🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON
BY
NARNAH KANWAR SOJA
💫Royal Star Association,💫
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
Page 1 & 2
Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba ,
mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya
show me some love guy's 🩷
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم
Zaman motar ya fara yi musu nauyi tun kafin su iso Yobe daga nan sai suka shiga ƙasar Chad da yamma, rana ta fara dusashewa cikin baƙin gajimare da iska mai ɗauke da ƙura gaba ɗaya zuciyar su ta fara karaya koda kuwa basu furta ba.
John ne ya fara gyara zaman sa yana duba agogon hannunsa.
"Wannan hanya wallahi kamar babu wanda ke bi ta yanzu," ya faɗa cikin ƙaramin murya
Maryam ta kama hannun Ihsan tana danne tsoro da karfin hali, "Mun riga mun fito, ai sai gaba."
Motar ta dinga kutsawa cikin kura da kankara, har aka kusa tsallaka wata ƙaramar kwazazzaba da aka samu a tsakiyar duwatsu. wani ƙara mai firgita ya tashi daga motar.
"Grrrrkkk—krrr!"
Kafin su fahimta, tayar gaba ta tsinke da wani ƙarfi motar ta faɗi gefe kamar zata tintsire Yazid ya damƙe sitiyari yana ƙoƙarin tsayar da ita amma komai ya gagara Ado ya rike bangon motar yana fadin:
"ALLAHU AKBAR!"
Sai kawai suka ji "dduuummm!", motar ta buge da wata babbar dutse, ta tsaya cak anan ne shiru ya biyo baya, babu motsi, sai sheshshekar Ihsan da Maryam suna kuka.
Yazid ya fito daga motar yana duba tayoyi, idanuwansa sun cika da 'kura. "tayar gaba da gefe duk sun ƙone clutch ɗin ma ya tarwatse. muna cikin matsala mun rasa motar mu."
John ya farka daga karyewar da ya sha, ya dubi hanya yana shan iska mai zafi, sannan yace:
"Wannan ba hanya ba ce, wannan tabo ne. mu kwashe kayanmu mu shiga cikin dajin nan idan muka tsaya nan dare zai riske mu, barayi ko dabbobi za su iya far wa."
Babu wanda ya musa kowa ya ɗauki nashi kaya cikin tsoro da damuwa. Ihsan na riƙe da kwalbar ruwa, Maryam na lulluɓe da veil tana kare jikinta daga cizo.sun fara takawa cikin ƙaton daji, cike da raɗaɗin ƙasa mai kaifi da ciyayi masu yankan ƙafa Ado na gaba yana amfani da torchlight wayarsa yana duba hanyar da zasu bi tsakar dare ne lokacin da suka hango wani tsohon baranda kamar dafa-gari. ba za a iya ce masa gida ba, amma yana da rufi da bango.
"Mu tsaya nan mu huta. Allah ya kawo safiya lafiya," Yazid ya faɗa.
Maryam ta kifa kanta a kafadar Ihsan, tana kuka cikin salo mai ciwo, "Idan na mutu a hanya ki ba baba sanina... ki ce Maryam ba ta jure tsanani ba." John ya dan murmusa cikin firgici, "Zamu mutu fa kafin mu isa Dubai idan muke tsoron hanya haka tun a Chad."a haka dare ya cigaba da raguwa, zafin rana ya mayar da dare sanyi mai shigowa jiki kowa ya kwanta da kaya a jikinsa yana jiran asuba da fata, da addu’a, da fargaba.
Dare ya yi tsayin gaske kamar zai hana wayewar gari ,sanyi ya ratsa kowane sassa na jikinsu, kowane yana neman ɗan nutsuwa da kwanciyar hankali, amma babu shi.
sai dai ƙasa mai kaifi da raɗaɗin tunani.
Asuba na ƙaratowa, Ado ya farkar da su ɗaya bayan ɗaya.
"Ku tashi, lokaci yayi... sai mu yi sallah kafin rana ta fito."
Sun fito daga barandar ruwan zufa da ƙura na hade da jikinsu. kowa ya shimfiɗa ɗan zane a ƙasa, suka gabatar da sallah da natsuwa da ƙasƙantar da kai. bayan sun idar, Yazid ya zaro ɗan kwali daga cikin jakarsa.
"Ga ruwa nan da snacks ɗin biscuit da gurasa. Amma sai mu kiyaye amfani da su, ba mu san inda zamu isa da kafafu ba."
Ihsan ta amsa kwalbar ruwa tana goge fuskarta da tissue, Maryam na gefenta, kukan jiya ya bar wani ɗan kumburi a idonta.
"Da gaske zamu ci gaba da tafiya ne?" Ta faɗa da rauni.
