GINSHIƘIN DUTSE...
True life story.
BOOK 1
FATIMA SUNUSI RABIU
Ummu Affa
HAƘƘIN MALLAKA: Ummu Affan ban yarda a juya mini littafi ta ko wacce irin siga ba, ba tare da izini na ba. Da fatan za a kiyaye haƙƙin mallaka.
Page 1-2
Katsina State 2010
Unguwar Rimaye.
A daidai lokacin Alhaji Ɗahiru ya biyo yarinyar da bulala har ƙofar gidan, yadda ya daddage yana kaiwa yarinyar bugu da bulalar dorinar mai baki biyu da hannunsa sai ka ɗauka wata balagaggiyar yarinya ko budurwar mace ce. Sai dai a ƙiyashin shekaru yarinyar ba zata wuce shekaru goma sha ɗaya a duniya ba, sai dai yanayin girman jiki na yarinyar da kurman jiki da Allah ya bata, a kallon farko sai ka ɗauka takai goma sha biyar koma sama da hakan. Sai dai, abin da zai matuƙar baka mamaki da ɗaure kai shine ko ƙwayar ƙyalla babu a idanuwanta duk kuwa da irin shauɗa mata bulalar da Mahaifin nata ke mata. Ga idanuwanta ƙur a kan shi tana kallo ranta a jagule tamkar zata kai mishi bugu.
Ƙarasowar Babban Yayansu Auwalu, tare da riƙe bulalar hannu Appan nasu kamar yadda suke kiran shi ya dakatar da bugun, inda ya dunga sauke numfarfashi tamkar wanda ya yi tseran gudu. Sosai ya jigata da dukan da ya yi mata wanda ita da aka dokon ko ɗaya alamominta ba su nuna ba.
Cikin haki da matuƙar fusatuwa Appan yake furta.
"Haba Auwalu, har yaushe ruwan ya tafasa balle kuma ya ƙone? Tun yanzu Surayyah tana nuna wannan mugun baƙin halin da taurin kai ina kuma ga nan gaba lokacin da shekarunta suka ƙara yawa?"
Kama hannun Appa ya yi, tare da duban yara har ma da kaɗan daga manya da suka farawa ƙofar gidan nasu cincirindo ya ce,
"Appa kazo mu koma ciki, kaga mutane sun fara taruwa."
Haka Auwalu ya dunga jan Appan nasu har ya komar da shi ciki.
Da hanzarinta ta miƙe ganin shigewarsu tare da waigowa ga mutanen dake gurin ta riƙe gudu tana karkaɗawa.
"To munafukai sa'idonawa ana ruwa kuna irgawa, masu zuwa lahira da ido ɗaya. Sai ku wuce, idan kuma kwana zaku yi ai ga fili ga mai doki. Mtsuww!" Ta ƙareshe da sakin dogon tsaki.
Yaran tuni suka tarwatse saboda sun san halinta ba ƙaramin aikinta ba ne ta rufe su da dukan tsiya kuma uwar yaro tazo ita ma ta tsuka mata zagi da cin mutumci. Manyan ma wucewa suka yi suma mata addu'a wasu kuma suna zaginta. Sai mutum ɗaya ya tsaya yana cewa.
"Ke dai Surayyah iyayenki sun yi asarar haihuwarki, wallahi da na haifi irinki gara ayi ɓarin cikin yar bula'uba kawai, tur da haihuwar irinki.''
"Kai ne matsiyaci tsananne ba ni ba, to me yasa baka zo kasa uwata tayi ɓarin cikin nawa ba tunda kai ne ubana? Ai yaro maso min babba, kai ma daga ganinka da hakan ka tashi kaga kuwa ashe Talle ba ta wa Audi gori."
Zai yi magana ya yi shuru sakamakon fitowar Yaya Auwalu yana aika mata wani kallo.
"Zo ki wuce fitsararriya!"
Tura baki gaba tayi tana ƙunƙunai tare da wucewa ciki a fusace tamkar wata zakanya.
Ya gyaɗa kai yabi bayanta. A tsakar gidan nasu da yaji Tas mai ɓalle-ɓalle an share shi fas sai ƙyalli yake suka iske Appa zaune saman kujerarsa da yake zama musamman idan zai yi karatu ko kuma hutawa idan yana zaune tsakar gidan. Innana zaune gefensa tana bashi haƙuri da faɗin har yanzu Surayyah ƙaramar yarinya ce.
