🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON
BY
NARNAH KANWAR SOJA
( Sayeddan Addah )
💫Royal Star Association,💫
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya
ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara
basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
Page 5 & 6
Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin
posting kullum ba ,
mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya
show me some love guy's 🩷
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم
Haka abin ya faru da Sarki Numan haba ɗaya
mutanensa sun gaji da mulkinsa, wasu daga cikin mayaƙansa sun juya masa baya,
suka sayar da kansu ga mutanen Dursum, wanda suka sayi rabin mayaƙan domin
samun nasara a kansa.
"Kado,
ka kula da ‘yata. Ita kaɗai ce abin da na mallaka," inji Sarki
Numan, ya faɗa wannan karo fiye da goma.
"Eh, mai martaba, zan kareta da
raina," Kado ya sake amsawa cikin nutsuwa.
" Baba ka bar ni na tafi tare da
kai!" Princess Rahila ta faɗa cikin kuka, tana faɗawa jikin mahaifinta.
Ba ta son wani abu ya same shi ita fa ba komai ba ce idan ba tare da
mahaifinta ba.
“Je Kaɗo , tafi yanzu da ‘yar gadona. Ka
kiyaye ta kamar zinariya.” Sarki Numan ya faɗa da murya mai ƙarfi, irin ta
jarumai, sannan ya juyawa wajen baya yana barin gurin.
Princess Rahila ta sake gudowa ta rungume
mahaifinta daga baya da jin ɗumin hawayenta a bayansa, zuciyarsa ta raunana sai
dai ya ƙi juyawa saboda kar ta hango hawaye a idanunsa — alamar rauni ga jarumi
kamar shi.
Duk da haka, yana son Rahila ta ci gaba da
tunawa da shi a matsayin jarumin sarki, gwarzon da yaƙi bai faye shi ba, ba mai
zubar da hawaye saboda galaba ba.
Bayan wani lokaci, Rahila ta saki mahaifinta,
sannan ya tafi ba tare da ya waiwayo ba.
Baba Baba
Ka kalleni ko sau ɗaya,” Rahila ta faɗa tana fāɗowa kan gwiwowinta, amma
Sarki Numan bai waiwaya ba yana ƙoƙarin ɓoye hawayensa.“My princess, dole mu
tafi yanzu,” Kado ya faɗa yana ƙoƙarin tashi da ita, amma ta ture shi.“Kar ka
kuskura ka saka kazamin yatsunka a kaina!” ta faɗa cikin ƙiyayya.
(Duk da girman haɗari, girman kai na sarauta
ya mamaye ta.)
Kado bai ce uffan ba. ya saba da halayenta,
tun da shi ya horar da ita duk da haka, shi kansa bai tsira ba suka fice ta
wata sirriyar hanya da ba kowa ke san da ita ba, sai dai shi da Sarki Numan.
Yayinda Sarki Numan ya dawo fadar sa, sai ya
tarar da rabin masarautar an lalata ta. Mayaƙan Dursum sun riga sun mamaye
wajen.
Sarki Numan ya shiga ɗakin sirrin da ke ajiyar
makamai, ya sa tufafin yaƙi, ya ɗauki manyan takubba guda biyu zuciyarsa cike
da fushin jarumi, ya kuduri niyyar mutuwa a matsayin gwarzon sarki maimakon
guduwa kamar gwanin fargaba.
A lokacin yaƙi...
Yaƙin ya riga ya barke, sara suka hannu da
ƙafa. Sarki Numan ya fafata kamar zaki, yana yanke mayaƙa tamkar bishiyoyi
lokacin da ya hango Prince Dursum, tun da farko ya ɗauka Prince Tarhim ne, sai
dai da ya kalli fuskar, ya gane cewa uban ne — Sarki Mujus. Da haka ya soki
kansa ƙasa, alamar ƙarshen nasarar da yaƙin zai iya kawo masa.
