Tsantsar Kauna
Page 34
Written by Tahir Yusuf (Novels Elite)
Na bar ta, ta dauki Affan ta giya shi ta saka hijabi ta bude ƙofa ta fita, sai ta dawo ganin dare yayi ɗaki kawai ta wuce ta kwantar da Affan itama ta kwanta, na shigo nayi ta magana amma bata amsa ba, ganin taƙi kulani yasa na ɗauko waya ta na cigaba da magana da Maryam har bacci ya ɗauke Ni.
Washe kuwa da sassafe Fatima ta fita daga gida ta tafi gidansu.
Abdullahi na kira na sanar dashi halin da ake ciki, abin ya bashi Mamaki kwarai da gaske in da yake cewa
"Kamal mace na iya yin komai akan kishi, ka bi komai a hankali, kada ka je gidan, ka barta tukuna, nasan ko a gidansu ba'a a goyi bayan ta ba"
"Irin yadda tayi jiya wallahi ya bani mamaki sosai, ashe ko wata mace tana da kishi sosai."
"Yanzu dai ba wannan ba, ya maganar tafiya Yola,?
"Tafiya ta na nan dama ranar Juma'a nake so mu tafi amma kuma ga abinda ke faruwa, ko zamu jira mu ga yadda za'a sasanta wannan matsalar na Fatima"
"Eh, Nima dama abinda nake so na ce maka kenan mu jira muga yadda abin zai kasance"
"To shiken Allah ya warware mana wannan damuwa"
Abdullahi ya amsa da Amin kafin na katse kiran.
Sallamar Fatima ne ya tashi Hajiya Rabi daga baccin da ya ɗauke ta kan addu'ar da tayi Sallah, ko amsa sallamar ma ba ta iya yi ba.
"Lafiya kuwa Fatima da sassafe haka?
"Umma ba lafiya na"
"Me Kamal ɗin yayi Miki?
"Umma wai Kamal aure zai ƙara"
Aure zai ƙara shine ya kori ki gida ko yaya?
"Ba shine ya kore Ni ba nine kawai bayan iya zama tare da wata ba, fara na bar Kishi gidan"
"Fatima, zauna muyi magana.
Fatima ta kwantar da Affan wanda har lokacin yana bacci ne tashi ba sannan itama ta zauna Banda kuka babu abinda ya ke yi. Umma ta lalle tace "share hawayen ki kuma daina kuka ki saurari abinda zan faɗa Miki"
Fatima ta zauna sannan ta barshi amma dai hawaye bai daina fitowa daga idon ta ba.
"Fatima, kin daina samun kulawa ne daga wajen shi?
"A'a, yana sona sosai hasali ma duk abinda nake so yana yi min"
"To amma meyasa kike fushi harda barin gida don zai ƙara aure, ƙarin aure ba laifi bane ko a Muslunci, saboda haka Banga laifin da ba don zai ƙara aure"
"Haba umma nema kina goyon bayan da ne?
"Kada ki zama mai son kan ki da yawa mana Fatima, yanzu idan kina da Yaya namiji yana son ƙara aure, zaki goyi bayan ya ƙara ko baza ki giya masa baya ba?
"Zan goya masa baya"
"To kin gani, Fatima ki zama mai yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, saboda duk abinda Allah Ya ƙaddara ko kina so ko baki so sai ya faru, saboda haka tun kafin Banki ya dawo daga Masallaci ki koma ɗakin ki domin idan yaki wannan maganar ran ki zai ɓaci sosai."
Tana rufe baki Alh. Abubakar yayi sallama ya shigo
"Lafiya kuwa me Fatima keyi a gidan nan da sassafe?
Umma ta bashi labarin duk yadda akayi
"Fatima, a matsayina na mahaifin ki ina so ki kwantar da hankalin ki, don zai ƙara aure ai ba haramun bane, kamata yayi ki goya masa baya hakan zai sa ki ƙara samun matsayi a wajen da, ki kasance mai son duk abinda yake so in har bai saɓama shari'a, hakan da kika yi kuskure ne babba, na farko kin fita ba tare da izinin sa ba, ki ji tsoron Allah ki zauna da mijin ki tsakanin ki da Allah"
Fatima ta ƙara fashewa da kika, Ganin haka Hajiya Rabi ta ci gaba da rashin kafin ta cigaba da fadin "Ki sani, a yanzu baki da wanda ya wuce Kamal a rayuwarmu, ina so yanzu ki tashi ki koma gidan ki, idan ba haka ba, kina ji kina gani wata zata kwace Miki miji, dole sai kin sake dagewa wajen kula da mijin ki, ki taya shi don duk abinda kikasani yana so, hakan zai ƙara Miki matsayi wajen mijin ki, sannan ki kula da girki sosai"
Mu haɗu a page 35 don jin Fatima na tafiya gida, tana amincewa da auren Kamal kuwa.
Wadanda basu yi Following wannan page ɗin ba suyi domin samun littafai masu daɗi na marubuta daban-daban.
Kada a manta da.
Like, Comment and share.