Tsantsar Ƙauna – Kashi na Bakwai
Na
Tahir Yusuf (Novels Elite)
Washegari da safe, kafin rana ba ta fito sosai, zuciyar Kamal ta yi haske fiye da kowanne lokaci. Ya fito daga ɗakinsa sanye da rigar T-shirt mai sauƙi da wando shuɗi, yana ta murmushi kamar wanda ya ci gasar soyayya. Wayarsa ce a hannunsa, yana dubawa lokaci lokaci, ko Fatima ta aiko da saƙo ko ta kira.
Yayin da yake tafiya zuwa zauren gida, mahaifiyarsa Hajiya Zainab ta dubi fuskarsa ta ce:
“Kai Kamal, yau naga yanayin ka ya canja, wannan farin cikin dake fuskar ka fa. Me ke faruwa?”
Kamal ya tsaya yana kallonta da murmushi. “Maman, na yanke shawara. Lokaci ya yi da zan da ya kamata ayi maganar aurena da Fatima gudun kada na rasa ta.”
Hajiya Zainab ta dan taɓe baki da murmushi. “Ai tunda Fatima ce, ba komai bari Malam ya dawo sai muyi magana da shi ni, daga ɓangarena ba damuwa na amince. Allah Ya sanya alkhairi.”
Da wannan, Kamal ya tafi don zuwa wajen abokansa don tattaunawa game da aure da da fatima.
A bangaren Fatima kuwa tun da ta tashi tayi wanka ta sanya kaya, atamfa ce doguwar riga, yadda rigar da zauna a jikinta kai kace a jikin nata aka dinka kayan. Turare ta ɗauke ta fesa a duk inda ya kamata ko'ina cikin ɗakin ƙamshin turare yakeyi, zuciyarta cike da kwanciyar hankali da ƙaunar da take jin ta ƙara girma, wayar ta da ɗauko ta kira Kamal "Assalamu alaikum, Masoyi ina kwana, fatan ka tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau" Kamal ne ya amsa cikin murya mai cike da soyayya.
Da shagwaɓar ta tace "Yaushe zaka zo?"
"In Sha Allah nan bada komawa ba zan zo, ina wajen abokan na ne."
Da haka sukayi Sallama Fatima da Kamal.
Misalin ƙarfe 11:15am wayar Fatima ce ta fara ruri wanda tuni ta san wanda ke kira, domin kuwa ƙarar saurin kiransa daban ta saka masa. "Babe ka iso, to gani nan zuwa."
Kamal na tsaye a waje jikin wata bishiya dake ƙofar gidan su Fatima, nan ta dame shi suka tattauna batun auren su.
Tun bayan fitar Kamal gida Mahaifinsa Malam Umar ya dawo daga inda ya tafi, mahaifiyar Kamal ta faɗa masa komai game da neman auren Kama.
"Indai haka ne wannan ai abin farin ciki ne tunda har ta iya tunanin ya nemi aure kina yayi hankali kenan, ga yarinyar da yake so yar makwabci na, idan ya dawo kice ina son ganinsa.
"Assalamu alaikum" Kamal ne yayi sallama a ƙofar ɗakin mahaifinsa. Aka amsa ya shiga cikin ladabi ya gaida mahaifinsa. Malam Umar ya gyara zama ya kalli Kamal da kyau, ya ce: naji duk abinda ke faruwa, in sha Allah zan kira Kaduna ka sai mu sami Malam Abubakar mu tsayar da magana. Ka faɗa ma Fatima ta fyi magana zamu zo gobe da safe in Sha Allah " da haka suka gama tattaunawa Kamal ya fita.
Zuwa sa daki ke da wuyaya ɗaga waya ya kira Fatima ya kwashe labarin duk yadda sukayi da mahaifinsa, cikin farin ciki mara adadi tace. "Alhamdulillah! In sha Allah yanzu zan je na sanar dashi." Bayan sun gama waya, Fatima ta nufi ɗakin mahaifiyar ta domin isar da sakon gidan su Kamal. "Kwana biyu na kasa gane mene faruwa ne, wannan fuskar taki akwai magana ko?"
Fatima: "Eh Mama"
Tace "ya akayi"
Fatima ta rufe fuskarta da hannunta tare da sunkuyar da kan ta ƙasa "Dama Kamal ne yace iyanensa zasu zo gobe"
"Masha Allah, bari nake na faɗa ma Alhaji."
Cikin falo ta same shi yana zaune ta isar da saƙon. Shima Malam Abubakar ya kira yan uwansa ya sanar dasu.
Washe gari da safe aka saka ranar Auren Fatima da Kamal wata biyu.
Zuciyar Kamal ta cika da farin ciki, Fatima kuwa, idonta ya cika da ƙwalla ba na baƙin ciki ba, amma na farin ciki na cikar burinta.
Nan zamu tsaya sai mun haɗu a kashi na takwas.