Sarki Numan ya ci gaba da gwabzawa har sai da
zuciyarsa ta fara kasa dukan da kyau. Bugun zuciya ya rikice, zuciyarsa ta mutu
da ganin 'yarsa cikin halin ƙaskanci ya sulale ya fāɗi ƙasa, ya zubar da
makamai, hawaye na zuba daga idanunsa.
“Ba zai yiwu ba! wannan ba gaskiya ba ce!” ya
ƙwala ihu cikin azaba.
“… ku
bar ta ku kyaleta, ku bar ta haka kawai,” Sarki Numan ya roƙa yayin da aka jawo
Princess Rahila cikin sarka, tana kuka.
Jikinsa ya kasa tsayawa, ya durƙusa, yana
kallon Prince Tarhim yana ja da sarkar Rahila, har ta durƙusa ƙasa yana kai ta
gaban mahaifinta, yayin da wasu zaratan mayaƙa suka kewaye su yanda yake ganin
‘yarsa tamkar bayi, ya girgiza zuciyarsa sosai.
Princess Rahila ba komai ce a wannan lokaci ba
face bawa, jikinta da datti da ƙura, gashinta ya bazu.
“Ga ‘yarka, Sarki Numan babu sauran princess,
yanzu bayi ce a ƙarƙashin masarautar Zuma,” inji Prince Tarhim, ɗan Sarki Mujus
— jarumin da ya kashe dabbobi da suka kai hari garinsu, Zuma shekaru 27 ya
fafata yaƙe-yaƙe masu yawa.
Dogo ne, baƙi fari, da kyakkyawar fuska.
Fuskarsa da sunansa suna tayar da hankali, musamman ga mata.“Wannan ba zai faru
ba!” Sarki Numan ya ƙara faɗa.
“, ku bar mahaifina shi ne Sarki na Buga
Afirka,” Rahila ta faɗa cikin kuka.
Sarki Mujus ya fusata, ya jawo gashin kanta.
Rahila ta yi ihu cikin ciwo da azaba.
“Great king kike kira? kin san abin da
mahaifinki ya aikata wa mutanen masarautata?” inji Mujus.
Sarki Numan ya ce, “Kaɗo ne ya yi alkawarin
kare ki.”
“Baba Kaɗo ne ya ci amanar mu,” Rahila ta faɗa
cikin murya mai cike da raɗaɗi. Mahaifinta ya firgita.
“Kado? Amintaccena?”
“Eh, Baba ya ƙaddamar da komai.”
Kado ya bayyana yana faɗi, “Na tuna kuka na
iyayena da ‘yar’uwata lokacin da suka mutu a hannunka. kayi musu hukunci da
wuta saboda haraji na jure, na koya darasin rayuwa har na zama bawan da kake
amincewa da shi amma yau sai na ɗauki fansa ta, in ga yadda ‘yarka ke zama
bayi, kamar yadda ka mayar da ‘yan’uwanmu bayi.”Sarki Numan ya ƙara fashewa da
kuka, “Kado, me nayi maka har ka yi haka?”
“Zan bar ka da rai, Sarki Numan amma zan
tabbatar ka gani da idonka lokacin da ‘yarka ta fuskanci cin mutunci kamar
yadda wasu suka fuskanta.”
“Don Ubangiji… a kyale ta ku daina wannan,”
Sarki Numan ya ce yana ihu, yana ƙoƙarin miƙewa a lokacin ya sharɓi wuka daga
hannun wani mayaƙi.
...ya sharɓi wuka daga hannun wani mayaƙi, ya
sharɓa a cikinsa da ƙarfi, jini ya fara malala daga bakinsa, yana kallon ‘yarsa
da ƙyalli na ƙarshe a idanunsa.
“Rahila…” ya furta cikin muryar da ta dushe.
“Babaaaa” ta ƙwala ihu da karfi, tana ƙoƙarin
tashi daga kan guiwowinta, amma ankai mata dukan da ta sume nan take.
