RANDAR CIKIN ƊAKA...
©UMMU AFFAN
Page 11-12
Ƙarar zazzafan marin da ya sharara mata ne ya fargar da ni ina hannunsa. Da sauri na matsa tuni hawaye suka wanke a fuskata ya yin da jikina ke rawa, haƙorana har wani sautin ƙara suke saki. Sakamakon sabon zazzaɓin da ya saukar mini da rawar ɗarin da ta rufe ni lokaci ƙanƙani. Jagab na zauna saman kujera ina sauke numfashin wahala, Amal kuwa kuka take tan-tan ƙarfinta.
"Yanzu saboda wannan mai farar ƙafar ka ke marina? Da farar ƙafarta bata kassara ɗan uwanka ba da yanzu shine gaba-gaba a neman lafiyarta, amma ya barka da aiki shine har kaji haushi don na faɗi gaskiya?"
Girgiza kai ya yi, da alamar cike yake da takaici ya ce,
"Nihlah ƙanwata ce da ta ke da haƙƙin na nema mata lafiya ko da bata auren Md. Ko kin manta ne?"
"Ban manta ba ina sane, amma sanin nawa ba zai hana naji kishi da haushin kai zaka kaita asibiti ba. Idan har da gaske ne me zai sa ni bazaka ce na kai ta ba?"
"Saboda nasan idan duka duniyar nan da abin da ke cikinta zan mallaka miki, to bazaki kai ta ba."
Hannuna ya kama muka doshi hanyar fita. Amal ta biyo mu tana ta surutai, bai kuma kulata ba kamar yadda nima nake biye da shi duk inda ya jefa sawunsa na jefa nawa.
Har muka shiga motarsa ya ta da motar Amal bata daina tujara ba, haka muka muce muka barta ita ce har ƙofar gida ina hangenta ta madubin motar.
Muna barin layin ya fara tafiya a hankali, jingina nayi da kujerar da nake zaune ina sakin numfashi, ƙirjina har wani sauti yake ba da wa. Ɗal! Ɗal!!
"Kiyi haƙuri Nihlah komi lokaci ne." Hawayen da na samu sassaucin zubarsu ne suka kuma wanke fuskata yanzu. Muryata har rawa take gurin furta, "Yah Mz don Allah me zanyi da zai yi silar dawo da martaba ta arziƙin Yah Md? Duk abin da ya faru ba a son raina ba ne, hasalima ban san me yasa hakan ke faruwa ba, kuma wai duk a silana." Na fashe da kuka mai sauti zuciyata ta karaya.
Dubana ya yi idanuwansa jawul, kafin ya mayar da hankali ga tuƙi ya ce, "Jarabawa ce Nihlah, ki ɗaure ki cinye jarabawarki tabbas sakamakonki na gurin sarki Allah."
Jinjina kai nayi, cike da yarda da maganarsa, sai dai a zuciyata ina addu'ar Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar tawa. Domin nayi tawakkali cewa Allah bai ɗaurawa bawansa abin da yafi ƙarfinsa, sai dai idan shi bawan ne ya ɗaurawa kansa.
Mun isa asibiti, likita ya duba ni ya ce shawara ke damuna kuma ina buƙatar ƙarin ruwa, bai musa ba ya ce a saka mini. Gado suka ba ni a sami zuwa dare mu koma gida cewar likitan, kasancewar Dr Anas abokin Yaya Mz ne. Bayan an ɗaura mini ruwa, zama ya yi saman kujerar masu jinya yana danna waya. Ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.
Ɗago kan shi ya yi tare da zuba mata da mujiyarsa. 'Nihlah' Ya ambaci sunanta a zuciyarsa kafin ya sa hannu ya share siraran hawayen da suka sakko mishi, girgiza kai ya yi tare da sakin murmushi kuka da murmushi a lokaci guda.
Wajejen ƙarfe biyar ƙarfe biyar na yamma na farko daga barcin, babu laifi naji jikina ya mini daɗi sosai sai dai rashin ƙarfin jikin, nayi mamaki matuƙa ganin Yah Mz zaune har lokacin a gurin.
"Sannu!"
Ya furta cikin natsuwa bayan ya ɗago daga kan wayarsa yana kallona, "Yawwa!" Na amsa muryata a sanyaye.
Ajiye wayar naga ya yi gefen gadon da nake, ya jawo take away a leda ya buɗe mini tare da ajiye kusa da ni, ya buɗe gorar ruwa ya miƙa mini.
"Da na fita salla na saya miki, nasan kina jin yunwa yanzu."
Gyaɗa kai nayi alamar "Eh" Sannan na buɗe baki a hankali.
"Sai dai ina so na zagaya banɗaki."
"Ok!"
