Ginshikin Dutse page 3&4 Complete by Ummu Affan

Abokiyar Hira free novels

GINSHIƘIN DUTSE...

      _True life story._

*BOOK 1* 


UMMU AFFAN.


*Page 3-4*

Sai dai, ashe gudun gara tayi inda ta afka gidan zago domin Yaya Salisu ne ya shugo kwanar akan kekensa, sanye yake da baƙaƙen kayansa na aiki kasancewarsa na ɗan Walda. Domin Salis akwai ƙoƙarin neman halaliya da ya dawo makaranta to fa zai wuce Fanteka inda yake aikin Walda irin na su Gadajen ƙarfe su kujerunsu da gate na gida da ƙofofi da winduna a gurin mahaifin abokinsa inda shi da abokin nasa duka suke zuwa. Ƙoƙarin ɓuya tayi don kar ya ganta sai kuma ta makaro inda suka yi karo ɗaya wanda ƙwai da dutse ma sayi.

  "Ah yawo kazar ƙauye, ina kuma zaki lokacin islamiyya?"

Yadda taji sautin muryarsa a kanta ji tayi da da hali sai ta mazga mishi mari, sai ta juyo tana tura baki gaba idanuwanta cike da rashin kunya ta ce, "Innana ce ta aike ni ai."

  "Anya kuwa Surayyah? Kin san karona da ke muddin ƙarya ki ke." 

Babu ɗar balle shakka a tare da ita ta ce, "Eh da gaske ita ta aike ni, kuma ga Yaya Auwalu zaune a majalisa idan nayi ƙarya a tambaye shi."

Girgiza kai kawai ya yi tare da jan kekensa ya bar gurin.

Taja wani dogon tsuka "Mtsuwww!!!"

"Wai shikenan mutum don yana da Yayu kuma ba zai shaƙi iskar 'yanci ba? Haba wannan wacce irin rayuwa ce ina ma ace ni ce nazo babba a gidanmu." Ta faɗa a fili tare da jan ƙafarta tayi gaba tana surutai kamar wata zararra. Gidansu Hindu ta fara shiga Innarsu ta shaida mata bata gida, hakan yasa ta ƙarawa ƙafarta mai, bata tsaya ko ina ba sai Unguwarsu Malam Nura. 

Yana zaune dakalin ƙofar gidansu shi da wani abokinsa Sammani ya hangota, nan fa ya fara washe baki kamar gonar auduka, fara'ar da yake ne ya saka Sammani kallon inda yake kallo, ganin Surayyah ce ya girgiza kai har ta ƙaraso.

  "Gimbiya sarautar mata."

Malam Nura ya faɗa fuskarsa cike da annuri. Kaɗa idanuwa tayi da furta.

  "Kai kuma Sarki uban sarakuna mai mulki a faɗar birnin zuciyar Gimbiya Surayyah."

Dariya ya saka har da tafa hannu ya ce, "Lallai kam maganatuna ba dai iya tsara zance ba, ni ai naji tsoro na ɗauka Appa zai ƙara mana katangane kamar lokacin da ya cire ki a makarantar da nake koyarwa, sai kuma ga ki."

Guri ta samu ta zauna kusa da Nura shi kuwa har da ƙara matsawa ya haɗe cinyoyinsu ita kam ko a jikinta ta ce,

  "Ai ka san abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, duk duniya ai babu mai iya raba hanta da jini, idan kuwa aka raba dole sai dai duka ace rayuwar ce aka raba."

Sammani da ke gefe ya riƙe haɓa cike da mamaki yana duban Surayyah da Nura inda Nuran ya ce, "Maganarki haƙƙun tawan, amma dai Appa bai dake ki ba ko? Don tunda na taho jikina ke mini ciwo saboda nasan an duke ki, babu abin da nafi tsana a duniyar nan sama da a taɓa mini lafiyar jikinki."

Murmushin jin daɗin kalamansa tayi tare da kaɗa ido ta ce, "Kar kaji komi."

