗin da ake kallo shekaranjiya ne aka ɗauke nepa."

  "Ah ruga muje wallahi film ɗin nan ya haɗu, har mafarki sai da nayi akan sa."

Dariya suka saka tare da rugawa can bayan layinsu gidan Maman Ummi..

Cike suka iske gidan da yara 'yan mata da matasa daidai su, an cika ɗakin Maman Ummi ana kallo, wacce in dai akwai nepa rana ko safe haka ɗakin nata yake cika, musamman da ya kasance mijinta ba mai wuni a gida ba ne haka ko dare sai wajen 11 ko 12 yake shugowa. Ana kallo ana sayen Gyaɗa ta soyu da Maman Ummi ke sayarwa goma-goma. Yanzu ma Hindu ce ta saya musu guda biyu kowa ta goma sannan suka zauna. Wannan dalilin ne yasa Maman Ummi bata kora idan anzo kallo saboda cinikin da take kuma daman yarinyar mace ce ita ma haihuwarta biyu Ummi da ƙaninta. Wani lokacin ma idan ta shige cikinsu ana hira sai ka ɗauka duk ƙawaye ne sa'o'in juna saboda irin ƙaramin jikin nan Allah ya bata.

 Haka suke zaune har tara tayi goma tayi sha ɗaya ta doso kai, ba su ankara ba sai da film ya ƙare domin nepa ba su ɗauke ba. Lokacin sha ɗaya na dare har da kwata nan aka haɗa biyar-biyar kuɗin da za a amso wani film ɗin gobe da za a kalla, yanzu ma Hindu ce ta biyawa Surayyah da niyyar gobe zata zo mata da biyar ɗinta. Kamar nepa suna jira su fito daga gidan Maman Ummi aka ɗauke, sosai Surayyah ta zare ido ganin yadda gari ya yi duhu sosai.

  "Kai Hindu kalli yadda gari ya yi duhu."

Hindu ta ce, "Ai dole gari ya yi duhu, da zamu fito ba kiji Maman Ummi na cewa Sha ɗaya da kwata ba?"

  "Haka ne fa, Allah yasa dai ba a rufe gidanmu ba, bari nayi sauri na san Yaya Sani yaje kallon ball shima yadda aka ɗauke nepar nan yanzu zai koma kar ya rufe gida na shigenge."

Gudu suka fara domin ita Hindu bata da wargi ƙofarsu ta ɓalle daman ba rufewa ake ba.

Tana isa kuwa taci sa'a ba a saka kuba ba, amma an turo ƙofar, da sauri ta cire takalman ƙafarta ta shiga zauren gidan a hankali tana sanɗa ta wuce ɗakin sojojin gidan. Tsakar gidan ma ba kowa, ɗakinsu ta nufa har sun rufe. Turus tayi a gurin tasan aikin Mardiyyah ne kuma wallahi sai ta mata  rashin mutumci da safe, takalmanta ta ajiye sannan ta cire hijabinta ta shanya a igiya ta ɗauki buta, domin fitsari ne cike a mararta, can makwararar gidan ta nufa inda suke fitsari da dare kawai saboda basa son shiga banɗaki musamman cikin dare irin haka, bayan tayi fitsarin tayi tsarki sannan ta dawo bakin ƙofar, kamar ta buga amma idan ta tuna Appa zai ji sai ta fasa ta daɗe tsaye a gurin kafin ta zura hannunta ta wata 'yar ƙofa inda ya tsage jikin ƙofar cikin sa'a taja sakatar ƙofar sai gashi ta buɗe, wata boyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke tura ƙofar tayi ta buɗe sannan ta rufe bayan shigarta, hannunta ta yarfar domin taji lokacin da langa-langar ƙofar yaja mata hannu yaji mata ciwo don ya karceta. Hasken fitar ɗakinsu aci ɓalɓal mai ƙwai ta ƙaro tana duba hannun kuwa taga yadda yaja mata dogon layi har da cini kaɗan, gadan-gadan ta nufi Mardiyyah da ke sharara baccinta hankali kwance don ta kasa danne zuciyarta, bazata iya bari har sai gari ya waye kafin ta ɗauki hukunci ba..

Tunowa da tayi tsaf Appa zai jiyota don yana da saurin jin abu ko da yana bacci ne, hakan yasa dole ta dakata da ƙudurinta zuwa safiyar gobe ta waye.

Ko ɗazun ta ɗauka zai jiyota shi ya sa tayi saurin ɗaukar buta duk da daman fitsarin take ji amma cikin sa'a bai yi magana, don sau tari ko fitsari suka fita wani lokacin sai ya ce, "Waye a nan?" Su amsa da wacce ce fitsari zan yi.