"Wallahi Kuluwa ki rubuta ki ajiye ko ba na raye na faɗa miki wata rana sai Surayyah ta saka ki kuka da hawaye, ba hali a daki yarinyar nan ko ayi mata wani hukunci sai ki dage faɗin yarinya ce sai haƙuri ko? To kici gaba kar ki fasa, yanzu ma ai naga ba raga miki take ba amma kullum kina goyan bayanta."
"Fata dai na gari lamiri Malam, bai kamata kana faɗa mini haka ba, ai nasan ba zaka zo ace nan gaba ta fanɗare mini fiye da haka ba, ɗan yau kuwa kowa ya sani sai addu'a." Faɗar Innana cikin rashin jin daɗin maganar da Appan ya faɗa akan Surayyah.
Ita kuwa ko ajikinta, tana shugowa fuww ta wuce ta gabansu ba tare da ta kalli kowa ba, har zata shige ciki Yaya Sani da ya shugo yanzu ya daka mata wata muguwar tsawa.
"Ke zo nan don ubanki."
"Ba dai ubana ba." Ta faɗa a hankali yadda ba zai iya juyowa ba, sai dai Innana dake kusa taji abin da ta faɗa, hakan yasa ta ɗago tana ƙare mata kallo, yayin da Sani ya ce,
"Uban me ki ka ce?"
"Ni ban ce komi ba."
Ta faɗa tana tura baki gaba bayan ta zauna daɓaram kusa da Innana.
Appa ya girgiza kai cike da takaicin 'ya guda ta take son haihawar jininsa, domin tuni ta saka mishi hawan jini, 'ya'ya takwas Allah ya ba su maza huɗu mata huɗu, Surayyah ita ce 'yarsu ta bakwai a gidan kusa da auta. Amma babu wacce take haifar musu da matsala kamarta, Tun daga kan Auwalu babba har zuwa Mardiyyah ta shidda basu samu matsala ba sai akan Surayyah domin ko ƙanwarta Auta wato Mufidah bata aikata kwatar abin da Surayyah ke musu a gidan nan. Yayunta su daka Appa ya daga amma duk a banza domin duka kam ya gama zama jikinta. Yanzu sai dai a dake ta tana tsaye ƙiƙam kamar doki, wai tayiwa duka kuka? Ai wannan tsohon ya yi ne a gurin Surayyah. Sai dai kai da kake dukan nata ka gaji ka bar ta, amma ko ɗar bata yi.
"Uban me ki ka yiwa Appa? Yanzu ake faɗa mini wai har waje yana dukanki ana cewa ƙanwata na san ke ce zaki aika, wallahi da ina gidan nan sai na karya ki ba zaki takura mana tsoho ba."
"Sani ka rabu da ita tunda dai ya duketa, ni ba na son ƙananun magana ga mutane munafukai komi akayi sai ya zama abin magana a unguwa, ban san me ya sa 'yan layin nan suka sakawa Surayyah ido ba, shin ita kaɗai ce yarinyar da bata ji, wallahi akwai waɗanda ma suka fita fitsara."
Faɗar Innana cikin faɗa tana hayaiyakowa Sani. Appa ya ce, "Kuluwa ki kuka da kanki akan tare mata faɗan da kike, shin ba za a mata faɗa ko a dake ta ba. Gaki ga Surayyah nan, ni ba baki nake muku ba amma tabbas nan gaba zaki ce na faɗa."
Tashi ya yi tare da shigewa turakarsa, yayin da jikin Innana ya yi sanyi sosai. Auwalu ne ke faɗawa ƙaninsa Sani abin da Surayyah tayi.
"Kasan Appa ya hanata kula malaminsu Nura sanadiyyar hakan har canjen makaranta ya mata ka sani, shine ya dawo aiki ya gansu a layin baya wai suna zance kamar Surayyah shekara goma sha ɗaya, ya mata magana ta ce ita fa dole ya barta da Nura, in takaice maka zance kamar zata zagi Appa wai kawai ma ya aura mata Nura ba zatayi karatun ba, yarinyar da a shekarar nan ta kammala Primary ko jarabawar shigarsu Secondary bata fito ba."
