Ajiya a Duhu Book 2 Last Page

 

Littafan Billyn Abdul

 Ajiya a Duhu Book 2 Last Page 

217

..........Shekaru sun ja, abubuwa da yawa sun canja, su AA sun dawo Nigeria gaba ɗaya, sai dai sun sake gida dan Abah da su kansu basa son tuna komai daya faru a waccan. Sabuwar rayuwa, sabon family, sabon muhalli.


      Kyawawan hamshaƙan manyan mata ne guda uku zaune a wani katafaren falo da yaji kayan more rayuwa na haƙiƙa bana yaku bayi ba. A kallo ɗaya zaka tabbatar da kuɗi, tsafta, gayu da ƙwalisa sun zauna. A shekaru duk bazasu wuce 35 ba. Hira suke cike da nutsuwa da fahimtar juna. Kowace da murmushi mai ƙayatarwa akan fuskarta. Yanda suke hirar ƙasa-ƙasa suna kallon hanyar stairscase da akai adon falon da ita tamkar ba'a Nigeria ba zai baka tabbacin gulma suke ko hirar da basa so aji. 

      Kamar kuwa hakan ne dan wani matashin dattijon mutumi da zai iya haura hamsin na ɓullowa alamar zai sakko falon da suke daga upstairs sukai shiru. Sanye yake cikin ƙananun kayan zaman gida na shan iska. Duk da shekaru sun turza ƙyawun haibar da cikar kamalar na nan, ga wani furfura ɗai-ɗai datai masa ado a saman kai da gemunsa.

     Ganin yanda matan suka haɗe kai a ƙasa ya ɗan kallesu da yanayin nan nashi na rashin sakin fuska ya furta, “An dasa gulmar ko?”.

     A tare suka kalleshi, Ameerah ta ɗan waro idanu da faɗin, “ALLAH Big Daddy mu bama gulmar kowa, hirarmu muke yi”.

        “To ALLAH yasa, ai nasan hali ne, musamman idan naga Lilly da Najmah na wani sinne kai”.

     Dariya Maanal da Najma suka sanya. Cikin haɗa baki wajen kare kansu. Shima sai ya ɗan murmusa da faɗin, “Okay shike nan. Har yanzu su Fawzan basu shigo bane?”.

        Manaal tace, “Sunce suna gab, wai sai sun sauke Uncle R a gida sannan”.

      “Humm daga nan kuma Nuwaira ta riƙesu sai sunci abinci ba. Ina yaran nan ko suna waje”.

     “Suna kitchen kaf ɗinsu, Ni bamma san wane tsiyar suke ƙullawa ba wai kar muzo sai sun gama.”

    Ɗan jimmm Babban Yaya yayi sai kuma ya kaɗa kansa yana nufar hanyar fita da faɗin, “To idan tayi wari maji, ni bari naje massallaci kuma ku tashi salla.”

     Da to duk suka amsa, Najma ta nufi hannayar kitchen taima yaran knocking. Tace su buɗe, cikin haɗa baki sukace su dai a'a. 

     “Ikon ALLAH wai ubanmu kukeyi?”.

     “Mah ke dai kawai kije kiyi zamanki abinki, idan mun gama su Yaya Naufal sun dawo daga inda sukaje zaku gani”.

         “ALLAH ya shiryeku to, sai ku fito kuyi salla”.

   Da to suka amsa mata, sai da suka tabbatar tabar jikin ƙofar sannan suka fito. Oh oh Masha ALLAH, ƙyawawan ƴammata ne guda huɗu duk masu kammani ɗaya. Ɗaya duk ta fisu girma, sai biyu kamar tagwaye, sai ƙaramar da bata kaisu ba. Babbar zata iya kai 17years, Maryam kenan da suke kira Norah babbar ɗiyar Uncle RK, sai tagwayen su biyu da zasu iya kaiwa 15years Khadee da Zarah kenan, sai ƙaramar da zata iya kaiwa 13years Urwa kenan (Ruƙayya) kai daka gansu kaga ƴaƴan madara malam, ga ƙyau ga nutsuwa kamar ƴaƴan larabawa. Ɗakinsu suka nufa dake sama ɓangaren Babban Yaya, dan itama Norah tuni ta dawo nan gidan. Babban ɗaki ne da gado huɗu kowa da nata. Haka sukai alwala sukai salla. Suna idarwa suka sakko ƙasa, dai-dai iyayen na sakkowa suma. Suka gaishesu a nutse, sai kuma ga sallamar wasu magidantan su biyu masu kammani guda. Ɗaya zai iya kaiwa arba'in da tara, ɗaya kuma arba'in da biyu haka zuwa da huɗu ma. Sanye suke cikin yaduka da sukai musu ƙyau suka fidda kamalarsu da nutsuwa. Ai da gudu yaran suka sakko a stairscase ɗin suna faɗin, “Oyoyo Abbah! Abie Oyoyo.”

