214
.......A washe garin da aka sallami Oum da Maanal suka bar Nigeria gaba ɗayan su. Kuma da alama wannan tafiyar mai daɗewa ce. Dan ƙasar Chaina suka dira. A block ɗaya suka kama wajen zama. Sai dai kowa da apartment ɗinsa, amma floor ɗaya suke kuma a jere guda huɗu reras. Kowanne a nashi akwai bedroom ɗaya, kitchen, falo, sai wajen karatu. Komai dai tsaff, babu takura babu gajiyawa. Tsarin kuma duk iri ɗaya ne. Duk a gajiye suke, dan haka kowa yaja matarsa suka shige nasu. Oum ta amshi ƴan biyu ita da Abah, idan akai musu wanka a maido su. Hakan ya bama AA damar jan hannun Maanal suka shige nasu suma. Dan shekaran jiya ƙiri-ƙiri da aka sallamosu asibiti taƙi zuwa sashensu ta wuce wajen Oum. Haka ta barshi ya kwana shi kaɗai, sai a jirgi ne suka zauna waje ɗaya. Suna shiga ya maida ƙofar ya rufe ya mannata a jiki. Kallonsa take fuskarta babu walwala sam, ga idannunta sun ɗan ƙara fitowa saboda ramar da tayi ta jiyya. Shima kallon nata yake cikin wani yanayi mai wahalar fassara, kafin a hankali ya motsa lips ɗinsa cike da raɗa ya furta, “Besty bazaki yafe ma Ajwaad ki daina fushin nan ba?”.
Kanta ta ɗan kawar gefe kaɗan, idannunta na tara ƙwalla, ALLAH har yanzu taƙi daina ganin yanda yake dukan Nibras a idanunta da yanda take tsirara sai kimono a jiki, da yanda ta dinga roƙonsa akan yaransu amma taurin kai irin na mutumin nan ko. Hummm. Hannu yasa ya dawo da fuskar tata inda yake, sai kuma a hankali ya matsar da tashi gab yana busa mata numfashi. Cikin sake sauke murya ya ce, “Yanzu minene laifina anan? Ko sai yanzu kike jin kishi?”.
Hannayenta biyu ta saka ta turashi, dan wlhy da gaske fa sai yanzu take jin kishin abinda Nibras ɗin tayi, dan tun bayan lafawar komai zuciyarta ta kasa nutsuwa, tana matuƙar son tasan minene ya faru har yay ma Nibras dukan nan, musamman data ganta tsirara sai kimono a jiki. Amma babu wanda ya gaya mata komai har shi. Bata zarginsa, kuma ai tasan Nibras ɗin ce ta kawo masa kanta, amma idan ta tuna ko wani abu ya faru zafi zuciyarta take mata. Yanda take turashi shi kuma ko gezau baiyi ba ya sake fusatata tasa hannaye biyu tana dukan ƙirjinsa. Tsayawa kawai yayi yana kallonta yana danne dariya da ƙyar, sai da tayi iya iyawarta har ta gaji dan kanta ga hawaye sannan yay murmushi da kamota ya rungume tsam a jikinsa. Sai ta sake sakar masa kukan kawai. Baice mata komai bai har tayi shiru dan kanta sai a jiyar zuciya kawai take saukewa, sannan ya ɗagata cak ya nufi bedroom, saman haɗaɗɗen gadon ɗakin ya kwantar da ita ya fita ya jawo akwatinsu ɗaya jal sai dai babba ne sosai, sai bag ɗinta da bag ɗin laptop ɗinsu ita da shi dan aiki kam dole a cigaba da yinsa daga nan. Har lokacin tana a kwance inda ya barta. Baiyi magana ba ya shiga bayin ya dudduba sannan ya dawo bedroom ɗin ma ya dudduba, ya fita falo da ko'ina na gidan ya sake dawowa ya shiga bayin ya haɗa ruwa a jacuzzi mai ɗumu da ƙamshi sannan ya zo ya ɗagata ya cire mata kaya ya cire nashi ya wuce da ita. Cikin ruwan ya saka su, a tare suka sauke ajiyar zuciya. Sai kuma yanda ya ɗan ƙanƙameta ta ɗago tana kallonsa. Murmushi yay mata ƙasa-ƙasa fuskarsa a shagwaɓe ya ce, “Please Besty ki huce mana”.
