Tsantsar Kauna Page 25 - Abokiyar Hira Novels

 

El-Rufa'i Data Sub

Tsantsar Kauna 

Kashi na 25 

By Tahir Yusuf


Domin shiga Whatsapp Group na Tsantsar Kauna ga link:

https://chat.whatsapp.com/CdAafth1AN96UeXKPuGzH2


Littafin Tsantsar Kauna a Arewa Books.

https://www.arewabooks.com/book?id=681eab4136c55fcf7c41cd3f


"Na sami abinda kika daɗe kuma nema, wato lambar wayar wannan gaye Kamal"

Maryam tayi wani ihu tayi tsalle saida Auntyn ta ta shigo "Maryam Lafiya kuwa irin wannan ihu, ai sai muyi tunanin wani abu ne ya same ki" 

Ta ɗan natsu kafin tace "Wallahi muna waya da Zainab ne kawai.


"Allah ya shirya ku ke da ita" sannan t juya ta koma Falo.


"Zainab ina jin ki Auntyn ce ta shigo jin ihu da nayi, amma ta fita, amma ya akayi kika sami lambar."


"hmmm! Wallahi ɗazu Mama ta aike Ni Cikin gari, cikin adaidatar da na shiga na haɗu da wasu da zasuyi masa aiki, a inda yake siyar da motoci, a wanensu na ga katin sa d yake ba mutane "wato Complimentary Card" anan na ɗauki lambar , nace tunda kina nema zan baki."


Maryam dake kwance ta tashi ta zauna a tsakiyar gadon da dake ta zango matashi ta rungume "Gaskiya wannan labarin yayi min daɗi, yanzu kina ina? Idan kina gida ne nazo."


"Na ɗan sake fita amma ba nisa nayi ba yanzu zan dawo."


"To shikenan gani nan zuwa gidan" 


Farin ciki ya cika Maryam, Murmushin da ke fuskanta yaƙi boyuwa, Falo ta fito ta tarar da Auntyn ta, zata fita.


"Maryam yau ban gane miki bane, yau fuskar ki cike take da farin ciki ba kamar kwana biyu baya ba. Me ke faruwa?"


Maryam ta cigaba da Murmushin ta sunkuyar da kan ta "Bakomai wallahi Aunty."


"Koma dai Menene, idan tayi wari zamu ji" ta tambayi Auntyn ta kafin ta fita. 


Yau kuyi hakuri da wannan, Kwana biyun nan sai ahankali ne wlh.

Post a Comment

Previous Post Next Post