TSANTSAR KAUNA
Kashi na 27
by: Tahir Yusuf (Novels Elite)
Whatsapp Group:
https://chat.whatsapp.com/CdAafth1AN96UeXKPuGzH2
Read My Book "Tsantsar Kauna" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681eab4136c55fcf7c41cd3f
"Duk Abinda Allah ya Kaddara bazan yi fushi ba, kuma Duk abin da Yayi daidai ne" na duba sakon amma bance komai ba sakamakon jiki na yayi sanyi da jin kalamanta
Bayan na dawo gida muna zaune Ni da Fatima a Falo kamar kullum, sai Wani sakon ya sake shigowa, bayan na bude na danyi shiru har Fatima tayi magana ban ji me tace ba wanda hakan ya bata mata rai sosai, amma ba rashin amsawar bane ya bata mata rai ba kallo na da tayi yadda fuskata tayi wanda ta fuskanci akwai wani abu bata nuna min ba dai amma fuskarta ya canja sosai.
Tun Kalaman Maryam basa tasiri a cikin zuciyata har suka fara amma duk da haka Fatima ta daban ce, bazan iya ha?a soyayyar ta da kowacce mace ba.
"Tun tana magana bana amsawa har na fara, chat kawai muke yi saboda ta iya hira amma ban ta?a ganin ta ba ban san wacece ita ba" Abdullahi ya gyara zama ya fuskanci Kamal tare d sake bashi cikakkiyar natsuwa, "Ina jin ka"
"Yanzu haka mun fara waya, ina so mu ha?u ta ki bani dama, hatta hotonta ta ki nuna min, ban san dalili ba."
Abdullahi yayi murmush kafin ya ce "to kai yanzu da kake wannan, ta ya za ka ?auki irin wannan lokacin da mace baka san wacece ba sannan ta ?i yarda ku ha?u idan ba wani abu ne na cutarwa a ran ta ba ta bayyana kan ta."
"Babu yadda banyi da ita ba amma ta?i yarda, shiyasa kawai na barta da kanta zata bayyana kan ta."
"Kamal tambayar da zan yi maka ita ce, Aure zaka ?ara ko mene sannan Fatima ta san da wannan, dukka shekarar ka nawa da aure. Gaskiya kayi tunani."
Na gyada kai na sannan nace "In har tana da halaye masu kyau me zai hana na aureta, maganar Fatima kuma wannan mai sauki me"
"Haka dai kace, kada kayi tunanin Fatima na ?aunarka wallahi duk ranar da kayi mata maganar kishiya zaka sha mamaki, ranar zaka gane kishi a jinin mata yake, don haka bazan goyi bayan ka Dari bisa Dari (100%) ba saboda kada Fatima ta daina ganina da mutunci. Kasan Mata da sun ga Mijin su ya Kara Aure to duk tunanin su zai koma kan babban abokin su akan shi ya saka shi wanda ba haka abin yake ba"
"In Sha Allah babu abinda zai faru" abinda na iya fa?a kenan kafin mu cigaba da wata sabgar.
A bangaren Maryam kuwa aganar Kamal ya bata Tsoro sosai inda hakan ya haifar mata da tunani kamar yadda take furtawa cikin zuciyarta "Anya Zan cigaba kuwa naga kamar wanna ba ta ni yakeyi ba da alamu yana da mata, to amma ko da yana da mata ni ba damuwa na bane wannan in har zai amince da soyayya ta. Bari na daure kada hakan ya sare min kwarin gwuiwar da nake da shi, na damka komai nawa a hannun Allah shine wanda ke sanya soyayya a zuciyar wanda ya so da kuma lokacin da Yas." wani sako ne ya katse mata wannan tunanin da ta keyi, da sauri ta bude amma ba abinda take jira bane, Zainab ce ke tambayarta ya ake ciki'
"Zainab kamar zan hakura amma dai zan cigaba da gwadawa bazan gaji ba in sha Allah sai nayi nasara." ta tura ma Zainab wanda dama tana jira,
"Yauwa Kawata kada ki sare akan abinda kike so, ba komai ne ake samu cikin sauki ba, wani abin ma sai ka wahala sosai kafin ka mallakeshi, wani kuma zaki ga cikin sauki ko kina zaune zai zo har inda kike. Amma insha Allah wannan shine karshen wahalahar."
Na koma Gida Kamar yadda na saba na tarar da fatima zaune cikin falo tana wasa da Affan, tun da ta ganni ta fara daure fuska kamar yadda na ga canji jiya, yau ma bai sake da jiyan ba.
"Fatima Dan Allah me nayi miki tun jiya naga kin canja, idan wani abu ne ki fada min mana, dan Allah" na fadi hakan yayin da nake zama kusa da ita, da mamaki Fatima ta matsa tayi nesa dani abinda ban taba gani ba.
"Oho! Kai ka sani."
"Ban gane Oho ba, dan Allah fatima ki fada min idan wani abu na yi miki?''
"Bari kaji Kamal kwana biyu naga ka canja yanzu baka da wani abu sai danna waya ko magana mukeyi hankalinka na kan waya, ko dai ka gaji da ni ne?" hawaye suka ciko daga idon Fatima yayin da ta koma da kallon ta kan Affan da ke zaune yana wasa da mota"
"Ya za'ayi na gaji dake Fatima ki tuba Tsawon Lokacin da muka dauka tare, tun muna yara har muka girma yanzu kuma mukayi Aure ga yaro a tsakani, haba Fatima tun tuni ban gaji da ke bane sai yanzu. Ina son ki so na har abada."
Don jin ya zata kasance tsakanin Kamal da Fatima, sai kun biyo mu a kashi na 28.
kada a manta ayi mana Gyara ko Shawara in da aka ga baimuyi daidai ba.
comment, Share and Like in har wannan littafin yayi muku dadi.
Na Gode Tahir Yusuf (Novels Elite)✍️