Tsantsar Kauna
Page 39
Written by Tahir Yusuf
Kai tsaye falo na muka wuce Ni da Khadija, nan muka zauna tana jajanta min kan maganar aure da Kamal zai ƙara.
"Fatima wannan maganar ba ta min daɗi ba gaskiya, ban san me ke damun mazan yanzu bane, daga sun ji su da yan wasu kuɗaɗe sai su fara maganar ƙara aure"
"Hmmm! Ke dai bari ba abinda na iya haka dole zan haƙura, na ɗauki wannan abin a matsayin Ƙaddara ta, don babu wanda zai hana faruwar hakan sai Allah"
"Amma dai gaskiya ba daɗi ko shekara biyar ba'a yi da aure ba an fara maganar ƙarin aure"
"Kada wannan abin da ya dame ki babu yadda muka iya ba'a jikina zata zauna ba, ba kuma inda nake za'a tashe Ni a saka ta ba"
"Allah dai yasa mu dace, amma kuma Gara tun yanzu ayi ma mutum kishiya da ƙuruciyarsa kada sai ka tsufa a ɗauko maka 'yar ƙaramar yarinya sa'ar 'ya'yanka"
"Shiyasa ma ban damu ba, duk abinda take taƙama dashi ina dashi, kila ma na fita, zan yi yaƙin kwatan gidana da ƙarfina."
"Allah yasa dai kada ya zo da matsala"
"Idan ta so a zauna lafiya, in sha Allah zan a zauna lafiya, amma idan bata neman zaman lafiya ina daidai da ita."
"A'a kada ki ɗaga hankalin ki, kin fita sanin abinda Kamal ke so, tun yanzu Yakamata ki ƙara dage dantse wajen kwatan gidan ki, kin san irin abincin da yafi so da abinda baya so, hatta irin kayan da ya fi so ki saka min sani"
"In Sha Allah na zamu zauna lafiya da ita, addu'ar da zan yi kema dai Allah ya kare ki tun da kin ga bakin su ɗaya komai tare suke yi"
"Abinda ke bani tsoro kenan, Allah yasa idan ma zai ƙara ɗin Allah ya bashi wanda zamu zauna lafiya tun da Abu ne wanda baza ka iya hana su ba in har sunyi niyya."
"Maza, hmmmm!"
"Allah dai ya sa mu dace, bari ki gani na zo na koma gida naga har 12pm tayi"
"Lokacin ne yanzu babu wuya, nan da nan zaki ga rana tayi"
"To Naman Ahmad, Allah ya tsare hanya."
Na tashi na buɗe mata gare ta shiga motar ta fita na kulle na dawo cikin gida.
Kamal da Abdullahi kuwa rusa wuta kawai suke yi a hanya suna tafiya suna hirar rayuwa da yadda aka fara soyayya gashi har an fara maganar aure.
Mu haɗu a page 40 don jin yadda labarin zai cigaba.
Wadanda basu yi Following wannan page ɗin ba suyi domin samun littafai masu daɗi na marubuta daban-daban.
Kada a manta da.
Like, Comment and share.Tsantsar Kauna