Alh. Nura Isma'il (Gwaska) Ya Bada Tallafin Naira 300,000 ga Hukumar Makaranta Al-hikma

Rabon Tallafin kuɗi

Alhaji Nura Ismail Gwaska, fitaccen mai taimakon jama’a a unguwar Rigasa, ya halarci bikin bayar da lambar yabo ta De-Wisdom Academy, wanda aka gudanar a Daura Road, Rigasa, Kaduna. A wani gagarumin taro da makarantar ta shirya, ya bayar da tallafin N300,000 ga mahukuntan makarantar da kuma N60,000 ga wasu zaqakuran dalibai shida da suka qayatar a harsunan Ingilishi da Larabci a lokacin bikin yaye daliban.

Malam Hussaini Salis, Daraktan Kula da Harkokin Addinin  Musulunci na Gidauniyar Alh. Nura Isma'il Gwaska, wanda ya wakilci Darakta Janar Comr. Ahmad Ashir, ya bayyana irin ayyukan tallafi da dama da Alhaji Nura Isma’il yakeyi, da suka hada da gyaran masallatai, gina magudanan ruwa, da wasu ayyukan a karkashin gidauniyarsa. Wadannan tsare-tsare na da nufin karfafawa matasa da mata ta hanyar koyon sana’o’i, samar da damar shiga Jami'a ga dalibai, da inganta harkokin wasanni a karamar hukumar Igabi.

A nasa jawabin, Alhaji Nura Ismail Gwaska bayan nuna farin cikinsa dakuma yabawa malaman makaranta yadda suke nada ilimi dakuma tarbiyya zai cigaba da bayar da goyon baya ga ci gaban ilimi a Unguwan Rigasa da Igabi da ma jihar Kaduna baki daya. Ya kuma jaddada mahimmancin ilimi wajen tsara makomar al’umma tare da yin alkawarin ci gaba da ayyukan alheri da yake yi.

Hukumar ta De-Wisdom Academy bisa godiya ta musamman ga Alhaji Nura Ismail Gwaska, sun ba shi lambar yabo ta gwaninta, tare da nuna irin daukakar da yake da shi, da goyon baya, da kuma gudunmawar da yake baiwa al’umma. An kammala bikin da addu’o’in Allah ya sakawa Alhaji Nura Ismail Gwaska bisa karamcin sa, ya kuma ci gaba da yi masa jagora a cikin ayyukan sa na alheri.

Post a Comment

Previous Post Next Post