Tsantsar Kauna
Page 36
Written by Tahir Yusuf
Fatima ta raka Khairat har bakin ƙofa sukayi Sallama, ta dawo cikin gida, ta ɗora abincin dare dama already tayi parboiling na shinkafa, ta gama miya.
Ƙarar buɗe gare ne da akayi yasa ta leƙa ta window, Kamal ne riƙe da Leda a dukkan hannayensa, ya nufi kofar dalibai shiga cikin gida, a hankali Fatima ta fito daga kitchen na dawo falo kafin ya shigo, tayi min sannu da zuwa ta karbi ledar dake hannuna ta shigar dashi kitchen ta ajiye ta dawo.
Cikin ɗaki ta same Ni ina ƙoƙarin canja kaya, ta zauna a gefen gado tana Kallona, har na gama sauya kaya daga manya zuwa ƙanana farin riga da baƙin wando jeans.
"Kamal ɗan Allah idan ka ci abinci zamuyi magana"
"To Fatima, Nima dama akwai maganar da nake so zamuyi, yanzu dai bari nayi sallah na dawo, sai muyi"
"Sai ka dawo"
Na shiga nan ɗaki nayi alwala na fita zuwa Masallaci. Ba ɗauki wani lokaci ba akayi sallah wanda lokacin Sallar Magriba bata da tsawo sosai, kamar zan fita na tafi gida zai dai na zauna ina jin wani karatu da ake yi a masallacin kan zamantakewar aure.
Malamin yayi magana akan adalci ga masu mata fiye da ɗaya da kuma kyautatawa ga matar da kake aure koda kuwa guda ɗaya ce. Karatun zai amfane Ni sosai musamman akan adalci tsakanin mata guda biyu ko fiye da haka. Hakan yasa na zauna har lokacin Sallar Isha'i yayi mukayi Sallah na koma gida.
Affan ne ke kula sosai tunanina wani abu akayi masa, ashe Sallah Fatima ke yi daidai lokacin shi kuma ya tashi daga bacci, a lokacin yana gab da yaye domin ya shiga wata na 19, yana ganina ya zo da gudu ya rungume Ni, na ɗauke shi.
Fatima ta isar da Sallah, har lokacin fuskar ta ba wani fara'a sosai, daurewa kawai takeyi.
Tare muka fita zuwa falo, Fatima ta zuba ma kowa abinci muka ci, babban abinda ke burge Ni da Fatima, gaskiya ta iya girki. Ta lalle da ce
"Baban Affan dan Allah kayi haƙuri da abinda ya faru kwana biyun nan, na kasa daurewa na, amma kayi haƙuri.
"Fatima babu komai kece yakamata na baki haƙuri"
"Maganar aure kuma bani da ikon hana ka, abinda zan ce kawai shine kaji tsoron Allah, kada kayi aure ka wulaƙanta Ni, ko matar ka ta sa ka canja min, ka ji tsoron Allah, ka zama mai adalci a tsakanin mu na matan ka, kada ka banbanta tsakanin mu ta hanyar fifita ɗaya ko makamancin haka"
"Fatima nayi Miki alƙawari in Sha Allah zaki same Ni mai adalci a tsakanin ki, bazan bambance kowa a cikin ku ba, to amma ki sani zuciya tana son wanda ke kyautata mata, ko da kuwa cikin 'ya'yan da mutum ya haifa ne."
"Zan kyautata maka, sanyi duk abinda kakeso, zan bar duk wani abinda baka so.
"Fatima ina ƙara baki haƙuri a karo na biyu, in Sha Allah zan kula daku fiye da yadda kuke tunani, ina ƙaunarki sosai Fatima na, Yakamata ki ɗanyi dariya mana"
Fatima ta ɗanyi Murmushin da be kai ciki ba, ya kalleta ya ƙara kallo
"Fatima wannan dariyar naki bai kai ciki ba a baki kawai kikeyi"
Tsam Fatima ta tashi ta shiga cikin daki lokacin sun gama cin abinci, Affan kuwa tun yana wasa har yayi bacci.
Nayi ta rashin Fatima na sai da na tabbatar da tayi dariya sosai samuwar da ke fuskanta ya ragu sosai sannan na iya yin bacci.
Wadanda basu yi Following wannan page ɗin ba suyi domin samun littafai masu daɗi na marubuta daban-daban.
Kada a manta da.
Like, Comment and share.