Tsantsar Kauna Page 31 - Abokiyar Hira

Kalbim Mamugee, Zafafa 5

 Tsantsar Kauna 

Page 31

Written by Tahir Yusuf (Novels Elite)


A firgice Maryam ta tashi, ba abinda take yi sai salati da karanta wasu ayoyi daga cikin Qur'ani na neman tsari daga sheɗanu. Waya ta ɗauko domin ganin lokaci, karfe 2:30 da rabi me na dare.


Ta sake kwanciya domin yin bacci amma idon ta babu bacci ko kaɗan, ban ɗaki kawai ta wuce, alwala ta gabatar ta dawo ɗaki, Sallah raka'a biyu tayi tare da roƙon Allah yasa wannan mafarkin nata ba wani abu ne ke shirin faruwa ba. 


Kur'ani ta ɗauko ta cigaba da karatu sakamakon baccin da ya ƙaurace ma idon ta. Aka bacci ɓarawo, Maryam bata san lokacin da bacci ya ɗauke ta ba, Muryar Auntyn ta Walima taji kamar daga sama tana cewa 


"Maryam yau lafiya kuwa,kin san ƙarfe nawa ne yanzu baki bacci da wuri ba kina chat har dare yayi ko."


"Wallahi ba haka bane Adda Walima"


"Yanzu haka ko Sallah baki ba"


"Eh, ban yi ba"


"To ki tashi ki Sallah lokaci ma ya ƙure don yanzu har 9am tayi, kuma idan kin gama ki zo ina son ganin ki"


"To shikenan"


Ibrahim kuwa iyayen Maryam ya kira yace yana son zuwa akwai magana mai muhimmanci sosai, ya faɗa masu duk yadda akayi kan wanda ke neman auren Maryam da kuma yadda yake mu'amala da mutane.


GIDAN KAMAL

Bayan na gama shiryawa na tarar da Fatima a farko tayi tagumin kamar akwai abinda ke damun ta "Fatima me ke damu ki naga yau yanayin ki ya canja, lafiya kuwa."


"Lafiya ƙalau kawai dai gaba na ne ke faɗi, sai wani irin tsoro da nake ji"


"Ki samu ki sadaka in sha Allah babu abinda zai faru, babu abinda yafi ƙarfin Allah."


"Shikenan Baban Affan"


"Ni zan fita yanzu ina da wani aiki da zamuyi a office Ni da Abdullahi"


"Allah ya kiyaye hanya, Allah ya ƙara buɗi, Allah y ƙara tsare min kai ya raba ka da sharrin mau sharri, Ya kuma raba ka da sharrin masu hassada"


"Amin Nagode Maman Affan, ki dage da addu'a dai kada ki dinga wasa da adhkar."


Ban fita ba sai da na tabbatar hankalin Fatima ya kwanta natsuwa ta zo mata, sannan na fita. Gidan Abdullahi kawai na wuce ya shirya tuntuni Ni kawai yake jira, wayar sa kawai na kira saboda kada n shiga mu zauna fira.


Bai dade ba ya fito ya shiga Mota Muka wuce wajen aiki.


Kiran Fatima na gani a wayar ta, "Lafiya kuwa Fatima irin wannan kira haka"


Ba tare d ɓata lokaci ba na ɗauka 


"Assalamu alaikum "

Na amsa da "Wa'alakumussalam, Lafiya kuwa?


"Lafiya Lau na manta ban tambaye ka ba ina so zan je gidan mu na gushe su"


"To shikenan idan kin je ki jira idan n taso zan zo n ɗauke ki, ki gaida su idan ki tafi"


Ta yanke wayar mu ka cigaba da hira Ni da Abdullahi, kafin wani mai Adaidaita sahu ya shigo wannan da ba. Ƙarar burkina da na taka ne ya dawo da hankalin kowa dake kan junction ɗin kan mu, jikina babu inda baya rawa amma Abdullahi ya fini tsorata, ko magana ya kasa.


Kafin kace kwabo mutane sun taru a wajen Allah ma ya tsare bai taɓa shi ba, sakamakon birnin da ya taka, fitilar motar ne kawai guda ɗaya ya fashe, haƙuri kawai mutane ke bani saboda ba laifina bane na mai Adaidaitan ne da ya shigo ba tare da ya duba hanya da kyau ba.


Jikina yayi sanyi sosai domin irin tsaratar da nayi, tun daga wannan lokaci har muka isa office babu wanda ya sake iya cewa komai, sai dai ya kalle Ni Nima na kalleshi.


Karfe 1:23pm na rana Fatima ta isa gidan su tayi sallama ta shiga, Hajiya Rabi ta samu a falo zaune tana, ta ajiye jakar da ke riƙe a hannunta sannan ta sauke Affan wanda ke fiye a baya.


Hajiya Rabi ta miƙa hannu da niyyar ta ɗauke shi amma dai ya ƙara maƙalewa a jikin Fatima alamun ƙyuya, "wani irin miji ne wannan me gudun matarsa, baka san kayi cefane shiyasa kake gudun matar taka ko" tna Magana tana masa wasa amma ko kula ta ma baiyi ba, sai wani maƙalewa da ya sake yi a jikin Fatima.

Fatima ta gaida Hajiya Rabi, sannan suka cigaba da hirarsu inda Hajiya Rabi ta kalli Fatima ta ce "Ni kam Fatima lafiya kuwa, naga kin canja, yanayin ki ya sauya sosai."


"Babu komai, Mama kawai wani lokacin ne sai Mani gabana na faɗi ko haka kawai naji na firgita"


"Kina Addu'a kuwa, da Adhkar na safe da yamma?


"Ina yi kullum, har Affan ina yi masa."


"Ki cigaba da yi kuma in so samu ne ko yawaita sadaka, koda wani abu zai faru dake zai zo da sauƙi in sha Allah"

"In Sha Allah, zan yi ko Baban Affan ma abinda ya faɗa min kenan" haka suka cigaba da hirarsu na 'ya da Uwar.

Don jin me zai faru gaba ku biyo mu a kashi na 32

Kada a manta ayi sharing, like Comment sannan ayi following ɗin mu.


Post a Comment

Previous Post Next Post