        Murmushi ne sosai a fuskar AA da Yaya Fawzan, yaran suka iso gabansu suka rirriƙe musu hannuwa. Suko suka shashahafa musu kai suna amsa gaisuwar da suke musu da sannu da zuwa. Kwanansu uku kenna a Kano, sun je wani aiki ne. Dai-dai nan Babban yaya ke shigowa da wasu samarin matasan yara har su biyar cif. Masha ALLAH yaran gwanin sha'awa. Akwai babban saurayi da zai iya kaiwa 25years, sai wasu dake kai ɗaya kai daka gansu kasan ƴan biyu ne da zasu iya kaiwa 17years, sai ƙanana da zasu iya kaiwa 12years haka. Manyan ledojin shopping ne a hannunsu alamar daga can suke. Suma tuni suka ajiye ledojin suka zo suka maƙalƙale iyayen nasu suna musu sannu da zuwa. Sai da suka gama sannan Yaya Fawzan da AA suka rungume Babban Yaya suma. A lokacin ne kuma matan ke isowa na musu sannu da zuwa. AA ya wani kafe Maanal da kallo cike da shagwaɓa. Ido ta ɗan kashe masa tare da masa nuni da yaran da su Babban Yaya. Koda ya ɗan juya sai yaga ido yaya Fawzan a kansa. Ido AA ya ɗage sama da ɗan harararsa sannan ya duƙo cike da raɗa ya ce, “A dai rage gulma Abban yara”.

        AA bai rufe baki ba Yaya Fawzan ya amshe da faɗin, “Adai rage taɓara Abien yara”. Murmushi Babban Yaya yayi yaja hancinsu a tare da dungure musu kawuna. Sai yaran suka sanya dariya. Wannan ba sabon abu bane ba a wajensu. Su Maanal kam murmushi kawai sukai kowacce taja mijinta suka shige ɓangarensu.

       Suna shiga ɗaki AA ya rungume Maanal yana faɗin, “I miss you bestie”.

     “Miss you too Bestyn Besty”.

Ta faɗa tana murmushi da ɗago fuskarsa ta manna masa kiss. Zata janye ya cafke lips ɗin nata ya shiga sumbata. Tun kamar abin zai tsaya iya nan har aka ɗauki wata hanyar, dan da gasken sunyi missing junan, kwana uku a wajen AA da Maanal ai kamar shekara uku ne. A hakama koda yaushe ana manne da juna ta waya da video call. Basu gane kansu ba sai da suka gama faranta ran juna, sannan sukai sabon wanka suka fito, ta taimaka masa ya shirya itama ta canja shiga. Sallar la'asar ta saka shi fita, ita ko tayi a ɗaki sannan ta fita ta samo masa fruits dan yace sunci abinci gidan RK. Ana kuwa idar da sallar la'asar ya shigo. Dan haka ta kawo masa fruits ɗin, yana fara sha da ƙoƙarin kunna television tana jikinsa ita kuma yace, “Besty wai saura kwana nawa a fara bikin nan na su Barru ne?”.

         “Bai wuce sati uku ba fa, shiyyasa nake son a next satin nan ma mu shiga Dubai ɗin nan, gashi kai kuma kanata ciccijewa.”

     “Am sorry ba cijewa nake ba, kawai kai-kawon nan ne ya riƙeni, amma Alhamdullah ai na kammala. Ke da waye masu tafiyar?”.