Kafin idon
Sarki Numan ya faɗi ƙasa shikake, ya rasa numfashi daga nan, aka ɗaukaka
tutar Zuma a saman fadar Buga Afirka aka kama bayi da mata da yara, aka raba
su. Masarautar Buga Afirka ta faɗi ƙasa, ta koma cikin tarihin da ake karantawa
da ba’a taɓa tsammani ba.
"Father please don't dîe. Please don't...
don't, I beg you! Somebody please help me. Please save my father."
Princess Rahila tana roƙon mayaƙansu
"Save your... breath.. my jewel,
take...take...care of yourself. I love you my baby rahila ke tuna ke sarauniya
ce juye duk abinda kekeso da zaran kin samu dama " King Numan aya faɗa
wanan shine sautin sa na ƙarshe ,
"Father please, please stay with me
please don't leave me." p rincess Rahila
ta faɗa cikin ƙunar zuciya tana daman jan tokobin daga cikin sa sai da
tasha wuya kasancewar hannunta da Chain
"Father please don't leave me.
"Father no...you can't do this to me, you
can't leave me here all alone!" Princess Rahila ta f
ad'a da ƙarfi wanda gabaɗaya ta razana gun da
ihun ta ta ɗaga tokobin sama tana kallon
yanda jinin mahaifin ta yaki wanzu akai , ta saita dai dai cikin ta da wuƙar ,
"let me go you ....Let me go
right now, ka bani tokobi na zan kashe kaina na huta Princess Rahila ta faɗa tana ihu lokacin da Prince Tarhim ya
ƙwace makamin hannun ta ,
"Tarhim ka barta ta mutu duk da haka uban ta baya nan da zaiga kalan
hukunci da zan mata let her kill her safe and go , Shashasan ya kashe kansa already don haka ita
ma barta ta kashi kankara kowa ya huta useless girl I do not care anymore"
."Father, do you think it will be okay for us da zamuga tana kashe
kanta " ya tambaya ciki da sonjin amsa daga mahaifin nasa" ƙwarai da
gaske wannan shine tabbatar da cewa mun gama samun nasara a wannan yaƙin....
"Keep quiet, shut up you son of bitch , don't talk to my father like
that!" Prince Tarhim ya faɗa yana tunkuɗe ta daga kusa dashi
Wanan yayi dai dai da zartar War tokobin king
Mujse saitin kanta sanadin bangaja da ta sama tayi ƙasa tokobin ta kwace wa
kanta
cikin
haushe da takaice rashin samun ta raised up his sword again after yayi rashi
nasara daga farko da zumar filli kanta charraf Prince Tarhim ya kama hanun sa
kafin tokobi sa yakai head of princess Rahila " father u don't have to do
this akaiw hanyoyi da dama da zamuyi amfani akanta
"What is wrong with you son? shin kaman ta yanda Uban ta ya kashe ɗan uwan
ka ?" king Mujse ya faɗa cikin kaɗuwa da mararrin jiki .
The
king Mujse Taki yaji komai ya zama sabo
burin sa kawai kashe ta ko zai rufe wanan chapter daya jima yana mafarkin samun
nasara akan sa.
Prince Bella firstboy na king Mujse wanda ya
bashi matsayi prince yana da mata Princess Afrah wanda suki zauna lafiya sun
haifi yarinya ɗaya Aflim tana da wata biyar Prince Bella ya haɗu da mummunar
ƙaddarar sa da ta janyo baƙin cikin da tsananin ɗaukar fansa na king Mujse..
King Mujse ya aika Prince Bella zuwa meeting to wanda za'ayi a
birnin Kursum inda manya manyan sarakai zasu haɗu su tattauna to solve a issues
affecting their kingdom prince Bella
Jauro got dressed and said goodbye to his family. inda suka rabo d kyar ta
hanyar kukan baby Aflim king Mujse ya amsheta da rarrashin ta yana cewa shi
bazai samu zuwa ba duk da cewa yaron sa yana. tareda da sabon baby babu but ya
hallarchi taron kasancewar shine next of the king .
