Tsantsar Kauna Page 37 Complete

littafan Zafafa 5 hausa Novels

 Tsantsar Kauna 

Page 37


Written by Tahir Yusuf

Sosai Na sami natsuwa ganin yadda Fatima ta kwantar da hankalinta, "In sha Allah zan kula da Fatima sosai, domin mace irin Fatima ba abin wulakantawa nace ko yarwa ba, ya Allah ka bani ikon kula da ita da abinda ya haifa da wanda ma zata haifa nan gaba, Ya Allah ka bani ikon yin adalci a tsakanin su"  na cigaba da tunanin zuci har bacci ya ɗauke Ni.


Washe gari da sassafe na tashi ganin Fatima tana jin daɗin baccin da takeyi bana so na tashe ta, yasa na shiga kitchen na shirya mana Breakfast, na shirya a a farko inda muke karawa, na dawo cikin ɗaki.


"Fatima, Fatima ki tashi "


"Innalillahi wa'inna Ilahirraji'un, meyasa baka tashe Ni ba ƙarfe 10am da"

Da sauri Fatima ta tashi ta shiga nan ɗaki ta yi brush ta fito da niyyar shiga kitchen ta shirya Breakfast, na zauna a kan gadon ina ta dariya ganin yadda ta ruɗe, fita farko, ganin yadda fakon yayi tsaf kamshi turare kawai ke tashi ga wani irin ƙamshin abinci wanda bata taɓa jin irin sa ba ta tsaya tana ta mamaki yaushe ya tashi yayi wannan aikin.


Da gudu ta dawo cikin ɗaki daidai lokacin ya miƙe zai fito, tayi tsalle ta rungume shi ta sumbace shi, kamar ba wacce za'a mata kishiya ba, ta ƙara kwantar da kan ta a ƙirjina, cikin Muryar shagwaɓa ta tace 

"yaushe ka iya girki?


"Na iya girki sosai,"


"To amma a ina ka koya?



"Ina da mata wacce ta iya girki sosai ta ya nuna bayan iya ba"


"Hmmm! Nidai ban yarda ba, ka faɗa min in da ka koya, dan Allah"



"So da yawa ina ganin yadda kuke girki kuma ina karanta yadda ake girki a Google "


"Daga yau kai zaki riƙa yi mana girki"



"Yadda kike so haka za'a yi, Mu 001"


"I really love you my love"


"I love you too, my 001"


Na ɗauko ta muka dawo farko na zaunar da ita na zuba mata abinci a plate na ajiye a gaban ta amma ta langwabar da kanta alamun a'a,


"Me kike so"


"A jikin ka nake so na zauna ka bani a baki"


Na riƙe mata hannu na zaunar da ita a kan cinya na , nacigaba da bata abinci a baki kamar yadda ya buƙata, ina bata nima ina ci.


Rayuwar gidan mu tayi matuƙar chanjawaz ana cikin haka ne ranar zuwa Yola ta zo, na faɗa mata zan tafi Yola ta kalle ni da fuskar tausayi.

"Allah ya kiyaye ye hanya, Allah ya dawo da ku lafiya"


Na jawo ta jikina na kwantar da kan ta nazo daidai kunnenta na raɗa mata 

"Ina son ki, kina da darajar da ba duk mace ce zata sameshi ba."


Da sauri ta ɗago kanta, ta goge ɗan hawayen da ya fara zuba daga idon ta, idon kyar a kanta, ganin ɗan samuwar da ta shiga sanadiyyar maganar da na faɗa mata, na sake sabon rarrashi, ban rabu da ita ba sai da na tabbatar ta kwantar da hankalinta.


Ta sake kallo na ta ce "Dan Allah ina roƙon wani Alfarma guda ɗaya"


"Wacce irin alfarma kike buƙata?


"Ina so idan ka tafi nake gud na kwana ɗaya"


"Babu damuwa na baki dama ki je" 


ta sake tsalle ta rungume ni, tayi ta sumbata na.


Mu haɗu a page 38 don jin yadda labarin zai cigaba.


Wadanda basu yi Following wannan page ɗin ba suyi domin samun littafai masu daɗi na marubuta daban-daban.

Kada a manta da.

Like, Comment and  share.

Post a Comment

Previous Post Next Post