Tsantsar Kauna Page 10 - Abokiyar Hira Novels

Abokiyar Hira Hausa Novels

Tsantsar Kauna – Kashi na 10


Na 

Tahir Yusuf (Novels Elite)


Rayuwa ta fara sabuwa ga Kamal da Fatima. Bayan kwana uku da ɗaurin aure, suka gidan su karamin gida ne mai ɗaki biyu da falo, amma yana cike da kwanciyar hankali da farin ciki.


Fatima ta fara sabuwar rayuwa cikin tsari. Duk da cewa ta saba da gidan iyayenta, ta kama sabuwar hanya da zuciyar da ke cike da ƙaunar Kamal Kowace safiya, sai ta tashi da shirin girki da gyaran gida, tana fuskantar Kamal da murmushi mai cike da soyayya da kulawa.


Kamal kuwa, ko da ya fita aiki, ba ya manta da kiranta ko turo saƙon soyayya:

“Amaryata, ko sau ɗaya ba zan gaji da furta miki ina son ki ba.”


Sai dai kamar yadda kowace rayuwar aure ke cike da jin daɗi da farin ciki, haka take da ƙalubalenta. Bayan wat biyu, Kamal ya shiga cikin wani yanayin aiki da ke buƙatar karin lokaci a ofis. Yakan dawo dare, Saboda aikin da ya samu a a gidan Radio, mafi yawan lokuta a gajiye yake dawowa gida, wani lokacin ko iya ɗaukar dogon lokaci don tattaunawa da Fatima kamar yadda sukeyi da baya iya wa, saboda yana buƙatar biyu.


Yanayin halin aikin da yake yi ma Kamal ya tsinci kansa hakan yasa Fatima ta fara jin wani canji a cikin Zuciyarsa Sai ta fara zargin ko Kamal yana canza hali ne, Amma ta tuna da kalmomin da ya faɗa mata tun farko:

"Zan kasance tare dake ke har tsawon rayuwata, ke kaɗai nake so." Hakan yana tasiri sosai a zuciyar Fatima sai ji hankalinta ya kwanta.


Wata rana da dare, ta kalle shi bayan ya gama cin abinci da yake ranar Kamal bashi da aiki, ta kalle shi cikin nutsuwa tace, 

“Kamal, ban damu da kudi ko kaya ba. Amma kada ka bari nisan lokaci ya kashe jin daɗin zuciyata.”


Kamal ya kalleta, ya kama hannunta. “Ki gafarce ni Fatima. Rayuwa tana so ta ja ni nesa, amma ki tuna da cewa, ko da yaushe kece a cikin Zuciyata. Kiyi ta haƙuri in sha Allah watarana sai lsbari, 


Tun daga wannan daren, Kamal ya ƙara kulawa da da Fatima, yana barin wajen aiki da wuri, yana dawowa gida, domin faranta ran Fatima.


Fatima ta cigaba da jurewa da fahimta. nan ne ta gane amfanin haƙurin da ake bata a gida. Ta rungumi ƙalubale da ƙauna, ta cigaba da safiyar da rayuwar aurenta da haƙuri da addu’a.


Washegari, suna zaune suna shan shayi a cikin falo, Fatima ta ce masa:

“Na fahimci cewa soyayya ba ita kaɗai ke ɗaukar gida ba sai da fahimta, addu’a da yarda.”


Kamal ya ce:

“wannan shi ake kira da rayuwar aure, watarana aji daɗi watarana kuwa kaga kamar ba auren soyayya akayi ba.”

Sannu a sannu lokaci na tafiya, auren Kamal da Fatima ya kai tsawon wata 7, haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa, wani lokacin ayi farin ciki, wani lokacin kuma sai haƙuri. Dama haka rayuwar take ko ga irin mu da bamu da mata wani lokacin zaka tsinki kanka cikin farin ciki wani lokacin kuma akasin hakan.


Sai mun haɗu a kashi na 11 kada a manta ayi mana sharing pls.

Post a Comment

Previous Post Next Post