Ya furta tare da taimaka mini na sauka, har ƙofar toilet ya rakani, ko da na shiga fitsari nayi tare da tsarki ganin da ruwan zafi sai nayi wanka na mayar da kayan jikina tare da ɗaura alwala, ina fitowa na gabatar da sallar azhar da la'asar da ta wuce ni, sannan na fara jin abincin, don naji ƙarfin jikina sakamakon wankan da nayi.
Ina cin abinci Yah Md ya yi sallama tare da Amal, dukanmu muka amsa,
"Ya jikin naki?"
Ya tambaye ni bayan ya zauna kujerar da Mz ya tashi ya ba shi, shi kuma ya zauna bakin gadon da na tashi.
"Da sauƙi."
Na furta ina kallon Amal da ke hararata, ko sallama bata yi ba, sai kallon banza da take mini. Abincina naci gaba da ci nima ban kulata ba, ina ji tana tambayar Yah Mz wai tunda ya kawo ni yana nan, banza ya ba wa ajiyarta ba tare da ya kula ta ba.
Ina kammala cin abincin, Yah Mz ya ce zamu iya tafiya gida tunda daman likita ya ce idan ruwan ya ƙare zamu wuce. Yah Md ya ɗauki ledar maganin da aka saya mini, ya yi gaba sai Yah Mz ne ya ce mini, "Ta so mu tafi."
Amal taja wani dogon tsaki ta fita. Nima a hankali na miƙe nabi bayansu.
Har muka isa gida ba wanda ya yi magana, bayan Amal da lokaci-zuwa-lokaci take jan tsaki.
"Na gode Yaya Muzzamil Allah ya saka da alkhairi, ya bar zuminci."
Abin da na furta kenan muna isa parlour. Murmushi kawai ya yi, ya bi bayan Amal wacce har ta shige ɗakinta tuni. Sauke ajiyar zuciya nayi nima nabi bayan Yaya Md. Akan mirror na iske ya ajiye magungunan, ya zauna bakin gado. Jiki a sanyaye na ƙarasa.
"Kayi haƙuri Yaya daman..."
Maganata ta katse sakamokon tsawar da ya daka mini, nan take jikina ya kama rawa nayi ƙasa da kaina hawaye har sun tarar mini.
"Ban tambaye ki komi ba, abin naki ya wuce kan mazan waje ya shugo har akan Muzzamil, idan ma kin yi akan nashi ai ba sabon abu ba ne!"
Tuni hawayena suka tsinke, cikin tsananin tashin hankali na ɗago fuskata, gabaɗaya namujiyata suka zube akan fuskarsa ta take ɗaure, kamar magribar ɗinya.
"Yaya Md daman zargina kake duk bayan abubuwan da ka ke mini a tarayyarmu? Tabbas biri ya yi kama da mutum yanzu har ka zarge ni da Yaya Muzammil bayan kai da kanka ka ba shi izinin ya kaini asibiti?"
"Kiranki a waya nayi na sanar miki?"
Ya yi saurin tarar numfashina, mamakina ya kasa sauka,
"Amma ce mana ya yi kai ka ba shi izinin ya kaini asibiti?"
"Nihlah yaushe raini ya fara shiga tsakaninmu, har ina tambayarki kina tambayata? Wallahi na gaji da wannan halayyar taki, Allah dai ya kai damo ga harawa lokacin da zan sami sauƙi."
Murmushin takaici nayi domin na gane nufinsa wai lokacin da zai sauwaƙe mini. Ban kuma kula shi ba na faɗa toilet ba don ina buƙatar hakan ba, sai domin ina so zuciyata ta sami sauƙi. Jingina nayi da bangon toilet ɗin ina kuka a hankali, wannan wacce irin jarabawa ce. A gidan mahaifina ba sauƙi haka a gidan mijin, na daɗe ina addu'ar samun sassauci a gidan miji, ban yi fatan samun miji tamkar mahaifina ba. Sai dai ba a rabu da bukar ba ne aka haifi Habubakar. A hankali na zame ƙasa kukana na som tsananta ina daddanne shi. Na ɗauki kusan rabin awa a toilet, ko da na fito ban iske Yaya a ɗakin ba. Nayi tunanin haka dama saboda yau ba gidana yake da kwana ba.
Wayata na ɗauke kiran Adyaan na tadda guda sha biyar, ban bi takan layinsa ba na gwada kiran Mamana, sai dai baturiyar nan ta sanar da ni wayar a kashe take, daman nayi tunanin hakan tunda tun ina gida Babana ya amshe wayarta.
