Tsantsar Kauna Page 24 - Abokiyar Hira Novels

 

Rufaida Youghurt

Tsantsar Kauna - Kashi na 23

Na Tahir Yusuf (Novels Elite)


Bayan kwana biyu da haduwar su Maryam da Kamal, Maigadi ya kira Maryam ya shaida mata ya sami lambar wayar Kamal, da sauri Maryam tace a ya tura mata.


Suna Gama waya sako ya shigo wayar Maryam, nan da nan ta bude, lamba ne nan take ta kira amma wayar a kashe, ta kara kira karo na biyu amma lambar a kashe, sai ta hakura da tunanin kila wayar ko ba chaji ko kuma matsalar network, ko idan dare yayi yana kashe waya. 


Lokacin dare ya fara babu damar fita ta tafi gidan su Zainab, wayarta ta dauko ta nemo lambar kawar nata Zainab, kira daya kuwa ya shiga, bata dade ba Zainab ta dauka "Ke Na sami lambar na kira amma a kashe, in atunanin ya kashe ne saboda dare ko kuma matsalar network."


"Masha Allah" abinda Zainab ta Fada kenan don lokacin ta dan fara bacci kadan wanda kira Maryam ne ya tashe ta.


"In Allah ya kaimu da safe zan sake kira muji ko zan samu"


"To shikenan Allah ya Kaimu, da safen ki kira"


Da haka suka gama waya, Maryam kuwa saboda doki da zumudi ko baccin kirki bata iya yi ba ganin burinta ya cika. Amma abinda ke mata yawo a zuciya shine, Shin Idan na bayyana masa abinda ke cikin zuciyata wani irin kallo zai dinga min, Mara kamun kai ko kuwa Masoyiya? ko ma dai menene ina son shi a haka.


Washe gari tun safe Maryam ta fara kiran lambar Kamal amma wayar dai a kashe, hankalinta ya tashi sosai, hakan ya sa ta nufi gidan su Zainab ko wanka ba da yi ba.


"Lafiya Kuwa Maryam, Me ya faru?" Zainab wacce tayi sauri ta mike tsaye daga kwancen da take.


"Zainab, Lambar fa taki shiga, na kira yafi so goma, Menene abinyi yanzu?"


Zainab ta rike mata hannu ta zaunar da ita a zefen gadon dake dakinta ta juyo ta kalle ta sosai "Maryam na sha gaya miki ki daina gaggawa a komai, ba lallaai ne ki sami abinda kike so a lokacin da kike so ba, Idan wannan bayan Alla din mijin ki ne duk duniya ba wanda ya isa ya hana faruwar hakan, kina zaune zai kawo kanshi wajen ki, amma idan har ba mijin bane duk duniya ba wanda zai sa hakan ya faru, saboda haka ki bi komai ahankali nima zan taya ki sai inda karfi na ya kare."


Jikin Maryam yayi sanyi sosai jin kalaman Zainab, hakan ya sanya zuciyarta tayi sanyi sosai, amma duk da haka soyayyar sa dai tana nan cikin zuciyarta "shikenan Zainab zanyi duk abinda kikace, nagode da samun kawa irin ki"


Maryam ta kira Maigadi ta sanar dashi"Lambar da ka bani baya Aiki"


"To Hajiya zan cigaba da nema miki wani in sha Allah"

Su kayi sallam kowa ya kashe wayar sa.


Tun daga Ranar Maryam ta rage irin zafafawar da take yi wajen sai ta mallaki Kamal ta ko wani hanya.


Na cigaba da ganin budi daga Allah sosai harkokina na kasuwanciya karu sosai, Godiya ga Allah kawai nakeyi a ko wani lokaci. Fatima kuwa kullum sosayyarta karuwa yakeyi a cikin zuciyata kamar yadda itama take sona.


Bayan wata biyu da

Affan ya cika wata takwas sai gagara saboda rarrafen da yake yi, babu daman ajiye wani abiu mai amfani ko wanda zai iya cutar dashi a fili don kuwa zai dauka kuma komai ya samu a baki yake sakawaaganinsa abinci ne.


Kiran Zainab ne ya shigo wayar Maryam wanda ke zaine a Falo tare da Yayarta da mijinta suna kallo, da sauri ta shige cikin daki don kada ta dauki wayar a gaban su ba. 


"Ke Banza Albaishirin ki" Zainab ta fadi haka muryar ta cike da zumudi.


"Goro, ki dan Allah ki Fada min ko menene don yadda naji muryar nan taki tabbas wani ya faru ko kuma wani abu zai faru."


don jin menene Zainab zata fada ma Maryam sai ku binyo mu a Kashi na 24.


kada a manta ayi comment idan kuna da tambaya, gyara ko korafi, sanna ayi sharin don wasu ma su amfana

Post a Comment

Previous Post Next Post