Kama baki Yaya Sani ya yi, tare da nufarta gadan-gadan, tashi tayi tana nufar bayan Innana bakinta bai mutu ba, tana faɗin.
''Yo ina ruwan wani da rayuwata, ni ce na zaɓi zamana a hakan ba na son karatun kuma wallahi bazan yi makarantar ba."
Innana ta kauce tana faɗin, "Sani zo ka fasa bakin tunda rashin kunya ba za ta bari ba."
Da gudu ta shige ɗakinsu, Sani kuwa yabi ta don sam bashi da haƙuri zuciyarsa kusa take ya tsani raini, shi kuwa Auwalu yana da sanyin hali da tausayi sosai, ko kafin Sani ya isa ga ƙofar har ta banko ƙofa da ƙarfi kuwa Sani ya fara ciniyar buɗe ƙofar.
Ai tana turo ƙofar tun kafin ƙarasowar shi ta saka kuba, sakamakon hakan ya saka duk kiciniyar da yake na ƙofar ta buɗe ta gagara.
"Matsoraciyar banza kawai, zabuwa ga tunon faɗa ga tsoro da ki tsaya mana, wallahi da na karya yarinya naga ƙarshen rashin kunya."
Yaya Sani ya faɗa ransa a ɓace duk da haka bai daina ƙoƙarin ganin ƙofar ta buɗe ba.
"Tabb ba kasan cewa karan bana shike maganin zomon bana ba ashe."
"Ki ka ce me?"
Banza tayi da shi, Innana ta ce, "Da ka rabu da ita da yafi, domin idan Surayyah ce bakinta ba zai yi shuru ba, sai dai ta ƙara maka ban haushi. Shegiyar kafiya ce da ita ga naci kamar kuturu."
"Na barta a yanzu amma ki faɗa mata karona da ita ba zai mata kyau ba, sai ta gane kurenta."
Surayyah daga cikin ƙuryar ɗaki tana jinsu, sai wani girgiza kai take kamar kaɗangaruwa tana girgiza ƙugu da cewa,
"Can da su gada, amma ba mai taɓa ni na ƙyale. Ai ni ba jaka ce ba, Appa ma don ubana ne ba yadda zan yi da shi ne, amma ku kuwa kun daina dukana na tsaya ai ba jaka Innana ta haifa muku ba."
Kubra da ke kwance a ɗakin ta buga wani uban tsaki.
"Surayyah nifa kin takura mini, da surutunki zan ji ko da ƙofar da kika rufe duhu ya mamaye ni?"
"Ah'ah Kubra ɗakin nan fa ba ke kaɗaice da shi ba, mu huɗu ne, kuma ko wacce tana da iko gidan ubana ne, ki bari idan kinje naki ɗakin na kai wato gidan miji sai ki nuna ikonki amma ba a na gado ba ahha!"
Kubra ba mai surutu ba ce, bata magana sai an ƙureta ita ce ta biyar a gidan Sannan Mardiyyah sai Surayyah amma duk da ganin ta bata shekaru har biyar hakan bai sa taƙi mata rashin kunya da na cin mutumci ba. Shiyasa Kubra idan ta kula Surayyah to abin ya dameta ne. Amma halinsu guda da Yaya Auwalu ba dai sanyi ba. Kau da kanta tayi tare da runtse ido a ranta tana faɗin 'Kanki ake ji' Hakan da tayi kuwa bai saka Surayyah yin shuru ba sai surutu da habaici take mata, ita dai bata sake kulata ba.
Sai da ta tabbatar Yaya Sani ya bar gidan sannan ta buɗe ƙofar. Mardiyyah da tun ɗazu take jiran ta buɗe ta fara masifa.
"Wallahi ke dai anyi mai mugun hali Surayyah, tun ɗazu na fito banɗaki nayi wanka kaya zan saka na wuce makaranta amma kin rufe ɗakin. Shin wannan wanne mugun abu ne har jikina ya bushe ko mai na shafa ba kamawa zai yi ba."
"Na rufe ɗin, ai da kin zo kin karya ƙofar kin shiga. Idan kuwa baƙin hali gare ni har da ke dukanmu domin gado mu kai."
"Ke dai ce kika gada, kuma ba mu san gurin da kika gado shi ba, da shegen bakinta mai tsini kamar zomo."
