Randar Cikin Daka page 9-10

Randar Cikin Daka

RANDAR CIKIN ƊAKA...

©UMMU AFFAN

Page 9-10

Hasken da ya haskaka fuskarta ne yasa ta sakin miƙa tare da wata doguwar hamma. Mutsittsike idanuwanta tayi ganin hasken ranar da ya dallo ta wundon ɗakinta. A gigice ta duro daga kan gado ta juyar da fuskarta ga agwogo ƙarfe sha ɗaya na safe.

"Kai! Taya bacci ya kaini har wannan lokacin?" Ta tambayi kanta, inda ya kwanta ta duba babu shi ba alamarsa, numfashi ta sauke tare da shiga toilet, alwala ta ɗauro nazo tayi sallah a lokacin, wayarta ta jawo tana ƙara jan doguwar hamma. Saƙon Yaya Mz da taga ya turo mata ta fara buɗewa.

  _Idan kin tashi daga baccin asarar ni na wuce Office, kuma jiya ya zama rana ta ƙarshe da zan ƙara ganin irin wannan girkin. Sannan Nihlah bata da lafiya ki shiga ki gaisheta._

"Chafɗijam!" Ta furta a bayyane kafin ta ce"Rashin lafiya, gaisheta, lallai ma yarinyar nan ubanwa zata rainawa hankali?'' Ta kuma tambayar kanta a fusace kafin ta miƙe cikin fushi ta nufi ɗakin Nihlah, ko da ta shiga ta isketa rufe da bargo tana bacci. Har zata tasheta sai kuma ta fasa parlour ta dawo tana bala'i ita kaɗai kamar zata ci babu. Wajajen sha biyu Yaya Md ya shugo, sannu ta mishi tare da gaishe shi da sauri don tasan baya ɗaukar raini. Tana gurin ya shiga ɗaki har ya fito. Haka dawowarsa da magani a leda. Yana shiga taja wata uwar ashar, ganin yazo ya shiga kitchen ya dawo da buredi a hannu nan ma ta riƙe baki. "Wallahi sai Umma taji wannan zance, kar dai ace ciki ne da Nihlah." Ƙirjinta na bugawa ta kira lambar Umma wacce bugu biyu ta ɗauki wayar..

"Amal fatan dai shirinmu na safe ya tafi yadda ake so?"

 Cikin sauri ta ce,

 "Bar wannan zance Umma, ai Nihlah ce ba lafiya ina fa tunanin ciki ne da ita."

 "Ciki!!!" Ta faɗa cikin ƙara don har sai da Amal ta janye wayar a kunne ta kuma maidawa.

 "Haka nake tunani, kuma baki ga yadda Yah Md ya ruɗe ba sai wahala fa yake mata ni abin ma tsoro ya ba ni."

 Ki bari ina zuwa. Ƙit Umma ta katse wayar tana zan numfashin tashin hankali. A fili ta furta "Wallahi bazata saɓu ba wai bundiga a ruwa. Nihlah ciki ai ke da haihuwa kam sai dai ki ga sauran mata nayi a gidajensu, yadda uwarki ke guda ta haifa ke ɗinma da ƙyar Allah yasa ma rayuwarki da na tsawo ne, amma ke kuwa kin bar ganin ƙwanki a duniya Amal ma ta samu ciki ba sai ke haɗamamma?" Juyi take a ɗakin kafin ta tsaya chak! "Kai taya ma ta sami cikin bayan anyi aiki ta yadda Mudasseer ba zai taɓa iya kusantarta ba?" Da sauri ta ɗauki wayarta tare da kiran Farrah. Har ta katse bata ɗauka ba sai a kira na huɗu da Umma tayi mata.

  "Umma irin wannan kira haka, bacci fa nake kina damuna da kira, kin san ban cika san ƙara ba."

 "Allah ya baki haƙuri 'yata, kiran ne yazo a bakatatan. Ko kin san Nihlah na da ciki kuwa?"

  "What?" Farrah ta furta wacce ta wuntsulo daga gadon da take kwance. Nan take ta miƙe tsaye.

  "Umma kin san me kike faɗa kuwa? Nihlah ke da ciki bayan ko hannunta ban bawa Dear damar riƙewa ba? To wallahi idan har ciki ne da ita tun wuri ku nemi ubansa, zan iya kassara yarinyar nan fa." Ta ƙarashe cikin fushi kafin ta ɗaura a fusace.

  "Yarinyar nan ta rusa mini duk wani tanadi da jin daɗina, ta rusa ni da rusa mijina ta ɗaiɗaita mini rayuwar 'ya'yana, tunda ta shugo rayuwarmu muke fuskantar ƙalulabale wallahi idan ta kuskura ta sami ciki da mijina sai na kashe ta!!" 

