Tsantsar Ƙauna – Kashi na Takwas
Tun Bayan saka ranar Kamal da Fatima, ko wanne gida suka fara shirye-shiryen biki sakamakon saka bikin da akayi wata biyu mahaifiyar zauna da yan uwanta sun siya kayayyakin auren Fatima da yawa.
Washegari, an fara tattauna kan lokacin da za a yi gaisuwar iyaye, da kuma sauran shirye-shiryen al’ada da za su biyo baya. Kamal da Fatima sun zauna su biyu a gaban gidan, suna tattaunawa.
“Fatima, kin fi duk wata kyauta da nake tsammanin samu a rayuwa. Amma yanzu akwai aiki a gaba, mu shirya.”
Ta yi murmushi ta ce: “Na sani, soyayya da aure ba wasa ba ne.”
Biki ya rage saura sati Uku, Kamal ya fara neman abokai da dangi domin ɗaukar nauyin dukkanin abubuwan da al’ada ta tanada. Yana tuntuɓar mai ɗinki don kaya, a wannan lokacin kuwa ya gama haɗa lefe da abubuwan da za su dace da mutuncin Fatima da danginta.
A bangaren Fatima, Mahaifiyar ta da yayyunta sun gama haɗa duk wani abu da ya kamata ace anyi ma yarinya idan za tayi aure, sai dai abinda ba'a rasawa.
Kamal da Fatima suka cigaba da rubuta labarinsu cikin kulawa da tausayi. Sun daina ɓoye soyayyarsu, domin yanzu ta zama abin alfahari da ake wa kallo da koyi.
A wani dare, bayan sun gama waya da juna, Fatima ta zauna a gefen gado tana tunani. Idanunta na cike da farin ciki. Ta ce a ranta:
“Wannan ba mafarki ba ne. Kamal na gaske ne. Kuma ni ce zan zama matar Kamal.”
Laifin daɗi ƙarewa. Mu haɗu a kashi na Tara.