Tsantsar Kauna Page 28 - Abokiyar Hira Novels

 

Abokiyar Hira Audio Download

TSANTSAR KAUNA 


Kashi na 28


by: Tahir Yusuf (Novels Elite)


Whatsapp Group:


https://chat.whatsapp.com/CdAafth1AN96UeXKPuGzH2


Read My Book "Tsantsar Kauna" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681eab4136c55fcf7c41cd3f


"Ya za'ayi na gaji dake Fatima ki tuba Tsawon Lokacin da muka dauka tare, tun muna yara har muka girma yanzu kuma mukayi Aure ga yaro a tsakani, haba Fatima tun tuni ban gaji da ke bane sai yanzu. Ina son ki so na har abada."


Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya yau da daɗi gobe babu, amma dai Kamal na ƙaunar Maryam sosai, Maryam kuma na ƙara samun kusanci da kama.

Fatima, gobe Affan zai cika shekara ɗay da haihuwa me kike ganin za ayi masa na murnar zagayowar haihuwar sa?


"Oho! Duk abinda da kake so kayi masa mana ina ruwa na"


Haba Fatima, nine Kamal ɗin ki fa, dan Allah duk abin da ya wuce ya wuce mana, ina ce mun gama wannan maganar, dan Allah kiyi haƙuri, ki min uzuri. Pls baby in Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba.

Allah ya sa da gaske kake yi, amma gaskiya rai na ya ɓaci sosai, yanzu komai ya wuce Mijina Kamal Baban Affan.


Naji daɗi sosai a cikin zuciyata cin kalaman Fatima, hankalina ya sake kwanciya sosai, nan da nan ta faɗi abin da Yakamata ayi duk da ba wani shagali za'a yi ba, amma dai kayan abubuwan wasa muka suyi, wanda tare muka fita zuwa inda muka yi siyayya.


Alhamdulillah! Affan ya cika shekara ɗaya da haihuwa, ya yi wayo sosai yana iya yawo ko ina a cikin gida, idan ba bacci yake ba, saidai a kawar da duk wani abu mai amfani ko wanda zai iya cutar dashi.


Ina zaune cikin gida Fatima tana cikin kitchen tana girki, Affan kuwa guje-gujensa kawai yake yi yana wasa da kwallo, buɗe data danayi yasa saƙonni ke ta shigowa a WhatsApp, Sunan Maryam ne kawai na fara gani. Sai na kira ta a waya ringing ɗaya kuwa ta ɗauka muka gaisa cikin mutunta juna "Maryam hankalina ya kwanta da ke kuma na amince da Soyayyar ki bisa binciken da nayi da kaina da wanda nasa aka yi min game da dake. Ba abinda zan ce sai dai Allah ya tabbatar da Alkhairi"


"Alhamdulillah! Nagode Baban Affan in Sha Allah zan zamo mai yin duk abinda kakeso da bin duk umarnin ka"


"In Sha Allah idan na gama duk wani abu da Yakamata, zan sami mijin yayarki muyi magana sai ya haɗa Ni da wanda zan nemi aurenki a wajensa" da haka muka gama wayar na cigaba da harkokina Affan kuwa Wase sa kawai yakeyi.


Farin ciki ya cika Maryam sosai ganin mafarkinta na daga da zama gaske "Oh Ni Maryam zan zama Matar irin mijin da nake so a rayuwata. Alhamdulillah" Maryam ta fita farko domin ta sha ruwa kafin ta dawo ta faɗama Zainab yadda sukayi da Kamal.


"Maryam, kwana biyun nan na kasa gane miki fa wannan farin cikin da kikeyi ban gane masa ba zo ki zauna ki faɗa min menene, kamata yayi ace idan abin farin ciki ya sameki nine na farko da Yakamata na fara sani, haka idan na baƙin ciki ne." Babu gardama Maryam zauna kusa da ita "Auntyn gaskiya na sami wanda nake so shima kuma yana sona sosai amma yana da mata har da yaro guda ɗaya"


"Masha Allah, gaskiya na ji daɗin wannan maganar taki Kinga kuma sai ki aurenki ki koma gidan ki"


"Kuma yace idan ya gama wani abu da yakeyi in Sha Allah zai sami Yaya suyi Maganar"


"Amma kina ganin baiyi wuri ka kuwa?


"A'a Auntyn, baiyi wuri ba"


"Oh! Maryam har kina iya cewa baiyi wuri ba ko?


Da gudu Maryam ta shiga cikin ɗakin ta don kunyar da ta ji, shigar ta daki ke da yiwa ta kira Zainab hana labarta mata duk yadda sukayi da Kamal.


"Gani nan zuwa gidan yanzu ki jira Ni" lokacin ƙarfe 5 biyar  na yamma daidai lokacin dama zaman gidan ya isheta saboda yau bar fita ko ina ba kuma zaman gidan ya isheta.


Na fito daga masallaci Sallar Magriba, kiran Fatima kawai nayi na sanar da ita ba zan sami daman dawowa ba sai bayan Isha domin zan wuce gidan su Mama.


Assalamu alaikum! Sallamar da nayi a ƙofar ɗakin Mamana na jira kafin a amsa na shiga.


"Amin Wa'alakumussalam, shigo"


Na shiga na zauna kusa da ita na mika Mata ledar da ke hannu na "Mama ga wannan kaza ne nazo wucewa naga ta burge Ni na siya Miki"


"Allah yayi albarka, ina Maigidan nawa Sarkin gagara?


"Basu san zan zo ba daga masallaci kawai na zo nan, dama wata magana nake son nayi dake"


"Wace magana ce haka Kamal?


"Mama, wata yarinya na samu natsatstsiya kuma mai hankali g natsuwa, idan da hali ina so na ƙara aure"


Ta dafe ƙirji tace "Aure Kamal? Dukka dukkan yaushe kayi auren ka na farko yanzu kuma k sake bijiro da wani auren, kada fa hakan ya saba maka ka zama mai aure-aure."


"Mama hakan ba zai faru ba in Sha Allah Ni dai kawai ki saka Ni a cikin addu'a idan Alkhairi ne Allah ya tabbatar dashi idan kuma ba Alkhairi bane Allah ya canza min da abinda yafi Zama Alkhairin."


"Ban ƙi maka ba Kamal, wai ma in tambaye ka, ko Fatima ta maka wani abu ne?


"Fatima bata min komai ba kawai lokaci ɗaya na kamu da son yarinyar idan na rasa ta samun irinta zai min wahala, Mama."


"Zanyi magana da mahaifin ka idan ya dawo, amma kasa kayi garaje ka zauna kayi tunani sosai tukuna Kamal"


"Shike nan in sha Allah zan yi hakan" 


Kiran sallar Isha ne ya yanke mana tattaunawar da muke yi, nayi mata sallama na fita.


Don jin ya zata kasance tsakanin Kamal da Fatima, sai kun biyo mu a kashi na 29.


kada a manta ayi mana Gyara ko Shawara in da aka ga baimuyi daidai ba.


comment, Share and Like in har wannan littafin yayi muku dadi.


Na Gode Tahir Yusuf (Novels Elite)✍️

Post a Comment

Previous Post Next Post