Kafaɗa ta maƙe masa tana tura baki da kauda kai. Ya riƙo haɓarta cike da lallashi yace, “Mizan miki ki huce to?”.
“Ka faɗa min abinda ya faru a ranar”.
Ajiyar zuciya ya sauke, sai kawai ya shiga bata labarin komai bai ɓoye ba. Kai tsaye ta ce, “ALLAH ya isa ban yafe mata hawa min jikinka da tayi ba wlhy”.
Dariya ce ta kusa kufcema AA ya danne da ƙyar, sai kuma ta kalleshi itama kamar wata yayarsa ta ce, “Kai ma ka kalleta ko?”.
Kansa ya girgiza mata yana sake rungumota. “Ai har abada babu wata surar jikin mace da zata sake birge Ajwaad balle ta zame masa abin kallo in sha ALLAHU Besty. Kiyi haƙuri Besty mubar maganar nan wlhy ko tunawa bana son yi dan ƙona ni take matuƙa, ina jin nauyi da kunyar Yaya Fawzan da ke kanki da yarana, shiyasa har yanzu ji nake ban gamsu da abinda nai mata ba ma”.
Karon farko Maanal tayi murmushi tana shafa ƙirjinsa cike da kulawa. Sai kuma ta tausasa murya ta koma lallashinsa. Sun jima a bayin kafin su fito, haka ya taimaka mata tai shirin barci shima yayi, basa jin yunwa dan sun ci abinci a jirgi gab da zasu sauka. Dai-dai nan bell tai ƙara, yasan su twins aka kawo dan haka yaje ya amso su hannun Abah, sai coffee da Abah yay musu order shima suma su Babban Yaya sun amshi nasu. Sukaima juna sai da safe ya koma nasu shima ya shigo. Bayan sunsha coffee ɗin Maanal tayi feeding su twins kwanciya kawai sukayi duk da AA na cikin yanayin buƙata haka ya daure....
__________★
Satinsu ɗaya kenan a Chaina, Alhamdullah jikin Maanal kuma yayi sauƙi sosai, dan anan ma ta sake ganin likita sun tabbatar musu komai kuma normal. Shi AA ma ranar baya nan sunyi tafiya da abokinsa prof.. wani program. Oum da dama tafe take da kayan gyaranta sai tayi amfani da wannan damar ta shiga gyara Maanal ta jiki data ciki. Dan danan ta ƙara murjewa da gogewa dama ramar nan da tayi duk ta ciko abinta, sai wani glowing take kuwa Masha ALLAH. Ameerah da Najma suka sakata gaba, wai da alama Yaya AA na dawowa ba sauƙi za'a sake samo twins. Tun tana ƙyalesu harta fara ramawa itama. Kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki da ƙaunar juna ta haƙiƙa. Su twins sam basu da taka maiman wajen zama. Barci kawai ke kaisu wajen Maanal.
Kwanan su AA takwas suka suka dawo. Kallo ɗaya da Maanal tai masa ta fahimci babu sauƙi, dan bai ɓoye mata ba ya fito fili ya nuna mata yana cikin wani hali. Murmushi kawai tayi batace komai ba, sai da ta taimaka masa yaci ya ƙoshi ta jashi bayi yin wanka. Anan ne fa ya kasa jurewa aka fara sakin layi, ƙarshe dai babu arziƙi aka kammala wankan aka fito. Daga nan ne fa labarin ya canja. Haba ai yayi haƙuri, kusan wata biyu.
