🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON🌕
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
GABATARWA
Wanan Labarin zai fara zuwa muku Ranar Litinin da yardar Allah shafin shine asalin gundarin labarin matafiya ne wanda suka bar kasar su zuwa wata ƙasa domin muradun su, a sannan labarin ne cikin labari domin dukkanin su zasu bamu labari mabanbanta daga cikin tafiyar su
sanin haƙiƙanin labarin lallai sun mun shiga ciki domin karatu tare....
Masu laɓe a cikin group wanan sabon littafi ku fitoo kafin ayi waje daku fatan zaku na sharhi da share Nagode..
Chapter 1 & 2
Tafiya Mabuɗin ilimi
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم
Ƙara duba email nasa yayi nan John ya dafa kafaɗar sa " Common man muna late fa " ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske cikin tunani tsarin ɓarauniyar hanyar da zasu bi daga Kano zuwa Dubai cikin kwana 150
Addu'a suka fara bayan kammala wa motar tasu ta zubin taxi ya tashe da matuƙar gudu
Duk wani abun buƙatar su na abinci kuɗi sutura tare da abun bukatar su na yau da gobe yana cikin wannan motar
Hannu tasa tana lissafi cikin buguwar zuciya
" Kano (Nigeria) Yobe → Chad → Libya → Egypt → Israel → Jordan → Saudi Arabia → United Arab Emirates (Dubai)
Yanzu wanan ƙasasshen dukka sai mun tsallake su Innallilahi wai'na illaihin rajiuon " take hawaye ya fara zubuwa a idon ta, harara Maryam ta buga mata " Haba Ihsan meyasa kina da saurin kuka ne tafiya ce kawai duk da munsan akwai wahala a hanyar mu amman ai muna tare ke tuna buri da muke dashi a rayuwar mu idan bamubar Nigeria ba ina zake samu bukatar aikin da muke so " ..
Tunda suke magana Yazid na latsa wayar sa wanda yake buga game nasa cikin nishadi sosai
Yazid,
Yaro ne mai shekaru 25 a rayuwar sa ya gama makarantar secondary school sai dai yana da Babban buri a rayuwar sa ma buɗe katafaren Company gine gine hakan yasa ya yanke shawarar zuwa ƙasar Dubai inda suka samu labarin ana zuwa neman kuɗi sosai kuma ana dace domin kuɗaɗen su mai matukar girgiza ruhin mai neman kuɗi da wanan niyyar ya baro gida
Ihsan
Yarinya ce wacce take da shekaru ashirin a rayuwar ta sai dai ta tasu daga gidan marayu na nan Kano tabbas Ihsan yarinya ce mai basira sosai ga kuma kyau da ilimi sai dai Ihsan yarinya ce mai neman na kanta duk inda taga zata samu kuɗi tana zuwa neman aiki lungu da sako Ihsan yanzu babban burin ta shine ta samu jari sosai wanda zata fara kasuwanci gari zuwa gari har ma da ƙasasshen waje Amman yanzu dole sai ta tafe Dubai domin samun aiki ko na aikatau ne domin cikkar muradun ta.....
John
Idan ana neman yaro mai karfe da fikira to John ya samu wanan shaidar babban abokin Yazid kinan wanda suka ye makarantar tare sai dai shi ya samu aikin soja wanda aka Kore sa daga aiki dalilin mugun ƙazafin da abokan sa suka masa shi kuwa ya yanke hukuncin baren ƙasar domin ya tafe nemo kuɗi kodon huci takaice abinda aka masa .....
MARYAM
Kuna neman matsoraciyya yarinya ga tsoro ga rashin jin magana ga kuma taurin kai sai Maryam wacce take da shekaru ashirin da ɗaya chifff Maryam ta tasu gaban muguwar kishiyar uwa wacce sai abinda tace baban ta zaiyu hakan yasa take azabtar da Maryam ta kowani yanayi kyakkyawan yarinya ce ga ilimi boko da na arabiyya sanan tayi karatun health care ƙaramar nurse ce dalilin barin ta gida kuwa kishiyar uwarta ne ta yanke mata hukuncin auren wani tsoho a unguwar sa wanda baban ta ya amince hakan yasa ta gudu tabar gidan sai gashi ta haɗu da ƙawa a titti wato Ihsan wanan yasa ta yanke shawarar binsu chan ko ita ma zata tsira da gujje gujje da take ye akan hanya ..
ADO
Engineer kinan saurayi mai shekaru ashirin da tara mai hazaƙa da basira baiye makarantar ba sabo da tsananin talauci wa da bai san uwar sa ko uban sa ba a kan titti ya gansa yana tafiya bashi da kowa ko komai Amman ko wacce mota ce ya iya gyara ta sanan ya iya duk wani abinda ya shafe igiyar wuta, sanan ya taɓa shiga ƙasar Chad neman kuɗi a takaice dai Ado yana cikin wanan sahun tafiyar domin yana da buri mai yawa a rayuwar sa ...
A haka suka kama hanyar Yobe state domin fara tafiya zuwa Chad, muna fatan tafiya yayi kyau a dawo da cikakkiyar nasara...
Please don't forget to comment and share
Continued........
Narnah ƙanwar soja ✍️✍️
—