Ai fa Surayyah ta chakumi Mardiyyah da faɗa. "Wace ce mai dogon bakin? Wallahi Allah bazan rabu da ke ba."
Faɗa sosai suke, daman Surayyah ba dai iya dambe ba, ƙarfi gare ta kamar namiji saboda duk wasan maza shi take yi. Kuma daman tsakaninsu kamar mage da ɓera sam basa shiri faɗan saƙo da saƙo ya aure su. Gashi Mardiyyah ita ce babba kuma ita ce ke shan wuya kamar yanzu ma, kafin Innana tazo ta raba su tuni ta galabaita, zanin da ta ɗaura Surayyah ta fincike shi ya faɗi haka duk ta ji mata ciwo yakushi a fuska haka wajen wuyanta. Daman ko a girman jiki Surayyah tafi ko Kubra baza ta nuna mata girma ba, shiyasa ma idan ba sani kayi ba sai ka ɗauka duk ita ce yayarsu. Da ƙyar Innana ta raba su tana tambayar me ya haɗasu domin ta shiga madafi (Kitchen) duk aka fara tsiyar. Cikin kuka Mardiyyah ke mayar mata da zance, Surayyah kuwa sai aika mata da harara take babu alamar ta gaji sai wani kumbura take kamar an zuba yis a fulawa. Innana wani lokacin har gani take anya Surayyah bata da mutanen ɓoye, lamarin nata yana bata tsoro da ɗaure mata kai. Haka ta ba Mardiyyah haƙuri da faɗa mata ta daina biyewa Surayyah tunda ƙwararta take. Tana kuka ta ce,
"Bari Yaya Salis da Yaya Sani su dawo, wallahi sai na faɗa musu duk abin da kika mini mara mutunci."
"Ahayye!" Ta buga shewa da ɗaurawa da cewa.
"Surayyah taci dubu sai ceto, ko su nan gani nan bari wallahi haka zasu bar ni ba yadda suka iya da ni ato."
Ta buga ƙafa da ficewa daga cikin gidan, Innana na tambayar ina zata ko juyowa bata yi ba balle na sakaran zata bata amsa haka ta ƙarawa ƙafarta mai.
Sai dai rashin sa'ar da tayi tun kafin ta ɓullewa kwanar layinsu ta iske su Yaya Auwalu da abokanansa zaune a majalisarsu, yana ganinta kuwa ya ce,
"Surayyah ba lokacin islamiyya ya yi ba? Ina kuma zaki?"
Tura baki tayi cike da takaicin ganinsa a gurin, a ranta ta ce, 'Aikinku kenan zaman majalisa tun kuna yaranku da ku, ayi da gulma da tsegumi da zancen 'yan mata sai musun ball abin da kuka iya kenan da kallon 'yan mata idan za a wuce kuna gulmarsu.' A fili kuwa yaƙen ƙarya ta ƙwaƙwulo domin tana ragawa Yaya Auwalu ne saboda baya bugunta sai dai ya mata nasihar dake bi ta bayan kunnenta ta ce,
"Innana ce ta aike ni na amso mata kayan miya gurin malam Sule."
"To kiyi sauri ki koma, kin ga lokacin islamiyya na ƙurewa."
Da gudu ta falla tana dariyar ƙeta. Wallahi duk a yayunta babu dolo kamar Yaya Auwalu komi ka ce sai dai ya ce tom ga shi shine babba duk gidan sai dai ya zamo ƙarami saboda Sani da Salisu duk sum amshe girman idan wajen shuka rashin mutumci ne wa ƙannansu...
_Kamar yadda na faɗa labarin nan ya faru a gaske, ina fatan zaku ba ni haɗin kai kuma ku biyo ni domin ɗaukar darasin da ke cikin labarin nan mai cike da abubuwan takaici, baƙinciki, haushi, kuka, danasani, kaico, kai har da dariya. Fatana ku bi ni sau da ƙafa domin ɗaukar ilmin rayuwa da ke cikin labarin wanda dalilin ma har yasa nayi zaman rubuta muku shi. Aka ce dai komi ya yi farko zai yi ƙarshe sannan ƙarshen alewa ƙasa..._
An samu sauyawar gari, sunayen jarumai da wasu abubuwan a ciki amma kaso 80/100 abin da ya faru da gaske ne.
08104335144
U M M U A F F A N