 Umma tabi wayar da kallo bayan Farrah ta datse kiran. murmushi ne ɗauke a fuskarta kafin ta ce "Daman haka nake so, gama mata aiki fara mai farar aniya Farrah uwargidan ɗana Mudasseer." Hahhahhahhahhahh ta saki dariya tare da kums kiran Amal wacce ke faman zagaye parlourn tana tunani, tana gurin har Yah Md ya fito ya wuce kasuwa. Yana fita Umma na kiran wayarta..

"Umma ke nake ta jira naji me zaki ce."

 Dariya Umman tayi mai sauti kafin ta ce"Komi ma zanyi Amal, amma yanzu mu jira muga hukuncin da Farrah zata fara kafin muyi namu. Alƙawari ne fa na ɗaukarwa kaina ba Huraira ba hatta 'yarta Nihlah sai naga ƙarshenta, wallahi jin daɗi dai na gidan duniya sun bar samun sa, da ni suke zancen."

 Ajiyar zuciya Amal ta saki tare da furta "Har naji sanyi Umma, amma idan Nihlah ta rigani haihuwa ai na kaɗe, wallahi na tsaneta tsana mai muni. Ko ganinta bana son yi a duniyar nan don dai ba ni da yadda zanyi ne, tun farkon tasowarmu komi ace Nihlah haka a school duk ƙyauta ita ke samu, sai da kika hanata karatu hankalina ya kwanta wallahi na tsaneta."

 "Ki kwantar da hankalinki Amal Nihlah ko ɓari bazata taɓa ba balle haihuwa."

 Da wannan zancen sukayi sallama, nan Amal ta duƙa sakin murmushi ranta ya mata wasai.

Nihlah pov.

Lokacin da na farka Alhamdulillah jikina naji sauƙinsa sosai. Sakkowa nayi daga saman gadon na shiga toilet, nan take wanka nayi don naji daɗin jikin nawa kafin na ɗaura alwala da na gama wankan, fitowa nayi na shirya cikin riga da siket na atamfa kafin na gabatar da sallah bayan na saka hijabina. Na daɗe zaune ina azkar har zuwa lokacin da naji sallar la'asar domin wajajen uku na farko daga baccin nawa. Bayan na idar da sallar la'asar ɗin addu'o'ina nayi kafin na nunnuke dadduna da hijabin na ajiye su ma'ajiyarsu, har na doshi ƙofa zanyi kitchen na tuno da gargaɗin Amal akan kitchen ɗin, ɗan jim nayi kafin zuciyata ta yanke mini naje. Bata parlour hakan ya bani damar wucewa direct, Tunani na fara akan abu mai sauƙi da zan tafa, bana sha'awar cin indomie hakan yasa na fara ƙoƙarin girka Makroni, a hankali nake yin komi domin bana so Amal ta jiyo ni har tazo taci mutuncina, nayi sa'ar kammalawa a kitchen ɗin na sami guri na zauna naci har na ƙoshi, sanin Yah Md ba gidana yake ba yasa yau banyi tunanin masa girki ba, daman rabi na dafa ragowar na juye a ƙaramar kula na wanke duk abin da na ɓata, duk da kitchen ɗin a yamutse na same shi banbi takan komi ba don bana ƙaunar tujarar da Amal ke mini duk da ni tsararta ce da kaɗan ta girme ni amma tsoranta nake ji matuƙa, hakan na da nasaba da yadda muka taso tun muna gida. 

 Fitowata kenan mukayi kiciɓis gabana ya bada wani rass! Da sauri kuwa ta amshe kular da ke hannuna buɗewa tayi. Wata uwar harara ta jefa mini kafin ta ce"Amma na hanaki shigar mini kitchen tunda ba gyatumarki ce ta ajiye kayan ciki ba, amma kinyi da 'yar gaske wallahi kin bar cin abincin nan." Zama tayi ta fara ci, hannu baka hannu ƙwarya "Daman yunwa nake ji wallahi baki cin shi." Ban tanka mata ba nayi shigewata ɗaki don nasan yadda na ƙoshi ko haka zan iya kwana. Hasken da wayata tayi yasa na miƙa hannu na ɗauka. Yah Md ne da mugun sauri na ɗauka. "Hello Yaya!" Na furta da hanzari. Ɗan tsaki yaja tare da fesar da huci "Kira na nawa na miki baki ɗauka ba?"

 Murya a raunane na ce"Kayi haƙuri ban daɗe da tashi bacci ba kuma na shiga kitchen."

 "Ya jikinki?"

 "Naji sauƙi Yaya."

 "To yayi."

Ƙit ya yanke kiran, nabi wayar da kallo ina murmushi, Ya jikinki na maimaita kamar yadda yayi, 'Daman kadamu da lafiyata?' Na tambayi zuciyata. Kira uku ya mini ban ɗauka ba yayin da naga Adyaan ya kira ni har so sha biyu.