Shin a hakane zaka jagoranci kujerar mulki
idan bana nan ? zaka ajiye duty saboda
akan kukan baby ?! a lokacin da
ya hangi tsantsan tausayi baby Aflim da mutuwar jikin Prince Bella ,
"Her mother is here and your mother is
here too. We are all here to take care of her so please, you must leave at once
son." King Mujse ya maimaita maganar cikin ƙwarin guiwa da yaki bawa
Prince Bella ,They didn't know that it was the last hug and last goodbye.
Duk sarakuna sun kammala haɗuwa a inda Aki
jiran king Numan wanda ya ƙaraso da dukkan tawagarsa cikin isa da mulki da
kaddara dukkan su suka miƙi tsaye wasunsu har ɓoya bayan wasunsu suki ,
kasancewar sa Jarumin jarumai da babo mai ƙarfin ikon sa a wannan nahiyar ,
Duk
abinda yake faruwa Prince Billa ya
chigaba da zama ba tareda ko kallon sa yayi ba
In one-time ba zato ba tsammani ya zaro
tokobin sa ya sara kansa taki y rabi gida biyu sai jini da ya wantsala umarni
ya bawa Slave's nasa da susa kansa cikin akushi su ƙona ganganr jikin sa da
wuta a idon duniya su
" ku ɗauki tokan ganganr jikin sa kukai
ga uban sa ku sanar masa dukkan abinda yafaru ya sanarwa ɗaya daga cikin
dakarun da suka sa prince Bella rakiya inda yayi arrest na sauran suka zama
Slave's nasa .
A lokacin da King Mujse yaji wanan Labarin
sosai ya razana inda queen Afra ta. kamu da heart Attack a wanan time Prince
Tarhim ya chigaba dajan ragamar shugabancin Dursum
After
sometime soon king Mujse ya warke yafara plan tareda mutanen sa plan to their
revenge hakan ya faru sukayi nasara ganin ga king Numan kwance a cikin jini a
masaurautar sa king Mujse yana shirrin Kashi Princess Rahila prince Tarhim ya
dakatar dashi .....
BACK TO STORY
"Father, wanan shegiyar yarinyar can't
dîe just like that. I have a better plan for her ." Prince Tarhim ciki da
tsananin fushi da fusata King Mujse baxai iya jira ba yaji wanan plan nin ba
King Numan already dead but still bazai iya yafe mishi akan kashe ɗan sa ba
dole sai ya kashe ta zai samu sallama He
would do anything to complete his revenge mîssion
"Father, you will be helping her if you
kîll her now. a rashin sani uban ta ya tsira daga punishment za muka shirya
masa taya zamu barta itama jikinta ya tafe a banza Rahila dole ta biya bashin da ubanta yaci akanmu
mu barta har sai ta roqe mutuwa da kanta da muguwar azabar dazamu ɗanɗana mata
let's kill her slowly
Kanta ta ɗaga sama tana kallon sa da idannunta
da suki wanzuwar da jini a kowani tsako daki da jijjiya a. ƙwayar idon
"son of bithch kill me now you have only one change kar kabari wanan damar
ta wucce ka Tarhim because jaine mutum na farko da zan fara kashewa idan ka
barni a raye da Rayuwa ta
"I shall kîll you all one by one. gabaɗaya
ku sai kun ɗanɗane zumar kaɗai na mutuwar ku a tafkin hannuna i sweer with my
beloved father ." "I, the
princess of Buga Afirican promise you
all today. sai na kawo ƙarshen ƙasar Dursum ta durgusa a kan guiwarta sai na sa
kun tsani kanku ta faɗa with her fire eye's
bata damu da zaratan mazajen da suki kewaye da ita ba burinta kawai suyi
zuciya su kashe ta ko zata huta da wanan bak'ar rana da ko. mafarki batayi
tunanin kasancewar sa ba ..