Tura Mardiyyah tayi gefe har sai da ƙafafuwanta suka sauka ƙasan katifar don ganin yadda ta wani babbaje gurin kamar ita ɗaya ce mai katifar. Daman katifun ɗakin biyu ne, Kubra da Auta ɗaya sai kuma Surayyah da Mardiyyah ɗaya, babu tunanin yin sallar da lokacinta babu wani uzuri da ya riƙeta haka yanzu da ta dawo ko tunanin yinta ba tayi ba tabi lafiyar katifar zuciyarta cike da turirin fushi akan Mardiyyah, ji take daman yanzu safiya tayi saboda kawai ta shuka mata rashin mutumcin abinda ta aikata mata, don har lokacin zafin karcewar take ji sosai. Da wannan tunanin bacci ya ɗauki Surayyah.

 Ana kiran sallar asubah kamar yadda Appa ya saba kafin ya wuce masallaci sai da ya buga ƙofar ɗakin 'yan matan. Kubra ce ta buɗe. Ya ce,

  "Yawwa Kubra maza ki tashi 'yan'uwanki kuyi sallah."

  "To Appa, sai ka dawo."

Amsar da ta bashi kenan tana mutstsika ido na mai bacci, yayin da ya nufi zauren gidan ɗakin samarin, mazan kuwa duka yake tasa su gaba su tafi masallaci.

Kubra ta fara ƙoƙarin tayar da Autah sannan ta tayar da Mardiyyah. Haka ta fara taɓa Surayyah wacce cikin magagin bacci ta ce,

  "Mene ne kuma?"

  "Appa ya ce a tashi ayi sallah."

Ta faɗa tare da nufar hanyar fita ɗakin, Surayyah taja tsaki tacigaba da baccinta. 

Haka duka su ukun suka dawo ɗakin bayan sunyo alwala amma Surayyah na sharar baccinta, kasancewar sun san halinta ne kullum haka suke da ita ba su taɓa tashin ta ta tashi, bayan sun idar Kubra fita tayi ta kunnawa Innana wutar murhu ta ɗaura ruwan dama koko sannan ta dawo ɗakin Mardiyyah da Autah duk sun koma sun kwanta, har zata kwanta ta kuma zuwa katifarsu Surayyah ta fara bugunta.

  "Wai ke Surayyah ba zaki tashi kiyi sallah ba? Kullum sai rana ta fito gatse-gatse sannan zaki yi alwala wallahi kiji tsoran Allah, hatta Autah Mufidah tayi sallah sai ke kin kasa tashi.

  "Wayyo kaina! Wai ina ruwanki da baccina dole sai kin takura mini? To bazan tashi ba kizo ki tada ni dole mtsuww!" 

Ta ƙarashe da jan tsaki. Sannan ta ƙara gyara kwanciyarta tare da juyawa Kubra baya.

  "To Allah ya shiryaki ya kuma ƙyauta miki, ni dai na sauke nauyin da Appa ya ɗaura mini."

Ta tashi ta koma katifarsu ita ma ta kwanta, nan kuwa bacci ya sake awan gaba da ita kamar sauran 'yan'uwanta.

Innana bayan ta kammala addu'o'inta ta fito ta isa wutar kafin ta koma ciki, sam ita bata komawa bacci aikace-aikacenta ta fara, sai da ta fara gyara ɗakin sannan ta fito ta dama kamu, daman tana da ƙullunta domin da yawa take markaɗawa ta ta ce sai ya mata sati tana damawa, bayan ta dama kokon ta mayar da numamen tuwo.

Misalin bakwai na safe Mardiyyah ta fito daga ɗakinsu, gawayi da ɗan gishiri kaɗan ta dandaƙa ta wanke bakinta da hannu take murza haƙoranta, ai kuwa tana wankewa sai gasu sun fito ras. Wanke-wanken da ke bakin rariya ta harhaɗa tare da ɗauko omo taja ruwan rijiya ta fara. Kubra ma da ta fito bakin ta wanke kamar yadda Mardiyyah tayi sannan ta kama sharar gidan.

 Har suka kammala hamshaƙiyar bata farko ba sai sharar baccin asara take, Autah Mufidah ma tuni ta tashi tayi abin da ke gabanta.

Farau-farau suka fara sha wato kokon sannan suka ɗaura da dumamen tuwon, har Samarin gidan Autah ta kai musu nasu ɗakinsu haka Innana da Appa suna ciki suna kari. 

Fuska a murtuƙe ta fito daga ɗakin, ko kallonsu bata yi ba, ta nufi bakin rijiya taja ruwa a buta. Banɗaki ta shiga ta daɗe ciki don ƙa'ida ne duk safiyar duniya sai tayi bayan gida. Ko da ta fito wani ruwan ta kuma sawa a buta fakam-fakam tayi alwala ko ince ɗauraye fuskarta dake da yan bacci da hannayenta sai kuwa ƙafarta. Ita ko yadda suke wanken bakin nasu bata yi, wuce tayi ta zuba farau-farau ko kallonsu bata yi ba ta koma ɗaki, su ɗinma ba wacce ta kulata a cikinsu.

