Tsantsar Kauna Page 29 - Abokiyar Hira Novels

 

Abokiyar Hira Novels Latest Audio

Tsantsar Kauna

kashi na 29


Na:

 Tahir Yusuf (Novels Elite)


Whatsapp Group:


https://chat.whatsapp.com/CdAafth1AN96UeXKPuGzH2


Read My Book "Tsantsar Kauna" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681eab4136c55fcf7c41cd3f


Tun bayan fitar Kamal daga wajen Mahaifiyarsa abin ke damun ta abincin da take ci ma saidai rufe shi tayi saboda mamakin maganar da Kamal ya zo mata da shi "Dan yau kenan ba saka ka sannan ba'a hana ka, Allah ya tabbatar da Alkhairi".  Tana tsaka da tunanin ne Mahaifin Kamal ya shigo bayan ya zauna ya fara cin abinci ta fada masa yadda sukayi da Kamal, baice komai ba saida ya gama cin abinci sannan ya fara magana 

"Gaskiya ba wani aibu bane duba da sunnah ce ta Manzon Allah (W.A.S.) matukar zai iya adalci a tsakanin matan sa"


"Amma ba ka ganin yayi kusa Baban Kamal?


"Babu wani wuri da yayi, yana da rufin asiri, yana da gida sannan yana da inda yake samun kudi, kawai addu'a zamuyi masa Allah ya tabbatar da alkhairin da ke ciki"


"Ban ki naka ba Amma Fatima fa"


"Nace miki wannan babu komai itama in sha Allah zata fahimta" haka dai suka cigaba da tattaunawa.


Tun da na bar gidan Mama Masallcin Layin kawai na tsaya nayi Sallah domin sun fara Sallah, bayan an gama ne na dauki hanyar gida, har na kusa shiga gida na tuna akwai abinda nake son siya kafin na shiga gida.


Baya na koma na shiga wani supermaket dake saman layin mu nayi siyayyar abinda nake so sannan na dawo gida.


Affan har ya fara bacci amma jin muryata ya tashi dama na siya masa yoghurt wanda nasan yana sha sosai, aikuwa yana gani da sauri ya karba tun kafin a bude ya fara sakawa a baki da niyyar zai sha, ban iya bude masa ba saboda ina cin yunwa sosai, Fatima ce ta bude masa, na zauna cin abinci sannan muna hira da Fatima amma ban fada mata abinda nake da niyyar yi ba sai na tabbatar da yiyuwar abin.


 Munyi hira sosai da wasa da dariya Kamar bamu sami sabani ba a baya. Gaskiya Rayuwar aure da dadi, amma ban sani ba ko dan ban taba fuskantar wata matsala bane mai girma a zamantakewar mu da Fatima.


Maryam cikin dare ta tashi tayi alwala ta gabatar da sallolin nafila tare da godiya ga Allah da ya karkato da zuciyar Kamal zuwa gare ta sannan ta sake yi wasu addu'o'in na neman zabin Allah akan lamarin, tun karfe biyu na dare da ta tashi batayi bacci ba sai da aka idan da sallah Asuba sannan ta koma tayi bacci.

 "Fatima Affan bai tashi ba gashi zan fita, naso in ganshi kafin na fita kuma bana so a tashe shi in har ba shine ya tashi ba, ko da yake jiya bayi bacci da wuri bane"


"wai Saurin me kakeyi ne haka, yau naga da sassafe zaka fita"


"wallahi wani abokin cinikayyar mu ne mukayi alkawari zai kawo mana wasu motoci siyasa yanzu haka kiran Abdullah na ke jira." ban gama rufe baki ba sai ga kiran Abdullahi na dauka kiran ya sanar dani yazo gashi a waje. Fatima ta dauko jakar da na ajiye a kujera ta biyo ni bakin gate dashi.


"Yau dai ka dauke min shi da wuri haka" Fatima dake bakin gate tayi maganar cikin tsokana tana kallon Abullahi wanda ke azazzalawa akan su tafi sun makara.


"Kiyi Hakuri yau da wuri zan dawo miki dashi, in Sha Allah" abinda ya iya fada kenan ya tada mota suka wuce, Fatima kuwa rufe gate din tayi ta koma cikin gida.


Karfe 11 na safe ne Salima na falo tana ta tunani ganin Maryam bata fito ba,  bata santa da yawan baccin safe mai yawa haka ba "Anya Lafiya kuwa yau maryam bata fito ba" ta gama dai zancen zucin ta kafin ta tashi don dubawa ta gani ko lafiya. 


Ganin bacci kawai takeyi babu wani alamun matsala a tare da ita yasa ta koma falo ta zauna ta cigaba da kallon da ta ke yi a tv. zuwa 11:24 na safe Maryam ta farka agogon da ke fuskar wayarta ta fara kallo "Innalillahi wa'inna Ilaihirraji'uuun, Yau nine da irin wannan baccin safen" da sauri ta mike tare da yin salati, da sauri ta shige bandaki tayi brush sannan ta fito kai tsaye falo ta wuce, Salima ta gani zaune tana kallo ta gaida ta sannan ta shiga kitchen neman abinda zata saka a bakin salati.


mu hadu a shafi na 30 

Dan Allah ayi mana sharing, like da kuma comment.

Post a Comment

Previous Post Next Post