Sammani da zuwa lokacin bakinsa yake a sake saboda al'ajabi ya girgiza kai, unguwarsu ɗaya da Surayyah duk wasu rashin jinta ya sani, sannan yajawa Nura kunne a kanta amma ya yi uwar shegu da shi, sam yaƙi rabuwa da yarinyar nan sun zamewa juna kamar cingam, idan ban da ma zamani ina Surayyah ta isa ta san irin waɗannan kalaman, wai yarinya ƙanƙanuwa ta iya furta maganganu na manyan mata, sai ma wasiƙar da ya gama karantawa wacce Surayyahn ta ba Nura ɗazun da suka haɗu, maganganu da kalamai sai ka rantse wata babbar macence ta tsara su.

Malam Nura ne ya katse masa tunaninsa inda yake cewa Surayyah.

  "Naga yamma ta fara ki tashi na raka ki gida ko?"

Sai lokacin ta tuna da za taje Islamiyya fa, miƙewa tayi tana ji idan zasu kwana a haka tare da Nura ba zata taɓa ƙosawa ba, ganin ta miƙe shima tashi ya yi yana kallon Sammani da furta.

  "Abokina ina zuwa."

Sammani da ya kasa ko da furta kalma ɗaya ce ya bi su da namujiya inda suke tafiya suna hira da dariya.

Daidai kwanar gidansu yaci burki, "Surayyah bari na tsaya daga nan kar wani daga gidanku ya ganmu tare, ban san me yasa 'yan gidanku ba sa ƙaunata ba?"

"Rabu da su don Allah, ai dai ni ina ƙaunarka kuma har abada zan ci gaba da ƙaunarka, su dai suje suyi ta ƙin ƙaunar taka ai ba fito maka zai yi a goshi ba ko?"

Tana tura baki da masifa tayi maganar, Nura kam murmushi ya yi da cewa "Haka ne, to sai anjima ko?"

Gyaɗa kai tayi tare da yin kwana sai da yaga tayi nisa shima ya juya, tana zuwa ta iske ba kowa gidan, ta san dai 'yan matan gidan suna islamiyya ne, su kuwa mazan gidan wasu na kallon ball ko majalisa. Appa ma ya fita sai Innana da ke talgen tuwon dare.

Innana ta ɗago kai ta dubi Surayyah da ta shugo.

"Ina zaki yawo, ina ki ka fito yawo, wai ke Surayyah baki gajiya da yawo ne? Ɗazun nan aka dake ki a gidan nan saboda shegen yawon nan amma a banza kamar ba ke ba ko?"

Buga ƙafa tayi da cona baki tana wani ƙifta ido na rashin ji.

"To zan tare guri guda ne, ai zama guri ɗaya lalura ne Innana."

Riƙe baki tayi tana kallon Surayyah kafin ta rufe talgen da ta ida ta miƙe tsaye.

  "Salisu da ya dawo kasuwa ya ce ya ganki kin ce na aike ki ne, sannan Auwalu ya miki maganar kar ki daɗe ki dawo saboda islamiyya, amma saboda ke ja'ira ce kina faɗa mini zama guri ɗaya lalura idan kin dawo ai makaranta zaki je da 'yan'uwanki ko?"

Ɗaki take ƙoƙoƙarin shiga ta ce,

  "Nikam wai karatun nan dole ne, gaskiya ba inda zan je."

Innana ta hangame baki har ta shige ɗakinsu, cikin faɗa ta bita ɗakin.

  "Wallahi Surayyah zan ci mutumcinki, ki tashi ki shirya ki wuce islamiyya. Idan baki yi karatu yanzu ba sai yaushe?"

  "Innana na makara fa, kuma wallahi makarantar nan babu abin da suka iya sai cin zalin mutane, suyi ta dukana saboda sun tsane ni."

  "Idan da kina yin abin da 'yan'uwanki ke yi zasu tsane ki, ko Mufidah ƙanwarki ce bata abin da ki ke yi Surayyah kina abu babu natsuwa ga rashin kunya tsoranki suke ji da zasu ƙyaleki? Wallahi ki kuka da kanki a gidan nan da ko ina ma don naga abin naki ba sauƙi gaba ma yake."

Saman katifarsu ta kwanta tana motsa baki da alamar akwai abin da take cewa amma bata faɗa da ƙarfi ba. Innana cikin ɗaga murya ta kuma cewa,

  "Shin ba zaki tashi ki shirya ba ne?"

Kuka ta saki a kwancen da take.

  "Nifa ba ni da lafiya Innana ba iya zuwa zan yi ba, kuma na makara ko naje buguna kawai za ayi ba za a bari ma na shiga ajin ba."