"Son, did you hear that?
jinin Numan yana kewaye da ita she is devil too kill her rayuwarta
tamkar na uban ta ne" , dogon tsaki yaja Prince Tarhim ya kasa fahimtar
meyasa ta kasance very hot stubborn duk da cewa tana ganin tana daga da
mutuwa even in the face of dànger.
"Father, I know how to handle people like
her."
"One day, you will beg for my
mercy." Prince Tarhim ya faɗa yana matso da hannun sa akan fuskar ta
matsar da fuskar ta tayi da tofa masayawun da ya haɗa jini in his face dariya
ya kicce dashi yawa hannu ya gogge yana dungule hannu yakai mata wani mugun
nashi da saida ya fasa mata kefin bakin ta
King Mujes daya amince da yaron sa ya yanke
hukuncin ya barta ta kasance matsayin
baiwar su ,it felt like a dream to Rahila batasan da cewa watarana wanda
yaki chan sama duk matsayin da mulkin sa ko ƙaddara sa da dukiyarsa watarana
zai faɗo ƙasa warwas ba kaman ƙitfawar ido
King Mujse later cût off king's Numan head from his body. ya ƙona ganganr jikin sanan ya umurce dukan
bayin sa suyi wasan harbil harbil da kansa a sansanin masarautar buga Afirican the most powerful king of Buga
Afirican bazai iya aikata komai ba kasancewar yau da kansa ki wasa a sansanin
masarautar da idon dubanne mutane da bai ɗauki su a bakin komai ba yaki
wulakanta su sa kiran su baye marasa amfani sai gashi shine yau a wannan
matakin
All that happened front of Princess rahila
wacce taki kuka ta tana rogon sa da
yadaina azabtar da kan mahaifin ta sai dai kash hakan ƙarawa king Mujse ƙarfin
guiwa yakiye da azama
Har abada zaki yafi ƙarfin ayi wasa a gaban
shi har akai masa raini ko suka sai dai idan ya kasance mattace har yaro zai
iya matsowa don yayi wasa dashi hakan ta kasance kansa ya zama abin nunawa da
dariya ga muradun buga Afirican .
Cikin
Chain a maƙale da wuya ta da hannun ta da ƙafarta Prince Tarhim yana kan dokin
sa yana janta cikin ƙunchi suka kama hanyar Dursum ana ball da kan mahaifin ta
wanan abin yafi mata muni akan yanda mutanen buga Afirican suki kallon ta a
wulaƙanchi even when she asked water sai dai tasha ruwan hawaye ta wanda suki
zuba layi layi tsananin tsana da ɓaci rai da mugunta daban daban taki saƙawa
prince Tarhim tabbas indai ta ƙungiya shine mutum na farko da zata kai lahira
kasancewar bata da wani babban maƙiyi sama dashi ......
Princess Rahila batayi tsammanin isowar Dursum
zai kasance sillar tsayawar hawayen ta sakamakon ganin cincirindon al'ummar
garin sun fito kansu da ƙwarƙwartansu suna watsa mata duwatsu wasu kuma tumatur
da takalma lallai ta sami tarbar na musamman haushi mulkin ubanta da nata taki
amsar hukuncin daga gari su
Numfashi ta ne ya tsaya chakk lokacin da aka
harba wani talkami ya sauka akan fuskar ta tunawa da cewa idan ace yau yana
raye babo wanda ya isa ya ɗaga mata ɗan yatsa a gaban ta
Taki ta yanke jiki sunammaya inda yayi dai dai
da isowar su wani bakin ɗaki su dark and hurt prince Tarhim ya tsuma ta da
umarnin kawo ruwan mai ɗumi aka watsa mata taki ta dawo daga suma ta cikin.
azaba ta ƙwala ƙara tunda taki for the first time taga irrin wannan duhu duk da
cewa takan iya azabtar dawasu a irrin sa
batayi tunanin kasancewar haka a garita ba .
NARNAH ƘANWAR SOJA 🖋️💞💝💝