Tsantsar Kauna Page 26 - Abokiyar hira

 

Happy birthday Affan

TSANTSAR KAUNA 


Kashi na 26


by: Tahir Yusuf (Novels Elite)


Whatsapp Group:

https://chat.whatsapp.com/CdAafth1AN96UeXKPuGzH2


Read My Book "Tsantsar Kauna" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681eab4136c55fcf7c41cd3f


Maryam ta kada kan ta ta fita waje da niyyar zuwa gidan su Zainab, yayin da ita kuma Zainab ta fita amma ba nisa tayi ba.


Bayan ta taji an dafa, amma kafin ta juya kamsin turaren wacce da dafa ta ya bata amsar ko wacece. "Kin zata bazan gane ki bane ko zaki iya bani tsoro?"  Maryam ce tayi tambayar yayin da take juyawa ta fuskancin Zainab.


"Meya biyo dake ta nan, kin ce an aike ki, aiken kenan?"


"a'a, kawai dai hanya ce ta biyo dani ta nan sakamakon abinda na tafi nema ban samu ba sai a bayan layin ku shiyasa na biyo tanan don na shiga wajen ki sai na hango ki a waje."


"To mu karasa gida na bada sakon da akayi min sai mu cigaba da magana"


Haka suna cigaba da tafiya suna hira kamar yadda suka saba duk lokacin da su ke tare, shakuwarsu ta kai shakuwa sosai amma fa watarana dole za'a rabu idan ba aure ba akwai mutuwa.


Daga shigar su gida dakin Umma Zainab ta wuce ta bada sakon da akayi mata kafin ta dawo dakin ta inda Maryam ke zaune tana jiran ta.


Zainab ta kwace labari tas ta ba Maryam yadda ta sami lambar Kamal. "To yanzu menene mataki na gaba?" in ji Maryam wacce ta natsu tana jiran irin amsar da Zainab zata bada.


"yanzu abu daya ne zamu fara, abinda zamu fara kuwa shine, kada mu tinkare shi da maganar soyayya kai tsaye, sannan zaki boye kanki na wani lokaci, sakonni kawai zaki fara tura masa wadanda zasu jawo shi jikin ki in Allah ya taimaka daga nan shi da kanshi zai kawo kanshi har inda kike, Amma fa ba lallai ne ki same shi da wuri yadda kike tunani ba."  Zainab ta gama maganarta tana kallon fuskar Maryam wanda ke cike da murmushi.

"Gaskiya samun Kawa irinki akwai wahala sosai, ban san da wani irin kalma zan gode miki ba"


"Haba Maryam dan wani abin, zan iya yin wanda ya fi wannan in har kawata zatayi farin ciki, hakan ba zai zama wani abu mai wahala ba, ga lambar nan na tura miki ta whatsapp."


Bakin Maryam ya kasa rufuwa tsananin murna wanda daga ka ganta kasan akwai wani abu.


Ina Zaune a gida ni da Fatima Affan na bacci a jikina yayin da nake danna wayata muna hira kamar yadda muka saba ni da ita idan ina gida, hakan na kara ma soyayyar mu karfi sosai.


Sako ya shigo wayata a whatsapp da lambar da ban san ta ba kuma babu a wayata na Karanta na sake karantawa, amma babu suna ba'a fadi daga ina aka turo ba. Ban Amsa ba dai na cigaba da hirar mu da Fatima a gefe daya kuma muna hira da Abdullahi a whatsapp.


Da safe bayan na gama shiryawa zan fita na sake ganin wani sakon ya sake shigowa cikin wayata amma a wannan karon sakon barka da safe ne, shima dai ban amsa ba amma na bude, nan dai mukayi sallama da Fatima na fita.


Munyi sati biyu tana tura irin wannan sakon amma bana mayar mata da nawa sakon.


Dai dai Karfe 2 na rana na kara ganin wani sakon kamar ba zan bude ba amma dai sai na bude na karanta ga abinda ke kunshe a cikin wasikar: "Assalamu Alaikum, Barka da rana ya Kasuwa. A yanzu babu abinda ya rage ni face tarin son kasancewa Abokin rayuwarka ta har abada. Daga Boyayyiyar Masoyiyarka."nayi mamakin ganin wannan sakon, kamar ba zan amsa ba a wannan karon dai na amsa kamar haka: "Da farko na gode da sakonninki kinyi kokari, amma ban san ko wacece ke ba, haka kema baki san ko wanene ni ba." na tura mata, bai wani dade ba ta bude alamun tana online.


"Kai dai baka san komai nawa ba, amma nasan wasu abubuwa daga gareka" 


"Amma kin san ina da mata"


"Ban sani ba amma namiji ai ba mijin mace daya bane da kai zan zauna ba da matar ka ba"


"hmmm! to amma idan kuma bani da ra'ayi ko bani da daman kara wata matar fa?" na tura mata amma shiru ba ta dawo min da amsa ba, hakan yasa nima na cigaba da harkokina.


Don jin Amsa da Maryam zata ba da sai kun biyo mu a shiri na gaba. Kada a manta ayi sharing, Like sai wadanda basuyi following ba su yi. 


Muna son jin ra'ayoyin ku, pls.


Tahir Yusuf ✍️

Post a Comment

Previous Post Next Post