        “Ai Mamma (Ameerah) ne kawai da Mah (Najma) sai yaran nan da suke ta naci yammatan, sai Aunty Sakina”.

     “Oh Shahidah da Amaal dai ba damar zuwa kenan?”.

     “Kai Besty, gamu kuma mi zasuje suyi suda zasu aurar da yara. Ai su ƴan kallone mune masu shirya komai”.

     “Hakane kuma amariri iyayen amare, nima ALLAH ya kaini randa zan aurar da nawa yammatan huɗu”.

    Murmushi Maanal tayi da faɗin, “Norah kam ai tana hanya, dan naga ita da Naufal da gaske suke kam. Sai dai Khadee da Zarah ai kwa ɗaga mana ƙafa da saura 15years da. Urwa kam ai ba'a magana balle su twins maza”.

        Cike da farin cikin zancen Norah da Naufal AA ya ce, “Amma ALLAH yay ma yaran nan albarka, haka nake fatan Muhammad da Ahmad su dai-dai da Zarah da Khadijah in sha ALLAHU”.

       “To ALLAH ya tabbatar, kuce duk ƴar gida zakuyi kenan”.

    “A in sha ALLAHU haka muke fata Besty”.

     “ALLAH ya bamu tsahon rai mai albarka kamar su Oum, wai yaushe zasu dawo ne wlhy kewarsu muke. Yau yaran nan suma tunda safe naga sun tashi suna gyara sashensu, kuma gasu can sun maƙale a kitchen bamu san uwar mi suke ba”.

           “Gyara fa dai?”.

       “Wlhy kuwa”.

   “To kodai su Oum na shirin dawowa ne jikokinsu kawai suka faɗamawa? Amma jiya munyi waya Abah ke cemin babu rana balle wata, ni harma naji haushi, dan na rasa mi suke a Yola ɗin nan ga zafi ma”.

     Kafin Maanal tace wani abu kawai sukaji hayaniyar yaran tayi yawa. Tashi AA yay da Maanal suka fito. Mi zasu gani Oum da Abah na shigowa. Maanal ta kalla AA, AA ya kalla Maanal. Sai kawai suka nufi staircase. Dai-dai su ma su Yaya Fawzan da Najma, Ameerah da Babban Yaya na fitowa. 

      Yaya Fawzan yace, “Dama bayin ALLAHn nan dawo zasuyi aka ɓoye mana sai jikokinsu”.

    Murmushi Babban Yaya da AA sukayi, Babban Yaya yace, “Ga alama kuwa Abbah”.

    Sakkowa sukai a tare, su Naufal na zagaye da su Oum daketa farin ciki. Duk da akwai jin daɗi tsufa sosai ya bayyana garesu. Dan kan Abah da sajensa duk sun zama furfura. Hakama Oum. Cike da tsokana suka buɗema su Babban Yaya hannu alamar oyoyo. Sai duk suka juya irin su sunyi fushin nan. Dariya yaran suka saka da su Aban, sai kuma suka fara lallashinsu. Suma duk sai suka murmusa suka juyo. Su Maanal ne suka fara zuwa ita da Najma da Ameerah suka rungume Oum, sannan Babban Yaya da su Yaya Fawzan suma suka rungume Abah. Kowa ka kalla kasan yana cikin farin ciki, satin su Oum biyu kenan a Yola daga bikin yarinyar Uncle Lamiɗo da akai aka kai can suka maƙale a asalin ƙauyen su Baba Sardauna na rugar Darma harda su Baba Sardauna ɗin wai zasu huta, suko suka shiryo suka dawo shine sai yau suke ganinsu.