Kuka take sosai kamar wacce aka daka. Innana tayi ƙwafa tare da fita daga ɗakin zuciyarta babu daɗi da wannan mugun taurin kan na Surayyah.

Ita kuwa tana ganin ta fita tayi shuru tare da gyara kwanciyarta tana cewa,

  "Wallahi ba zani ba, haka kawai suyi ta dukana kamar jaka don naje makarantarsu idan na daina zuwa ai sai inga wacce zasu daka, domin Surayyah dai ba jakarsu ba ce ehhen!"

Innana tacigaba da aikace-aikacenta, amma Surayyah na ɗaki ko da shara ce bata fito ta taya ta ba, da haka har ƙarfe Shidda su Mardiyyah suka dawo gidan. Lokacin Innana tana kwashe tuwo sannu da gida suka mata tare da shigewa ɗakin nasu, kwance suka iske hamshaƙiyar na bacci da yamman nan. Mardiyyah taja tsaki tana cire kaya.

Kubra ta ce, "Ke kuma ke da wa?"

Tana kuma jan wani tsakin ta ce, "Ni da banzan bazarar nan mana, kin ga bata je islamiyya ba ga ta nan kwance tana baccin wahala, 'yar wahalar."

  "Haba Mardiyyah ki daina faɗar haka, duk lalacewarta da 'yar'uwarmu ce ba yadda muka iya da ita."

  "Hmmm wallahi mu dai ba muyi sa'arta ba a gidan nan, dama ba 'yar gidan nan ba ce."

"To ya kuwa kuka iya? Ai na zamo muku ciwon ciki kuma kabewar kankabari baƙin cikin mai taushe, ya zaku iya da ni, wallahi nan gani nan bari naci dubu sai ceto."

Kamar daga sama suka ji muryarta inda ta miƙe tana wani cika da batsewa.

Kubra ta ce, "Kin ga abin da na gudar miki, domin idan ita ce bata ƙi ku kwana kuna bala'i ba."

  "Eh ɗin ai ita ce ke tonona amma da yake kema kin fi ƙaunarta a kaina ai bayanta ki ke goya, kuma ni nan Surayyah wallahi nafi ƙarfinki, tuni na san ba ƙaunata kuke ba don ba yadda kuka iya da ni ne."

Baki Kubra ta riƙe ya yin da Mardiyyah ta gama canza suturarta ta ce, 

  "Ke dai ki ka sani banzar bazara kawai, kina mace amma baki da kamun kai kowa gulmarki yake a unguwa banza jaka."

Har Mardiyyah zata fita Surayyah ta wani jawota da ƙarfi.

  "Wallahi ke ce jaka ba ni ba, kuma duk wanda bai fasa gulmata a layin nan ba uwarsa shege ta haife sa. To haushin me zanji ai ko ku da muka fito ciki ɗaya daku gulmar tawa kuke balle kuma wasu can, to abin da kake gani tun a gida mai zai sa don ka gan shi a waje ka tada hankalinka? Ni nan baki bai cina nan gani nan bari ƙwalelenku ato."

Hayaniyar da Innana ke juyowa ne ya sata maganantuwa.

  "Wai lafiya kuwa? An dawo kuma za a ɗaura daga inda aka tsaya ko?"

Mardiyyah ce ta ƙwace kanta a hannun Surayyah ta fito tana amsawa.

  "Innana daga dawowarmu waccen 'yar masifar ta fara hawa kaina kamar tana jirana."

  "Amma ai na ce miki ki daina biye mata tunda ba ragawa kowa take a gidan nan ba."

  "Ita dai ta sani duniya ce wanda bai zo ba ma jiransa take."

Nan ta fara kwashe tuwan da Innana ta gama zubawa a kwanuka wasu a tasa wasu a ƙwarya, tana shigar da su ciki. Kubra kuwa da ta fito tsintsiya ta ɗauka tana share tsakar gidan, Mufidah Auta kuwa na kusa da Innana tana taya ta ɓare maggin da take zubawa a miya. 

Dukansu da suka gama duk haramar alwala suka fara jin an fara kiraye-kirayen sallar magriba, 'yar mulkin kuwa na ɗaki hannunta ɗauke da alƙalami da faifa tana rubutawa Malam Nura wasiƙa..

