Tsantsar Kauna
Page 35
Written by Tahir Yusuf
Haka dai suka cigaba da rarrashin Fatima da fahimtar da ita ba komai ne ake samu a ko wani lokaci ba, duk wanda Allah ya Jarabta to lallai ana son gwada karfin imaninsa ne.
Fatima dai babu abinda take yi sai kuka Malam Abubakar ya fita ya barsu da mahaifiyarta, itama nan ltayi ta rarrashinta tare da jan hankalinta da sake fahimtar da ita namiji an bashi damar auran mata guda hudu in har zai iya yin adalci a tsakanin matayen sa.
Fatima ta koma gida amma ko sallama bata yi ba dakinta kawai daidai lokacin kuma Affan ya tashi ni kuma ina ofalo ina zauna na zura ma sarautar Allah ido.
Na tashi na bi bayan ta don na sake bata hakuri sannan na fahimtar da ita manufar wannan karin aure amma ko da na fara mata magana daga min hannu tayi alamun bata son yin min magana.
har wannan lokacin Fatima aikin kuka kawai take yi, da kyar ta iya tashi tayi ma Affan wanka ta bashi abinci ya ci ita kuwa ko abincin ma in ba dole ba bata son kallon shi.
Nayi wanka na fita dama Abdullahi na jira na akwai inda zamu tafi tare dashi maganar wasu motoci da aka kawp zamu ltafi mu gani, na shiga don yi mata sallama da fada mata na fita amma ko kallo ban isheta ba, na dauka key din mota na na fita.
"Abdullahi, Tun daga jiya da na sanar da Fatima zan kara aure ta ta daina mun magana dazu fa har gidan su ta tafi amma bata dade ba sai gata ta dawo"
"Mata kenan, yanzu duk irin soyayyar da kuke yi ta canja akan zaka kara aure? Tab, kace akwai drama idan nima nace zan kara aure, kila ma ni sai ta nemi muyi fada."
"Amma in sha Allah zata sauko ina jira zuwa dare ne kila lokacin lta sauko sai na fahimtar da ita."
Abdullahi ya fashe da dariyar keta
Na kalle shi da mamaki na ce "Kai ana magana mai muhimmanci amma kana kawo wasa a ciki, amma babu komai zan rama, ko kuma na fada ma Matarka zaka kara aure muga yadda kai ma zakayi"
Abdullahi ya sake fashewa da dariya a karo nabiyu inda ya kalle ni ya ce "A'a Kamal ka rufa min asiri, don wallahi idan ka fada wannan maganar kila yau sai dai na nemi wajen kwana amma ba dai wannan gidan ba."
"To yanzu menene abinyi, kuma ga maganar mu ta zuwa yola ga maganar saka rana"
"Maganar zuwa Yola wannan ka bari sai sati mai zuwa sai mu tafi, Maganar fatima kuwa wannan matarka ce ahankali zaka bita kasan tsakanin mata da miji sai Allah."
"To ai taki kula ni ne sai kuka kawai takeyi, ko fitowa ta da nayi bata ci komai ba daki ma ta shige ko kallona na lura bata son yi"
"hmmm! wannan duk ba wani abu bane, da Yardar Allah zata dawo kamar batayi wannan abinba, mai wuyar ta fahimce ka kawai."
"To zuwa yaushe zata fahimce ni, Wallahi tsoro ta fara bani, domin irin labaran da nake ji a kafan sada zumunta kaji ance mata ta kashe mijinta ko tayi masa wani abu na cutarwa don zai kara aure."
"Haba ka daina wannan maganar Fatima tana da hankali da ilimin da bazata iya aikata irin wanna ba."
"Yadda na ganta ne kawai jiya zuwa yau"
"Kawai ka kwantar da hankalinka ka dage da addu'a da kwantar mata da hankali har ta sauko daga fushin da takeyi."
"Gaskiya da nayi farin ciki kuwa, Allah yasa ta sauko da wuri."
