Tsantsar Kauna
Page 33
Written by Tahir Yusuf (Novels Elite)
https://chat.whatsapp.com/CdAafth1AN96UeXKPuGzH2
Read My Book "Tsantsar Kauna" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681eab4136c55fcf7c41cd3f
Maryam da Salima ya samu zaune a falo sun jera masa abinci kala-kala wanda suka dafa domin dawowar sa, da sauri Salima ta rungume shi sannan ta karfi jakar da ke hannunsa, sannan ya zauna Maryam tayi masa Barka da hanya.
Bayan ya ci abincnaya huta sai ya buka ci gani na domin isar da saƙon iyayen Maryam, bai sha wahalar samun sa a waya ba, ya sanar da Ni yana son gani na gobe da safe
"Idan Allah ya kai mu gobe zan zo"
"Shike nan Allah ya kawo ka lafiya."
Bayan Mun gama waya na kira Abdullahi na sanar da shi halin da ake ciki, Inda yace
"Kamar yanzu ne ne lokacin da Yakamata ka sanar da Fatima maganar auren ka amma sai mun dawo daga gidan su Maryam tukuna domin jin dalilin kiran."
"Allah da ya kai mu goben, Karfe 11am na safe zamu tafi"
"In sha Allah zan zo da wuri sai mu tafi"
"Allah ya kai mu"
"Amin"
Kamar tana jira mu gama waya da Abdullahi, sunan Love 002 ne ya bayyana a fuskar wayar wanda yasa da sauri na ɗauka.
Cikin sanyin murya mai cike da soyayya tace "Masoyi, ka wuni lafiya"
"Lafiya ƙalau My Love"
"A ko da yaushe gani ne ke yi kamar ina mafarki"
"Me yasa?
"Ganin zan same ka matsayin abokin rayuwa na tsawon rayuwa wanda zan ba kulawa da yi masa duk abinda yake buƙata, na tanadi abubuwa da yawa wadanda ba zaka san su ba sai lokacin da muka yi aure"
"Lallai! Ashe Ni Ɗangata ne, amma waɗansu irin abu ne haka wanda aka tanadar min?
"Zan baka kulawa wanda ba'a taɓa baka irin sa ba, zan ririta ka kamar jariri, sanyi maka duk wani abu da kake so, ko menene shi?
"Alhamdulillah! Gaskiya kuwa idan haka ne zanyi farin ciki da samun ki matsayin mata, Nima zan baki kulawa irin wanda ba'a taɓa baki irin sa ba, duk abinda kike so sanyi Miki, magana kawai ba zai bayyana irin kulawar da zan baki ba matsayin mata ta, kina bani farin ciki da nishad"
"Babban burkina shine na ga na saka Nishaɗi da farin ciki na tabbatar baka nemi wani abu ka rasa ba sai dai idan bani da ikon mallaka maka shi, ina ƙaunarka sosai Baban Affan"
"Nima ina kaunar ki Maryam, fata na Allah ya zaunar da mu lafiya, Allah ya sanya fahimta tsakanin ki da Fatima"
"In sha Allah ba zaka sami wata matsala tsakanina da Aunty Fatima ba, sai dai idan daga wajen ta, amma Ni in Allah ya yarda hakan ba zai faru ba."
"Allah ya tabbatar mana da hakan Maryam"
"Amin my love"
Munyi Hira sosai na fahimta matsayin waɗanda zasu zama mata da miji nan gaba, Alhamdulillah mun fahim ci juna sosai sai dai ban san ko nan gaba ba, domin yau da kullum ya wuce wasa, Allah dai ya zaunar da mu lafiya.
Washe gari tun ƙarfe 10:50am na safe Abdullahi ya kira Ni ga shi a waje lokacin na karya nayi wanka shi kawai nake jira dama yazo mu tafi.
Kasancewar da motarsa zamu tafi yasa ko shigowa baiyi ba don ko fitowa daga motar ma bai yi ba yana jira na fito, Affan ne ya fito da sauri da tuhumar da zai bi Ni.
Da sauri Fatima ta fito ganin zan fita, "Baka ɗauka key ɗin motar ka ba, ko baza ka fita da ita bane"
"A motar Abdullahi zamu tafi, yana waje ma yana jira na"
"To muke na raka ka wajen "
Ta ɗauko hijabi ta saka ta biyo mu a baya Ni kuma ina rike da hannun Affan har muka isa inda Abdullahi yayi parking motarsa suka gaisa da Fatima sannan ta karɓi Affan suka koma gida mu kuma muka tafi inda zamu je.