Shugowar Kubra ke da wuya ta ce,

  "Ki tashi kiyi alwala ana ta haramar sallah."

Yi tayi kamar ba ta jita ba, sai da ta kuma maimaitawa sannan ta ɗago a fusace.

  "Yau ni na shiga uku! Wai ina ruwanki da sallahta ne?"

  "Akwai ruwana a ciki kam, domin tuni na miki naga baki da alamar tashi ne, sai rubuce-rubucenki na banza da wofi da ki ke."

  "Eh lallai kema Kubra waccen Mardiyyah ɗin ta fara koya miki shiga shira ba shara, ai kuwa duk zan iya da ku domin na ƙuna sai ƙauri."

Riƙe baki Kubra tayi kafin ta ce,

  "Daga gyara kayanka sai kuma ya zamo sauke mu raba? To Allah ya baki haƙuri, nikam bazan iya da bala'inki ba."

Dadduma ta fara ƙoƙarin shimfiɗawa tare da ɗaukar hijabinta ta tayar da sallah, ganin hakan bai saka Surayyah tayi shuru da bakinta ba sai masifa take.

  "Haka kawai a saka maka ido kai da gidan ubanka ba ogola ba, to ni kam gimshiƙin dutse ce wallahi duk wanda ya yi karo da ni shi ne da faɗuwa ba ni ba."

Mardiyyah da ta shugo yanzu ɗaure da alwala ta ce,

  "Magananatu har yanzu ba a shuru ba kenan? To Allah ya ƙyauta."

Da hanzari ta miƙe tana gyara zanin jikinta.

  "Eh ban yi shurun ba, kin san dai a daku ba zaki iya dukana na bari ba, wallahi sai na nakaɗa miki na jaki babu mai iya rama miki."

Maganar da Innana ta faɗa mata ɗazu ta tuna akan ta daina biyewa Surayyah, sai ita ma ta shimfiɗa dadduma tana faɗin.

  "Daɗin abin sai an kula kashi yake ɗoyi."

Surayyah komawa tayi ta zauna taso yanzu ma Mardiyyah ta biye mata domin ta dakata sai aka yi rashin sa'a, tacigaba da rubutunta tana waƙar habaici.

"_Dole a zauna da ni, ko ana so dole a zauna ko da ba a so ne dole a zauna da ni ɗirinɗin!._

Tana yi tana buga tsaki, da haka har suka idar da sallar tana ta rubutun da waƙoƙi da ta gama wannan ta ɗaura waccen duk na habaici. Basu kulata ba har aka kira isha'i suka yi ita tana zaune.

Mufidah ƙaramar ƙanwarsu ce ta shugo tana duban Surayyah ta ce,

  "Innana ta ce ta mayar miki da ruwan wankan yau zakiyi ko kar ta wahar da kanta?"

  "Mtsuww!" Taja tsaki kafin ta ce,

  "Kema dai Mufidah magulmaciyar banza ce, to don ubanki abin da ta ce shi zaki faɗa? To bazan yi wankan ba."

  "Ai kuwa yau sai dai ki kwana a ƙasan tabarma, don wallahi bazaki kwanta kusa da ni kina warin balaga ba, kusan sati guda fa kenan baki yi wanka ba Surayyah."

Mardiyyah ta faɗa a fusace tana shafa addu'a.

  "Kwana akan katifa kuwa sai nayi, tunda ta gado ce wanda ya haife ki ya haife ni kuma shi ya saya don haka ba wacce ta isa ta hana ni kwanciya akan katifa wallahi, kuma wanka ne bazan yi ba."

  "Ai kuwa yau za a yita don wallahi Yaya Salisu yazo ya raba mana gaddama yau bazaki kwana kusa da ni kina wannan warin ba."

  "Ke ce ke tsoron ko ta kwana aradu." Cewar Surayyah tana tsaki.

Mufidah ta ce, "In ce mata bazaki yi ba yau ma ko?"

  "Eh ɗin, ko zaki sakani dole ne kema algumguma ɗaya."

  "Wallahi ni ba algumguma ba ce."

Mufidah ta faɗa tare da fita daga ɗakin....

[8/3, 11:29 AM] Ummu Affan: GINSHIƘIN DUTSE...

Post a Comment

Previous Post Next Post