Tsantsar Kauna
kashi na 30
Na:
Tahir Yusuf (Novels Elite)
Whatsapp Group:
https://chat.whatsapp.com/CdAafth1AN96UeXKPuGzH2
Read My Book "Tsantsar Kauna" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681eab4136c55fcf7c41cd3f
Ganin bacci kawai takeyi babu wani alamun matsala a tare da ita yasa ta koma falo ta zauna ta cigaba da kallon da ta ke yi a tv. zuwa 11:24 na safe Maryam ta farka agogon da ke fuskar wayarta ta fara kallo "Innalillahi wa'inna Ilaihirraji'uuun, Yau nine da irin wannan baccin safen" da sauri ta mike tare da yin salati, da sauri ta shige bandaki tayi brush sannan ta fito kai tsaye falo ta wuce, Salima ta gani zaune tana kallo ta gaida ta sannan ta shiga kitchen neman abinda zata saka a bakin salati.
Kamar yadda Abdullahi ya shaida m Fatima zai dawo sani da wuri, ƙarfe 1 na rana mun gama duk abinda ya fitar damu, muka sallami abokan kasuwancin mu su ka wuce mu ma dai gidan muka dawo saboda yanzu muna da ma'aikata a inda muke sayar da motocin na mu.
Kai tsaye gida na wuce na sallama kamar yadda na saba kullum kafin na shiga gida bayan na fito daga mota, Fatima ta amsa tare da suke min ƙofar falon da ta kulle da key, "Nayi mamaki sosai fa, ban ɗauka da gaske zaku dawo da wuri haka ba"
"Dama ba wani abu bane motoci aka kawo mana kuma akwai sauran cikon kuɗi da zamu bada, shine ba babban abinda yasa muka fita gaba ɗaya, amma banda wannan ai da ba inda zan fita yau, kin gama abinci ne?
"Saura kaɗan dai bai ƙarasa nuna ba" ta juya da niyyar shiga kitchen ta sake duba abincin duk da bata daɗe da fitowa daga kitchen ɗin ba"
Kukan Affan ne ya saka Ni miƙewa daga zaman da nayi kasancewar na gaji kuma ina jin yunwa, na shiga kafin na ƙarasa ɗaki ma ya fito gani na da yayi ya saka shi yin shiru daga kukan da ya fara na ɗauke shi muka fito falo tare.
Bayan na fito daga Sallar La'asar na kira Abdullahi na shaida masa bincike na akan Maryam ya kammala, ina so na haɗu da Mijin ƴaƴanta mu fara magana kafin zuwa mataki na gaba.
Inda yake tambaya ta "yaushe zamu gana da mijin yayan nata?
"Sai dai irin bayan sallar Isha zamu tafi, kuma ina so na sanar da Fatima tun da wuri kada sai abu yayi nisa ta ɗauki abin da wata manufa"
"Kada ka fara wannan gangancin, ka bari tukuna ba yanzu ne dai-dai 'okacin da Yakamata ka faɗa mata ba, ka jira zan faɗa maka lokacin da Yakamata ka faɗa mata."
"To shikenan, dan Allah in da hali kazo nan muyi Sallar Isha'i a nan kawai ko kuma a layin su Maryam ɗin zan sa ta sanar dashi zamu zo yau"
"Ba damuwa ango, yadda kake so haka za'ayi"
"Ka ganka ko bana son iska ci, sai anjima" na kashe wayar na koma gida.
Maryam farin ciki sai wanda ya ƙaru, jin za'a zo neman izinin aurenta, yau dai yin Maryam cur ba abinda takeyi sai godiya ga Allah kawai.
Kamar yadda muka shirya daga isar da Sallar Isha'i ba mu tsaya ko ina ba sai gidan su Maryam dake Gyallesu. Duk da ya san da zuwan mu amma mun sake kira don a sanar dashi gamu mun iso, da Murmushin sa ya fito ya yi mana nuni da mu shiga, bamuyi wata-wata ba cikin falon muka shige kai tsaye yana gaba muna bin sa a baya.
Ya karɓe mu cikin mutuntawa sosai, sannan Abdullahi ya fara masa bayanin abinda ya kawo mu. "Wani muhimmin abu ya kawo mu wannan gida, wannan abu kuwa shine neman izinin tsayawa da Maryam
"To, Maryam dai amana ce a gareni, domin kuwa ƙanwar mata ta ce, iyayenta suna garin Yola, amma idan ta amince tana son ka zan baku izinin tsayawa da ita, amma maganar aure ba sani za'ayi ba, sai na yi magana da iyayenta mun ji, in sun bani daman aurar da ita shikenN idan kuma basu bani ba sai kun sami iyayen ta a garin Yola."
"To Alhamdulillah! Dama abinda muke so kenan, idan sun daidaita kansu in sha Allah zamu dawo muni yadda za'ayi maganar aure, amma dai yanzu ka fara magana da iyayen nata tukuna, duk yadda akayi sai a sanar damu"
"In sha Allah wannan ba wani abu ne mai matsala ba."
Ya sallame mu muka fita ba mu tsaya ko ina ba Abdullahi ya sauke Ni a gida ya wuce.
Walima da Ibrahim na zaune a falo suka kira Maryam, ta fito nan suka sanar da ita duk yadda sukayi da su Kamal, sunyi farin ciki sosai ganin Kamal da alamu yana da hankali sosai. Maryam dai kunya ta hana ta cewa komai, suna gama maganar da zasuyi ɗaki ta wuce da sauri don shirin kwanciya.
"Ke ce Amaryata da aka kawo gidan nan ko, to ki sani wannan gidan nawa ne Ni kaɗai babu wacce ta isa ta shigo ciki, idan kin shigo ma to ko kwana bazakiyi ba zaki fita." Fatima ce ke magana tare da tsakiyar nata kawayen
Zubaida ce daya daga cikin Ƙawayen Maryam ta lalle ta "wallahi ƙarya kike yi wannan gida daram kawata kamar ta zauna a ciki ba inda zata sai dai ke ki fita"
"Zubaida ai idan kare na haushi ba'a kula shi, shiru ake yi a barshi" Zainabe ta faɗi haka tare da miƙewa tsaye ta nufi inda Fatima take
"Baiwar Allah, bari na faɗa Miki abinda ba ki sani ba, da kin iya riƙe miji da ba zai yi Miki kishiya ba"
"Haka kuka ce ko, to zaku ga abinda zai faru, kodai ta fita da ƙafar da ko kuma a fita da gafarta" Fatima ta juya da fita ba tare da ta ƙara furta komai ba.
Don jin yadda labarin zai cigaba mu haɗu a shafi na 31