 Suna kammalawa suka doshi ɗaki, Kubra ta shirya cikin uniform ɗinta na 'yan junior secondary ta gwamnati, yanzu tana Jss 2, haka ita ma Mufidah ta shirya cikin nata kayan na 'yan Primary domin ajinta biyar yanzu. Mardiyyah da Surayyah kam basa zuwa suna jiran fitowar jarabawarsu ne, don sun kammala primary ɗin.

 Bayan Kubra da Autah sun wuce makaranta Mardiyyah ta ɗauko jakar makarantarta ta islamiyya ta fara karatun Hadisi saboda jiya malaminsu ya ba su aikin gida tana so ta rubuta.

 Surayyah tana shan koko tana harararta, jira take ta kammala taci mutumcinta, yadda ba kowa ɗakin har ta tsara yadda zata daketa iya dakuwa, sai ta nuna mata abinda ke turewa buzu naɗi zata gane kuma kurenta.

 Tana kammalawa kuwa ta fitar da kofin waje tare da dawowa ɗakin ta tura ƙofar ta saka kuba. Da sauri Mardiyyah ta ɗago tare da furta,

  "Mene ne haka kuma? Kina ganin dai rubutu zan fara shine kika rufe ƙofar."

Cikin masifa Surayyah tazo gabanta ta tsaya tare da liƙe ƙugu.

  "Kaɗan ma ki ka gani daga aikina. Wallahi yau sai na fasa miki wannan shegen bakin naki sannan na rama karcewar da ki ka saka nayi. Jiya uban waye yasa ki rufe ƙofa da kuba bayan kin san ban shugo ɗakin ba?"

Mardiyyah maganar ta bata haushi itam ma miƙewa tayi ta ce,

  "Amma ai ba ni na saka ki fita da dare ba ko? Bayan Appa ya hana zuwa gidan kallon ke dole ne sai kin je? Ace kina mace amma baki da kamun kai fita gidan kallo kuma da dare sai ka ce mara mafaɗi to ba da ni ba gaɗa a hurumi kina mini rashin mutumci wallahi zan faɗawa Appa komi. Daman su Yaya Sani suna gida sai ki ɗanɗana kuɗarki tunda ke kunnan ƙashi ne da ke."

Surayyah taci ƙwalar Mardiyyah tana furta.

  "Ni ki ke faɗawa haka, to wallahi duk uban da zaki faɗawa kin daɗe baki faɗa ba, yau mai raba ni dake a gidan nan ban gan shi ba."

Buga ƙofar da aka fara ne yasa dole ƙanwar naƙi Surayyah ta saki ƙwalar Mardiyyah tana girgiza irin na zallar bala'in nan.

Mardiyyah taja tsaki tare da nufar ƙofar ta buɗe. Yaya Salisu ne ya ce, "Uban mene ne kuma na kulle ƙofa da safen nan?"

  "Ni babu ruwana Surayyah ce, kuma wai ta rufe ne zata dake ni."

  "Ehye! Ke Surayyah kina ina?"

Ya daka mata tsawa, tana wani gunaguni ta ce, "Gani nan."

Ganin bata da niyyar fitowa shugowa ɗakin ya yi, aiko yana ƙarasawa ya wanka mata mari, riƙe kuncin tayi tana zare ido ko ƙwayar hawaye babu.

Cikin faɗa ya ce, "Don ubanki bayan ƙaryar da kika mini jiya wai Innana ce ta aike ki ashe yawanki kika je kin ga ban kulaki ba, shi ne ya baki damar fita da dare jiya ko? Gidan ubanwa kika je? Ina zaune ƙofar gida naga dawowarki sha ɗaya ma ta wuce na dare ina kika je a daren nan?"

 Hannunta riƙe da kuncinta ta masa banza.

  "Ba tambayarki nake ba ko sai na tattaka ki ne?"

Nan ma banza ta ba ajiyarsa ko ɗagowa ta kalle shi ba tayi ba, sai wani ɓata rai da tayi tana wani girgiza kai. Ya ce,

   "Tabbas marin nan bai shige ki ba ne." Ya kalli Mardiyyah.

  "Ɗauko mini bulalar Appa, yau sai ta gane bata da wayau wallahi tunda ta raina kowa a gidan nan bata ganin mutumcinmu."

Da sauri Mardiyyah ta fita yayin da Surayyah ko motsi ba tayi a inda take ba duk kuwa da tana jin abin da yake cewa.....

[8/3, 11:35 AM] Ummu Affan:


Post a Comment

Previous Post Next Post