Yako tabbatar mata yayi haƙurin, dan taji a jikinta har sai da ta koma masa kuka da magiya. Amma ina sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so sannan ya koma lallashi da ban haƙuri, itako tana zuba masa shagwaɓa. Tun daga ranar aka buɗe sabon shafin amarci. Kullum suna sake mannema juna, kowa ƙoƙarin ƙyautatama ɗan uwansa yake. Kamfani kuwa suna tafi da komai yanda ya dace daga nan tamkar suna a gida Nigeria. Ga yaransu sunyi ƙyau sosai kamanin iyayensu na sake fitowa a tare da su.
Haka suma su Babban Yaya komai Alhamdullah, daga ɓangaren aiki har samun soyayya wajen matayensu, dan daga Ameerah har Najmah suna iya ƙoƙarin su suma na faranta musu. Ga ciki suna fama amma basa nuna gajiyawa da kulawa. Tsakaninsu da Oum da Abah tamkar iyaye ne da ƴaƴa ba surukai ba da iyayen miji. Duk abinda basu fahimta ba haka Oum ke zama ta koya musu yanda zasu gane. Kamar yanda suke kiran iyayensu da ƴan uwansu haka suke kiran Mamy suna gaisheta da Aunty, tun Mamyn bata sakewa har dai ta sake ɗin. A haka suka shiga watan haihuwa, dan tsakaninsu babu wani nisa sosai. Gaba ɗaya sai kulawarsu ta koma ƙarƙashin Oum da Maanal. Mazansu da ƴan uwa na binsu da addu'ar sauka lafiya.
Alhamdullahi Ameerah ce ta fara haihuwa ɗiya mace. Zo kaga murna wajen a halin Darma dana Hajiya Shuwa da dangin babanta na Katsina. Dan danan hoton yarinya mai kama da babanta ya baje ko ina. Kowa farin ciki yake da annashuwa. Anama Baby addu'a anama mai jego. Anama su Oum barka. Lokacin da Mamy taga hoton Baby harda hawayenta. Ita Aunty ma wlhy yanzu tausayi ƴar uwar tata ke bata.
Sati ɗaya da haihuwa aka sakama yarinya sunan Oum, sunan Anum ke nan, sai dai ita suna mata laƙani da Zarah. Duk da ba ƙasarsu ba AA yace sai sunyi shagali. Haka kuwa akayi, suka haɗa ɗan walimar cin abincin dare suka gayyaci abokan arziƙi na ƙasa da baƙin haure irinsu. Akaci akasha aka ɗan rausaya. Ƴan Nigeriya sai videos sukaita gani kawai da sanya albarka. Maijego tayi ƙyau har ta gaji, hakama Baby da ƙawayen maijego su Maanal, su twins yayu da sukai ɓul-ɓul abinsu dan har sun fara koyon zama ma sun sha ƙyau.
Sati uku tsakanin haihuwar Ameerah data Najma, itama ta sulluɓo yar budurwa mai kama da Yaya Fawzan. Yara dai duk sun rantse gidansu zasu ɗakko. Ya suhanallah wannan haihuwa ta musamman ce a zuri'ar Darma baki ɗaya. Danda nan itama hoton Baby ya fara yawo, finally Yaya Fawzan yaga jininsa a duniya. Ga yarinya ƙatuwa Masha ALLAH. Mutane sun so azo Nigeria a yi suna, sai dai yanzu ma haƙuri su Oum suka basu, dan su fa da gaske so suke su bama Nigeria iska sosai da sosai. Nan ma AA bai haƙura ba yace sai fa sunyi bikin suna. Haka kuwa sukayi shi tamkar na haihuwar Ameerah. Yarinya ta ci suna Khadijah. Nan ma anci an sha an yi wadaƙa sai dai mu babu damar cin banza wannan karon an barmu a Nigeria 🤭🥱. To ALLAH ya sanya albarka bazamu fasa addu'a ba ai.........✍️