       Sai da su Abah sukaje sashensu sukai wanka sannan yaran suka shirya abincin da suke haɗawa tun ɗazun a ƙaton dining table dake babban falo. Zaman hira akai ƴaƴa da iyaye zagaye da su Oum har magrib, bayan an idar suka zauna akai Isha'i sannan suka dawo gida. Suma zuwa lokacin su Maanal sunyi tasu kowacce ta yi sabon wanka da kwalliya ma oga, yaran ma sun yi tsaff da su sannan aka haɗu a dining. Cike da farin ciki da ƙaunar juna sukaci abincin su. Yaran suka gyara wajen mazansu da matansu sannan aka dasa sabuwar hira. Sai kusan 11 kowa ya nema makwanci. Washe gari ɓuruntun yara ya tada kowa. Koda suka fito sai suka tarar an gyara falon anyi decorating ɗinsa tare da ƙaton Symbol an rubuta *_HAPPY WEDDING ANNIVERSARY to the world's most wonderful grandparents! Your love is our legacy, and your journey inspires us every day._* Ƙasa suka saka 67years. Gasu sunci gayu sun haɗa abincin breakfast. Mamaki sosai iyayen sukayi, ashe abinda suke shiryawa kenan tun jiya.

      Farin ciki ya kamasu, hakama Oum da Abah bakinsu yaƙi rufuwa. Haka suka sakasu yin gayu. Su ma su Babba Yaya ai dole suka koma suka sake kwalliya. Sai da RK da Nuwaira da Aliyu da Kashim yaransu ƙannen Norah. Ai fa gida ya ƙara armashi. Anci ansha Abah da Oum suka ɗaɗarama cake wuƙa. Uncle RK shine Baba shi aka fara sakama a baki, sannan su Babban Yaya da su Maanal. Aka koma kan jikoki. Sosai ƴar walimar da yaran suka shirya ta ƙayatar. Ashe basu gama ba, da yamma ba sai ga ƙawayensu da abokai sun cika gida ba. Suka sha partyn su suka rakwashe suka ƙwalle sai iyayen suka zama ƴan kallo, dama ba barinsu suke yin wani birthday ba. Dan haka yau ma komai sun yi shi cikin nutsuwa da tarbiyyar da suka samu. Sai da za'ai hotuna su Maanal suka fito compound inda yaran suke bikinsu. Haka akai hotuna sosai harma da videos zuwa magrib aka tashi kowa ransa fal da farin ciki.✍️


Alhamdullahi, Alhamdullahi, Alhamdullah!! Kamar yanda nima Bilyn Abdull anan zan tsaya raina fal da farin ciki. Kuskuren da nayi ya rabbi ka gafarta min. Wanda na faɗa dai-dai ALLAH ka haɗamu a ladan ni da ku masoyana.🥰🙏


Kunyi ƙoƙarin kunyi juriyar bibiyar wannan labari daya mamaye mu yay tsayi fiye da yanda mukai zato. Amma Alhamdullah yau dai mun kai ƙarshe. Sai dai na ƙara ilimi da gane cewa lokaci na UBANGIJI ne, duk yanda ka kai ga sakashi bisa tsarin ka sai ya yarda. Sati biyu naso nayi na kammala bayan dawowarmu hutun salla. Amma sai gashi mune har a yau. To wannan itace tsarawar UBANGIJI ta gaskiya, dan dama kana naka ne yana nashi.😊❤️


Bazan gaji da godiya a gareku ba masoya, wanda suke bibiyata tun tale-tale dama masu ƙaruwa a yanzu. ALLAH ya saka muku da alkairinsa, ya tsare gabanku da bayanku, ya sanya farin ciki a rayuwarku kuma. ALLAH ya haɗamu a aljanna baki ɗaya. Ya rabbi duk wanda ya soni ina roƙonka da sunayen ka ƙyawawa masu tsarki kaima ka sosai haka shi da zuri'arsa baki ɗaya.❤️❤️❤️❤️❤️🥰🥰🥰🙏


Duk wanda na ɓatawa a yayin rubutu littafin nan ya yafe min, nima duk wanda ya ɓata min in har ba'akan izgili da ganganci bane na yafe masa. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya.😭😭🙏


      

   Ina son ku!!🥰 ina son ku!!😘 ina son ku!!❤️. Ina taya mu murnar shiga sabuwar shekarar musulunci. Sai kuma ALLAH ya kaimu wata sabuwar shekarar munzo muku da sabon Zafafa.❤️❤️❤️❤️❤️🙏


Yanda zanyi kewar Maanal da AA Darma kuma zanyi kewarku masoya.


WhatsApp number 

+234 805 568 7449


Bilyn Abdull ce😘    

((C)) 2015💤🔥✨

Post a Comment

Previous Post Next Post