"Me kike tunani?" John ya juyo yana gyara jakarta. "Za mu jira motar da ba za ta zo ba? Ko barayi su zo su kwashe mu da kaya?"
hka suka kammala shiryawa, suka kwashe komai da suka iya dauka akwai leda mai ɗauke da tuwo da miya wanda suka saya kafin shiga Chad, ruwan robobi guda shida, da wasu kuɗaɗen kasar da suka musanya kafin barin Nigeria.
Ado ya latsa map ɗin da ya saukar a waya, duk da babu signal sosai, yana ƙoƙarin duba hanya mafi kusa da wata rijiya ko gari “wannan hanyar zata kaisu cikin wata ciyawa mai tsayi—amma akwai wata ma'boyar ruwa da nake tunawa da ita daga lokacin da na taba zuwa Chad.”sai suka kama hanya, dajin yana cike da tsuntsaye masu shewa, ƙasasshiyar ƙasa na sa ƙafafunsu zubar da gajiya. Ciyayi na yanka ƙafafun su, ganyaye na goce su a fuska.
Yazid ya riƙe jakar abinci yana gaba, John na gefe yana duba kowane motsi, kamar soja na sahun fama. Maryam na tsakiyar Ihsan da Ado, amma ita ce ta fi fitar da kuka.
"Gsky, idan Dubai ne zai kashe mu haka, to wallahi zan koma gida."
"To sai a auri tsoho, ko?" Ihsan ta harare ta cikin dariya mai taɓarɓarewa.
Maryam ta kyalkyale da dariya cikin hawaye" ke Ihsan wallahi da aure Baba audu gwanda na mutu a hanyar nan"
Sun dauki kusan awa biyu suna tafiya cikin daji kafin suka kai ga wani tabo mai ɗan sanyi, kamar ruwan fanfo ya ƙyalƙyala sama, suka zauna a can suka sha ruwa suka ci ɗan abu.
Yazid ya duba agogon sa. "Zamu ci gaba da tafiya bayan minti talatin... don kada rana ta fara zafi mu gaji."
Cikin wannan rana, sun fara fahimtar cewa tafiyar nan ba zango ba ce, ba yawon shaƙatawa ba ce hanya ce ta ƙalubale da jarumta, da fahimtar juna. Kuma suna cikin ita....
Garin da suka zauna sun ɗan ji sanyi da natsuwa bai kai awa biyu ba, sai ga wani ƙara ya karad'e sararin samaniya. wani irin hadari ne ke tasowa daga gabashin jeji, ganye na yaye sama, ciyayi na karyewa, iska na tashi da kura mai kauri "Na shiga uku! wannan fa kamar guguwar jeji ce!" Ado ya faɗa yana rintse ido "Ku tattara kayan nan! Ku kamo jakunkunan ku!" Yazid ya ɗaga murya.
Cikin daƙilewar lokaci suka fara tattare kayan su, Maryam ta faɗi jakar ruwa, sai kuma aka jiyo busa kamar karar motar iska tana fashewa wata bishiya ta karye tana gangarowa da sauri!
John ya ɗago Maryam da sauri suka fice daga wajen,kowa ya rikice.ƙasa ta ɗan girgiza, sai ƙara da kuma wata shanya mai ɗauke da ganye da ƙasa ta tashi ta rufe hanya.
"Wayyo Allah na! kayi mana sauƙi!" Ihsan ta yi ihu.
Kowa da nashi, sai suka gudu sun rarrabu kadan, amma a ƙarshe suka taru bayan sun kusan rasa juna. tafe suke da keɓaɓɓen numfashi, zuciya cike da tsoro da gajiya, bayan tafiya mai nisa da hawan ƙasa da tsallake kwari, sai suka hangi wani ƙauye a can gefe da daji. wurin tamkar ya zauna a gaban dutse ne, akwai ɗan ruwa yana kwarara daga wani ƙanƙanin dutse.
Ado ya saki numfashi. "Wannan tamkar lahira muka tsira daga ciki muka dawo duniya ne wallahi."Yazid ya yi dariya. "Kai dai karka fara wahalar da mu da falsafa yanzu shin ka taɓa zuwa lahira ne."
Ihsan ta tura masa kafa, "Wai yanzu ni dai idan na nitsu zan rubutta wanan hargitsen cikin wannan littafin domin tarihi sai na rubuta wani Irin Jeji da na shiga."suka tafi da dariya, duk da gajiya ta cika jiki.
Sun isa ƙauyen, mutanen gari suka karɓe su da jinkai, suna ba su ruwa da wuri su huta. Sun zauna suka ci abu kaɗan, suka kwanta ƙarƙashin inuwa, Ihsan na kwance a gefe ta ce, "Wallahi idan na isa Dubai, zan fara kasuwancin ganyen magarya na gaji da dogon buri."dariyar su tashi, kowa ya ƙwalla dariya mai sa hawayen idanu.
