Tsantsar Kauna
Page 38
Written by Tahir Yusuf
Washe gari da sassafe na gama shiri ina jiran Abdullahi ya zo, Fatima kuwa kan dole zanyi wannan don ba so take ba, ko Murmushin da takeyi nasan a baki kawai takeyi tana yi ne don rufe abinda ke damun ta.
Ko wace mace tana da kishi, saidai kowa tana da irin yadda take nuna kishi akan abinda take so, itama Fatima tana da irin nata kishin, na gane hakan ne tun lokacin da na sanar da ita zan ƙara aure har zuwa yanzu tana biye ɓacin ran ta ne don Ni ta faranta min.
Tana Kallona cike da damuwa ganin yadda na shirya tsaf baki na yaƙi rufewa,
"Kana ta zumuɗi sai ka ce yau ne ranar ɗaurin auren" Fatima tayi magana can ƙasan maƙoshinta wanda idan mutum ba ya natsu bane ba zai ji me take cewa ba yana yi yadda tayi maganar.
"Uwargida sarautar mata, tuna nakeyi, ayi haƙuri na yau ne kawai"
"Hmmm! Maza kenan"
Na ɗan ɓata rai na kalle ta "me kuma maza sukayi"?
"Bakomai ban san maganar da nayi ma ta fito na"
"Fatima, kada ki saka damuwa a ran ki, in Sha Allah zaki zaki sami Maryam matsayin ƙanwa, 'ya Uwa da kuma abokiyar zama ba kishiya kamar yadda kuke faɗa ba."
"To Allah yasa ya kuma tabbatar da Alkhairi, amma so da yawa mutum na iya canzawa cikin ƙanƙanin lokaci"
Ƙarar da waya ta ce ta fara alamun kira ya yanke fitar da muke yi da Fatima, suna Abokina ya fito a fuskar wayar wato Abdullahi ne ke kira, da sauran na ɗauka tare da kara wayar a kunne na,
"Assalamu alaikum warahmtullahi talala wabarakatuhu"
Nima amsawa nayi da Amin Wa'alakumussalam warahmtullahi talala wabarakatuhu"
"Da fatan dai ka gama shiryawa"
Na shirya kai kawai nake jira"
"Ok, bani mintinan 10 ganinan zuwa"
"Allah ya kawo ka lafiya"
Janyo Fatima jikinsa na nayi wanda ke sanye Da Kayan bacci a jikin ta riga ce mata hannu sai dogon wando launin fari da ratsin flower mai launin ruwan gida, na saka hankerchief na goge hawayen da ya fara zufa daga idon ta.
"Fatima menene abinda kuka, tafiyar nan da in sha Allah jibi da sassafe zamu dawo, dan Allah ki kwantar da hankalin ki"
Ƙasa magana tayi sakamakon fashewar da tayi da kuka, "Fatima....". Horn ɗin motar Abdullahi yasa Fatima miƙewa da sauri ta shiga cikin ɗaki ta shiga ban ɗaki ta wanke fuskar ta sannan ɗauko wani ƙaramin hijabi wanda bai wuce gwiwar ta ba ta saka kafin ta fito falo.
Riƙe na ke da kakar kayan Kamal muka fita tsaƙar gida don nayi masa rakiya, daga nan mu gaisa da Abdullahi.
"Wai dama tare kuke"? Na tambayi Abdullahi ganin matarsa a gaban mota.
"Eh muna tare ganin da motar Kamal zamu tafi yasa nace tazo idan mun tafi ta koma da motar gida sai tace daga nan ma sai ta yini Miki ta tatali hira"
"Ai kuwa da na ji daɗi sosai, to bari na buɗe sai ka shigo da motar"
Kamal ya buɗe ƙofar (gare) Abdullahi ya shigo da motarsa yayi parking ta inda ba zai hana motar Kamal fita ba.
Basu dauki lokaci ba mu Kayi Sallama suka wuce, mu kuwa muka shiga cikin gidan don yin hira.
Mu haɗu a page 39 don jin me zasu tattauna, Ya tafiyar su Kamal zai kasance.
Wadanda basu yi Following wannan page ɗin ba suyi domin samun littafai masu daɗi na marubuta daban-daban.
Kada a manta da.
Like, Comment and share.