A hankali na zame na kwanta ina tunanin rayuwa da irin halin da na taso a gidanmu. Babana sunansa Musa Inuwa matansa biyu ne Ɗahare wato Umma da kuma Huwaila wato Mamana. Umma ce uwargida mai yara uku duka mata, Zainab ce babba sai Lawisa Sannan Amal. Mamana kuwa ni kaɗaice kasancewar da ta sami ciki yake zubewa nawa ma da ƙyar ya zauna da taimakon Allah. Nima Allah ya yi rayayya ce da tuni na bar duniyar, domin wuya da azaba babu wacce ban shata ba a hannun Umma. Mahaifina kuwa Babanmu daman mijin ta ce ne Umma daman ta riga ta shanye sa sai abin da ta ce. Hatta Kakata mahaifiyar Baba ta tsane mu, sakamokon sam bata ƙaunar Mamana silar ta fito daga yaran Nufawa Mamana Banifiya ce, Kakata kuwa ta ce dangin mayu ne hakan yasa ta ɗauki bakar tsana ta ɗaurawa Huwaila domin Babana ne ya nace sai ya aureta sai take ganin ta lashe mishi kurwa ne hakan yasa tsanar da takewa Mamana ta shafe ni, bayan hakan kuma kwatsam sai samun mahaifina ya ɗauke tun bayan shugowar Mamana, ada kam ba laifi ya fara taka sawun yayansa, sai dai tana shugowa kamar anyi ruwa an ɗauke. Wannan farar ƙafa da ta shugo da shi kamar yadda Hausawa ke cewa ya ƙarara rura tsanarta a zuciyar Hajiya Rabi kakarmu da duk dangin mahaifina. sam bata ƙaunata ko wasa taga inayi tun ina ƙarama idan ta daka mini muguwar tsawa sai na furgita. Hakan yasa na taso da mugun tsoronta. Yara biyu Kakata ta haifa Muhammadu Babansu Yaya Md sai mahaifina Musa ita ta raine su tun suna ƙananu domin tun a lokacin mahaifinsu ya rasu, ɗawainiyarsu da rayuwar karatunsu duk ita ce. Allah ya ɗaga Muhammad da arziƙi tun tasowarsa Allah ya huwace ma shi, shi yaci gaba da kula da Babana da mahaifiyarsu, domin akwai tazara ta kusan shekaru goma a tsakaninsu. Shima matansa biyu mahaifiyarsu Yah Md ita ce uwar gida wato Amma haka suke kiranta sai Inna. Amma yaranta huɗu Ibrahim ne babba sai 'yan biyun Mudassir da Muzzamil sannan ƙaninsu Lamir. Inna kuwa yaranta biyu Suraiya da Azima, ita kanta Inna bata da ƙyirki duk wani tuggu da makirci tare suke haɗa shi da Umma. Suraiya ce sa'armu duk cikin yaran ɓangaren domin ko Lamir ya girme mu sosai, sa'an Zainab ne babbar yayarmu...
Hawayen da ke zuraro mini na goge duk da sunƙi tsayuwa, duk na jiƙa fillon da nake kwance a kai. Ganin tunane-tunane ba za su barni ba, tashi nayi na ɗauki ruwa nasha magani na sannan naje na ɗauro alwala, salla nayi lokacin takwas na dare har ta gota, bana jin zan iya cin wani abu, hakan yasa na koma na kwanta ko hijabin jikina kasa cirewa nayi, rumtse idanuwana nayi da ƙarfi ina fatan bacci ya kwashe ni ko zuciyata zatayi sanyi, wayata naji ta fara ɓurari, har na tsorata da sauri na jawota idanuwana a runtse na kara wayar a kunnena ban ce ƙala ba.
"Nihlah fatan kina lafiya?"
Muryar Adyaan ta ratsa na'urar saurarena, babu shiri na buɗe idanuwana tare da tashi zaune. zuciyata idan ban da lugude babu abin da take, me zai sa ya dinga kirana ina matsayin matar aure? Ga shi har Yaya Md ya fara zargina ko ince ma yana zargina da kula maza a waje. 'To ko dai yasan Adyaan yana kira na ne?'
Wani ɓangare na shashin zuciyata ya tambaye ni, da sauri na dafe girji inajin kamar zuciyata zata fasa ƙirjina ta faso, idan kuwa har tunani na ya zama gaskiya na tafka kuren da ba ni da wata mafita a cikinsa.
"Nihla kina tare da ni kuwa?"
Maganarsa ta zo mini a bazata don har ƙaramar furgita nayi tsabar ruɗewa ban san lokacin da bakina ya furta.
"Wallahi ba gaskiya ba ne Yaya Md....
08104335144
Masu buƙatar littafin za suyi magana ta lambar da ke sama ko a tura kuɗi kai tsaye 500 ta 8104335144 Opay wallet Fatima Rabiu Sunusi sai a tura shaidar biya ta 08104335144 na gode.
#Nihlatulkhair
#YahMd
#YahMz
#Adyaan
#Amal
#Farrah
#UmmuAffan
#RandarCikinƊakaa