Bayan hutu da shan ruwa, suka sake tashi da niyyar cigaba da tafiya gobe da safe. kamar ba suba, suna dariya, suna kwance da juna kamar ƴan uwa, daga cikin hargitsi da wahala, nishad'i ya fara zame musu masoyi.
Kwanaki sun shige suna lissafa wa cikin jeji da ƙasa marar alamar birni, bayan haɗari da suka fuskanta, motar su ta hantsila a ƙasar Jamhuriyar Chad, suka kasa gyara ta, sai suka bar ta can da ƙyallen tarihi suka fara tafe da ƙafa, kamar masu hijira daga duniya zuwa mafarki.tun daga lokacin ne suka soma 'kulla wani ɗaurewa da ba wai jinƙai kaɗai ba, amma kamar ana zuba wani zuma a zukatansu, suka zama kamar ƴan uwa da aka haifa daga ciki guda.
Maryam, mai natsuwa da laushin murya, ita ce jinyar jikin su duk sanda ciwon tafiya ya kama daya, za ta tsaya ta fidda ƙananan kayan asibiti daga cikin jakar matafiyar ta—ta fiddo da tawul, ta sha da ruwa, ta gyara bandage. Ita ce ta fi sanin yadda ake shafe jiki da ganyen da suka ci karo da shi a hanya domin rage raɗaɗi.
Ihsan kuwa ta fara zama ƙawarta ta gaskiya. su biyu idan suka haɗu sai dariya da tsokana, suna ƙoƙarin mantar da sauran wahala. Ihsan da bakinta mai ɗaukar dariya, ita ce ke ba su nishadi, tare da Yazid wanda kullum da sabuwar waka a bakinsa. Yazid na iya busa leda da furar baki har kowa ya manta da gajiyar tafiya.
John, babban mutumin da ke ɗauke da baƙin laya a wuyansa, shi ke gaba da su a koda yaushe ƙarfin jikinsa da jajircewarsa ke kare su daga tsoron jeji da dabbobi. Idan dare ya fado, John ne ke ɗebo itace, yana hura wuta, yana saka su su ji kamar gida suke ciki.
Ado, ƙwararren masanin hanya, shi ke tsara hanya. Duk sanda suka tsaya yana fiddo taswira ko yana duba taurari da rana don sanin gabas da yamma,baya cika surutu, amma idan ya buɗe baki, kalmarsa zata zama haske.
A daren da abinci ya ƙare, sukayi shiru gaba ɗaya. ba kowa da bakin magana sai ƙarar cikin da ke ɗaukar wululu. Maryam ta rufe idonta da ƙirjinta, tana share hawayen da ba kowa ya gani ba. zai dai Ihsan ta ɗan matsa kusa da Yazid, suka fara raira waka:
"A cikin duhu akwai fata,
A cikin yunwa akwai madara,
Rana ta fito daga bayan wata..."
John ya sa dariya, ya ce:
"Kun sani, idan muka tsira daga wannan tafiyar, zaku fi daraja fiye da zinariya a gare ni."
Ado ya duba sama, yana murmushi da ƙyamshi, sannan ya ce:
"Idan muka kai Libya lafiya, zan gaya muku sirrin da ya sa na bar gida."
John ya ɗago kansa, ya ce:
"To, mu haɗa zuciyarmu." suka kama tare da muryar da ke daɗi ga kunne, duk da gajiya da yunwa, suka rera:
Bayan wata akwai dare,
Bayan dare akwai haske,
Bayan yunwa akwai cika,
Bayan hawaye akwai dariya.
Idan rana ta ɓuya,
Mun san wata zai leƙo,
Idan hanya ta dushe,
Mun san ƙafafunmu zasu kai.
Bamu daina ba, bamu ja baya ba,
Zamu cigaba har gobe ta zo.
Mu da juna, zuciya ɗaya,
Rana ta fito daga bayan wata"…
Yayinda suka rufe baitin ƙarshe, wutar da John ya kunna ta ƙara walƙiya, kamar yadda wata ke ɗaukaka cikin dare.
Tun daga wannan daren, wannan waƙa ta zama taken tafiyarsu duk sanda sun gaji, ko dare ya musu tsayi, ko cikin su ya fara kuka, sai daya daga cikinsu ya fara:
> “Bayan wata…”
sauran su kuwa sai su ɗaga murya cikin amsa, kamar ruwa da tsuntsu:
“…akwai dare… bayan dare akwai haske…”
suna shiga cikin sabuwar rana da sabuwar fata.
continued..... narnah ƙanwar soja ✍️