Ƙurawa lambarsa ido nayi tamkar shi nake kallo, "Me yasa ka dawo rayuwata a wannan lokacin?" Kamar yaji tambayar da na masa sai kawai kiranshi ya shugo, nan take naji jikina ya kama rawa kamar kar in ɗauka wata zuciyar ta ce 'Ki ɗauka ki masa kashedin ya daina kiranki.' Abin da zuciyata ta tsara mini nabi sai dai ina ɗauka nayi shuru sakamakon rigani maganar da yayi.

 "Haba Nihlah! Me nayi miki zaki gasa ni ta hanyar ƙin ɗaukar kirana ?" Hawaye naji sun fara tarar mini rashin mutumcin da nayi niyyar shuka mishi naji na gagara, daman sam hakan ba halina ba ne ban saba ba, shiyasa bana tunanin ma zan iya.

 "Adyaan ba ni da lafiya ne tun jiya shiyasa, ban daɗe da tashi a bacci ba sam ban ga kiranka ba sai yanzu."

 "Baki da lafiya fa kika ce Nihlah, meke damunki? Bari nazo na kaiki asibiti!" Duk naji ya ruɗe ya fita a hayyacinsa.

 "Karka damu Yaya ya sayo mini magani kuma yanzu naji sauƙi."

 "Anya kuwa Nihlah? Don Allah ki bari nazo na kai ki asibiti a duba mini lafiyarki."

 Cike da mamakin ƙarfin halinsa na ce"A'a na sami lafiya." Wai yazo ya kaini asibiti sai kace mijina, ko ya manta ina da aure ne oho.

"Nihlah ki rabu da wannan mugun mijin naki kizo ki sami farin ciki."

Nan take na ɗaure fuska, "Bari kaji Adyaan idan har kasan zaka kira ni ne domin ka dunga faɗa mini maganganun banza irin waɗannan to karka kuma kirana." Ina ƙoƙarin katse kiran ya ce"Don Allah karki yanke tunda baki so ina faɗa miki gaskiya. Hajiya ta ce tana gaishe ki."

 Numfashi na sauke tare da furta "Ina amsawa, sai da safe." Ban jira cewarsa ba na yanke kiran ina jan numfashi, ina tausayin kaina ranar da Yah Md zai gane ina waya da Adyaan tabbas nasan a ranar kashina ya bushe. Wai ma me ya jani bashi lambata bayan nasan yanzu aure gare ni? Tabbas na aikata kuskure babba. A bakin gadon na zame ina tuna yadda muke da da Adyaan, duk da tsanar da Umma ta masa haka kullum yana hanyar gidanmu matuƙar yana gari. Zagi kam kullum sai ya shashi gurin Umma fita kam gurinsa bata barina sai idan anci sa'a mun haɗu a waje..

Amal ce ta katse mini tunani wacce tayi tsaye a kaina tana hura hanci. Ɗagowa nayi ina dubanta cikin tsiwa ta ce, "Yah Mz ya ce kizo." Fuw! Ta fita, girgiza kaina nayi tare da miƙewa nabi bayanta.

''Barka da dawowa Yaya Mz." Na furta cikin sanyin murya ina ƙoƙarin zama saman kujera one sitter, shi kuma yana saman mai cin mutum uku shi da Amal.

 "Yawwa Nihlah ya jikin naki?"

  "Naji sauƙi.''

  "A'a fa karki cutar da kanki, ki sako hijab na kaiki asibiti munyi magana da Md."

 Alamar zan ƙara masa musu da ya gani ne yayi saurin dakatar da ni.

  "Kin san dai bana son musu ko?"

  Amal ta amshe a fusace ranta kuma a ɓace.

  "Tunda bata buƙata Yaya ka rabu da ita mana, ai jiki magayi."

 A hankali na miƙe tare da komawa ɗakin baccina na sako babban hijabi har ƙasa, ina fitowa ya miƙe tare da ɗaukar hularsa ya saka, Amal ta miƙe da sauri. ''Muje na raka ku!"

  "Bazaki bi mu ba!" Ya furta tare da yin gaba, nabi bayansa a zuciyata ina mamakin yadda Amal ta zaƙe da yiwa Yaya Mz rashin kunya bayan ada kowa tsoransa yake ji a gida. Saboda Yaya Md shine mai sakin fuska amma shi kam bai da fara'a, sai gashi wai Amal ce ke juya shi kamar waina a tanda. Bangajin da ta kai mini ne ya sani yin taga-taga zan faɗi. Cikin azama ya juye tare da tare ni na faɗa a hannunsa...


08104335144


Masu buƙatar littafin za suyi magana ta lambar da ke sama ko a tura kuɗi kai tsaye 500 ta 8104335144 Opay wallet Fatima Rabiu Sunusi sai a tura shaidar biya ta 08104335144 na gode.



#Nihlatulkhair

#YahMd

#YahMz

#Adyaan

#Amal

#Farrah

#UmmuAffan

#RandarCikinƊakaa

Post a Comment

Previous Post Next Post