Ƙarfe 11:17am muka isa gidan su Maryam cikin harakar gidan muka shiga da motar mu bisa umarnin Ibrahim mijin yayan Maryam, cikin falo muka zauna sannan shima ya fito ya zauna.
Bayan mu gama gaisawa ya kwashe duk yadda sukayi da iyayen Maryam a lokacin ziyarar sa Yola.
Cikin murna da farin ciki na amsa da in sha Allah zan je amma ban saka rana ba, amma idan na saka rana zan sanar da shi domin ya haɗa mu da wani a can saboda idan mun je kada mu sha wahalar gane unguwar.
Kuran sallar Azahar ne ya nuna mana rana tayi wanda bayan Mun gama magana da shi mun fito tare da Maryam kuma muka tsaya fira.
A hanyar mu ta komawa ne Abdullahi ya lalle Ni ya ce
"Kai abokina gaskiya yarinyar nan tayi, tana da hankali gata da natsuwa da sanin Yakamata, kada fa ka saka Nima na ƙara fa"
"Ka ga dama akwai wata ƙawarta Zainab"
"Wanda muka gansu tare last zuwa da muka yi?
"Eh ita"
"Amma fa Ni ban shirya ba gaskiya, ba yanzu ba"
"Kai dai kana jin tsoron Naman Ahmad dai?
"A'a wallahi, kasan aure lokaci ne idan lokacin ƙarin nawa yayi ƙila ma kaga na riga ka.
"Allah yasa da gaske kake yi"
"Amin, yauwa Kamal yau ne Yakamata ka sanar da Fatima kana neman aure amma cikin dabara da lallaɓa, so samu ne ma ka shi mata abinda kasan tana so sosai kafin ka faɗa mata, kuma ka ja hankalinta sosai bayan ka sanar da ita. Saidai zaka iya fuskantar canji daga gare ta amma kada ka ɗaga hankalinka, kawai ka cigaba da lallaɓa kayansa"
"In Sha Allah babu abinda zai faru idan na sanar da ita."
Ai kuwa hakan nayi, Fatima na son ice cream sosai, bayan Sallar Isha na fita na siyo mata ice cream Nima na siyo abinda nake so na dawo gida, na bari da natsu tan sha muna fira, kafin na kalleta nace
"Sweetheart ina so muyi wata magana"
Ta kalleni cikin yanayin dake nuna damuwa a fuskar ta, "wata irin magana kenan?
"Sweetheart Dan Allah kada ki ɗaga hankalinka idan na sanar da ke maganar da nake son faɗa Miki"
"Shikenan ina sauraro"
"Sweetheart, Aure nake son yin"
Ta ajiye ice cream ɗin dake hannun ta sannan ta kiwo ta kalle Ni da kyau kafin ta fara magana cikin rawar baki "Kamal, aure kuma? Laifin me nayi maka, ko ka gaji da Ni ne?
"Fatima ta ya zan gaji dake...........
Ban gama magana ba ta katse Ni cikin Muryar kuka ta ce "gashi nan kuwa zaka ƙara aure alamun ka gaji da Ni kenan ai"
" Ba haka nake nufi ba, ƙarin aure na baya nufin na gaji dake ko kuma wulakanta ki, baya nufin tozarta ki ko cin mutuncin ki, abinda nake so kawai a wajen ki addu'a kawai"
"Babu wani abu da zaka ce min, Ni gidan mu zan wuce yanzu, idan ka auri ta sai ku zauna tare da ita" Fatima ta fashe da kuka mai ƙarfi wanda hakan yasa hankalina ya tashi sosai, ta shi da niyyar fita na hana ta ganin lokacin ƙarfe 10pm na dare, nace koma dai menene ta bari sai da safe
"Ba abinda ya dame ka Ni dai ka bar Ni na tafi gidan mu, ba ruwanka da dare yayi dama ai Allah ke tsare wa"
Na bar ta, ta dauki Affan ta giya shi ta saka hijabi ta bude ƙofa ta fita.
Mu haɗu a page 34 don jin Fatima na tafiya gida, tana amincewa da auren Kamal kuwa.
Wadanda basu yi Following wannan page ɗin ba suyi domin samun littafai masu daɗi na marubuta daban-daban.
Kada a manta da.
Like, Comment and share.