"Amin"
Maryam kuwa kullum farin cikin ta ƙaruwa yake yi sakamakon irin kulawar da take samu tare da kalamai masu ratsa jiki a wajen Kamal, hakan ya ƙara mata natsuwa da kwanciyar hankali sosai wanda ko a makaranta yanayin ta ya canja, daga ka ganta kasan bata da wani damuwa sosai sai dai wanda ba'a radawa, ta ƙara kyau tayi ƙiba sakamakon kwanciyar hankalin da ta samu.
Kwana huɗu da faɗa ma Fatima maganar ƙara aure amma ta rame tayi abinci mai ba sosai take ci ba sama diyyar samuwar da ya saka ma kanta.
Khairat ce ta shiga tana ta Sallaama amma bata amsa ba har sai da ta taɓa ta sannan ta mota, "Fatima lafiya kuwa, kin ga yadda kika yi kuwa kamar wacce tayi watanni tana ciwo"
"Hmmm! Khairat Ina cikin damuwa sosai"
"Fatima me ya faru?"
Khairat wai aure Kamal zai ƙara"
"Fatima aure zai ƙara shine zaki shiga irin wannan samuwar, ba da a jikin ki ko a ɗakin ki zata zauna ba, haba Fatima, gaskiya kin bani mamaki"
"Mamaki kuma Khairat?"
"Eh mana kin ga idan kin kashe kan ki ta sami gida a sama kun gina rayuwar ku a tare tun bashi da shi amma wai yanzu don zai ƙara aure shine kike irin wannan shashancin. Fatima bari ki ji Ni Wallahi gaskiya Zan faɗa Miki sai dai kuyi haƙuri kin san wacece Ni tun da daɗewa bazan ɓoye Miki ba ki kwantar da hankalinka, ki ƙwaci gidan ki da kanki, idan kikeyi wasa kina ji kina gani zaki zama sabuwar ware a cikin gidan ki wata banza can ta sami miji a sama.
Kin daina kula shi baki ƙoshi magana mai daɗi abinci mai idan kin daga sai dai ki kai masa ki tashi a wajen, kin daina taraiyar shi, to wannan shine kuskuren ki na farko, saboda kin bata dama ta shaƙu dashi, kina can kina fushi zaki kashe kan ki su kuma suna nan suna soyayya.
Abu na biyu, Fatima ki dage wajen kula da mijin ki, ki ƙara akan wanda kikeyi da, ki kasance ko da yaushe idan yana gida kina tare dashi da shagwaɓar ki da komai, kina da kuɗi ki sake siyan kananan kaya wanda zaki riƙa sakawa idan yana gida, duk abinda yake so ki masa.
Abu na uku, Fatima idan Allah yasa anyi wannan aure Dan Allah ki da wasa kada ki yarda ku nuna baki don wannan auren, ki ha ta a jiki sannan kuma ki kama girma ki, kada ki bari ta raina ki kada kuma kuyi wani abu da zai Miki faɗa a gaban ta domin hakan shima ya jawo raini.
A bu na karshe, Fatima kiji tsoron Allah a duk abinda zakiyi, ki miƙa komai namu wajen Allah ki dage kuma wajen gyara gidan ki, kada ki wasa da tsafta ko kaɗan ne kuwa, kin ga magana mai daɗi shima kada ki wasa dashi. Nasan kishiya babu daɗi amma dan Allah ki ɗauki wannan a matsayin jarabawa ce daga Allah. Wannan shine shawarar da zan iya baki matsayin ki na ƙawata ta amana."
"Babu komai Khairat in sha Allah zanyi amfani da shawararki wajen ganin na kwari gidana ba tare da boka ko Malam ba."
"Shikenan, idan kuma kina neman wata shawarar ki kira Ni idan ma ta kama na zo in sha Allah zan zo"
"Nagode ma Allah da ya bani ƙawa wacce zata iya faɗa min gaskiya idan yaga nayi wani abu ba daidai ba."
"Kada ki damu Fatima muna tare, zan tafi naga yamma ta fara yi."
"Nagode, muje to na raka ki"
Shin Fatima na daukar shawarar Khairat ko zatayi amfani da abinda zuciyar raya mata.
Don jin amsar wannan tambayar mu haɗi a page 36
Wadanda basu yi Following wannan page ɗin ba suyi domin samun littafai masu daɗi na marubuta daban-daban.
Kada a manta da.
Like, Comment and share.