Tsantsar Ƙauna – Kashi na 9
Biki ya rage saura kwana biyu, An kammala shirye-shirye tsaf, har gidan da zasu zauna sun samu, Kowa ya san za a ɗaura auren Fatima da Kamal masoyan da soyayyarsu ta girma daga ƙuruciya har ta kai ga aure.
Yayin da limamin masallaci ke ɗaura auren a gaban manyan maza, Kamal sanya manyan kaya fari sun sha aiki sosai daga ka ganshi ka ga ango, abokansa kuwa sun kewaye shi yan'uwa da abokan arziki sun cika Unguwa, zuciyar Kamal ta cika da farin ciki bakin shi kuwa taki rufewa. Kamal ya biya sadakin auren Fatima Naira 300,000.
“Na karɓi aurenta… da sadaki naira 300,000i,” in ji limamin, Wakilin Kamal ya amsa cikin murya mai ƙarfi:
“Na amsa.”
Sai aka ɗaga hannaye da addu’a. “Allah Ya sa albarka.”
A can bangaren mata kuwa, Fatima ta sha kwalliya cikin rigar amarya, fuskarta cike da annuri da jin dadi. Mahaifiyarta da yayyunta na zagaye da ita suna tayata murna. A lokacin da aka sanar da ita cewa an ɗaura auren ta da Kamal, ta saki murmushi da hawaye suka gangaro daga idonta.
Ta ce a hankali, kamar tana magana da zuciyarta:
“Godiya nake wa Allah. Kamal ya zama mijina. Wannan soyayya yanzu ta zama aure, ta zama tarihi.”
Ana idar da ɗaurin aure, yan uwa da abokan arziƙi suna ta taya shi murnar, Kamal yana neman dama ne ya kira Fatima, lokacin da abokai da baƙin sa ke cin abinci a inda aka ajiye su don xin abinci, nan ne ya sami daman kiran ta a waya
"Assalamu alaikum, Amaryata," Fatima kasa amsawa yayi saboda tana cikin mutane da yan uwanta, na fita daga cikin mutane, a taƙaice sukayi wayar saboda mutane.
Da yamma aka shirya walima mutane sun cika sosai, inda Malamai daban-daban sukayi bayani kan zamantakewar aure, sai muce Alhamdulillah, an ci an sha sosai a wajen walimar.
Biki ya ci gaba da gudana cikin farin ciki da dariya. An ci abinci, an sha hula. Abokai da ‘yan uwa sun zo daga ko’ina. Wata yarinya daga makwabtan gida ta ce:
"Ki ji tsoron Allah yanzu Kamal ya zama mijin ki yanzu ya fi mu iko dake, ina da yaƙinin Kamal zai kula da ke kamar yadda muke kula dake a nan, dan Allah kada ki bamu kunya, ba ruwanki da wayarsa, banda sa ido a al'amuransa, duk abinda zakiyi ki faɗa masa, banda ɗaukar gulma, banda ɗauka shawarar banza daga ƙawaye, aure ibada ne kada ki ga yanzu kuna soyayya ba waje ɗaya kuke ba, yanzu ne zaku zauna a waje ɗaya, sai Kinyi ta hakuri, Allah ya zaunar da ku lafiya" mahaifiyar Fatima ce da yan uwanta sukayi ta mat nasiha mai ratsa jiki, Fatima kuwa banda kuka ba abinda takeyi. Shima Mahaifinta yayi mata nasiha sosai. An gama yi mata nasiha daga nan aka ɗauki Fatima sai gidan Kamal.
A can ma da aka kai ta sunyi ta mata faɗa da ta ji tsoron Allah, nan iyaye suka tafi aka bar Fatima tare da ƙawaye ta guda biyar.
Misalin ƙarfe 9 na dare abokan ango suka rako ango, bayan sun shigo aka sallami ƙawaye nan suma suka yi ta bashi shawara da faɗa don ya riƙe ta amana, sun daɗe don har karfe 10 suka kai, daga nan kowa ya kama kanshi.
Bayan kowa ya watse an bar Fatima da angonta Kamal, suka gabatar da ibada yadda addinin Musulunci ya tanadar, "Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicci duniya d abinda ke cikin ta, wanda ya halicci Fatima ya Kuma kawo mu wannan lokaci d ta zama mata ta" Kamal ne ya fadi haka yayin da yake kallon Fatima wanda kan ta ke ƙasa.
Nima sai nace Alhamdulillah anan zan tsaya a kashi na tara sai mun haɗu a kashi na 10, a taimaka a yi mana sharing.