Tsantsar Kauna Page 32

Ajiya a Duhu book 2, Zafafa 5

 Tsantsar Kauna 


Page 32


Written by Tahir Yusuf (Novels Elite)

Tun bayan zuwa neman izinin neman Maryam nake ta saƙe-saƙen yadda zan sanar da Fatima Amma bana so na faɗa mata da wuri sai anyi magana da iyayenta na Yola kafin na faɗa mata Ko yau ne aka saba dasu duk Amin ce in sha Allah zan faɗa ma Fatima halin da ake ciki.


"Kamal, Kamal " kiran da Fatima tayi min ne  ya katse min zancen zucin da nake yi.


"Na'am, Maman Affan"


"Lafiya kuwa kayi shiru ina ta magana ba jakin ma abinda nake faɗa?


Lafiya Lau kawai wani abu ne ke neman ya dameni."

"Dan Allah ka daina tunani da yawa kada ya haifar maka da wani Matsala.


Haka mukayi ta hira kafin wayar ta tayi ƙara, tsam na miƙe ganin Maryam ce ke kira, sai da na fita waje sannan na ɗaga 

"Assalamu alaikum" ta fadi na amsa da 

"Wa'alakumussalam"


"Ka tashi lafiya, ya su Affan."


"Lafiya ƙalau amarya"


Maryam taki kunyar da sai da ta sunkuyar da kan ta kamar suna tare.

"Amarya kuma ?

"Eh mana ko ba Amaryar ba ce?


"Hmmm!" Abinda ta iya faɗi kenan.

Doguwar waya sukayi sakamakon ba kusa da Fatima nake ba,  soyayya ta da Maryam wani haɗi ne daga wanda ya halicce mu domin kuwa shi kaɗai ne yasan dalilin haɗa wannan soyayya.


YOLA

Tun zuwan Ibrahim mijin yayan Maryam ya sanar da iyayenta halin da ake ciki game da maganar aure wanda Kamal ke nema, sunyi farin ciki sosai dama babban burin su shine Maryam ta sami mijin aure, mutumin kirki. 


Ibrahim yayi kwana takwas a Yola yan uwa da abokan arziki sunyi murna da zuwan sa, dama ya daɗe bai je Yola ba, hakan ya kara ƙarfafa zumunci da da yan'uwansa da iyayen matarsa. 


Ana gobe Ibrahim zai dawo daga Yola yaje gidan su Salima don yi ma iyayenta sallama, ya same su duk zaune a falo sakamakon bayan Sallar Isha'i ne mafi yawancin manyan mutane suna gida a wannan lokacin, dama dai ya sanar da su kafin ya tafi gidan

Yayi sallama, suka amsa, kafin ya shiga,

"Mun wuni lafiya"

Gaba ɗaya suka amsa da "lafiya Lau"


"Dama na zo yi muku sallama ne idan Allah ya kai mu gobe zan koma"


"To Allah ya kiyaye hanya, Allah ya mayar da kai gida lafiya" mahaifiyar Maryam ce ta masa kafin mahaifin Maryam yayi magana, inda yace


"Dan Allah idan ka koma muna son Kamal ya zo mu ga shi in ya sami daman haka, sauran maganar aure kuwa mun bar maka komai a wajen ka saboda Maryam da haifar ta kawai mukayi amma a wajen ka ta girma, da Allah ya baku haihuwa da yanzu yarinyar ku zata kusa s'a da Maryam, ko da zata girme ta kuwa ba da wani abu bane"


"Nagode da irin wannan karamci da akayi min, amma idan maganar aure ya taso ina so zan Turo da kuɗin mota wani daga nan yazo ayi tare dashi, ko da Baffa Kasim ne" 


"To shikenan Allah ya nuna mana lokacin" abinda mahaifin Maryam ya faɗi kenan har Ibrahim ya miƙe zai tafi 


"Mu'azzam ɗan jira kadan akwai sakon Salima da za'a kamata" kasan iyaye mata suna son ya'yan su musamman ma ba kusa suke ba.


Ibrahim yayi farin ciki sosai da irin karamcin da aka nuna masa a gidan su Salima matarsa, Na bashi damar aurar da Maryam matsayi waliyyinta.


Washe gari kuwa tun da sanyi safe Ibrahim ya kama hanyar Zaria daga Yola. Tafiya ce na kusan yini guda, ƙarfe shida na safe ya bar Yola, sai ƙarfe 5:30pm na yamma ya isa garin Zariya.


Don jin cigaban labarin mu haɗu a page 33

Post a Comment

Previous Post Next Post