Tsantsar Kauna - Kashi na 22
Na Tahir Yusuf (Novels Elite)
Wannan Littafin free ne ba na sayarwa bane.
Sun tsaya suna kallona kafin su nufi inda nake lokacin ina gab da shiga gida suka yi min Sallama na tsaya suka karaso muka gaisa sai na tambaye su abinda ke tafe dasu. Zainab ta dan Sunkuyar da kai kasa ta fara cewa "Dama..... dama......"
Dama me ki bayani mana ina so zan shiga gida ina da aikin da zanyi.
"Gaskiya tun ranara da muka ganka a cikin adaidaita kayi ma kawata, idan ba damuwa tana so ku zama abokai" ta gama tana kallon Maryam
"hmmmm, abokai kuma da mace ba ma namiji ba gaskiya ba'a haka dani dan Allah kuyi hakuri" na lura basu ji dadin magana ta ba hakan yasa na cigaba da basu hakuri.
Jikin su duk yayi sanyi ganin yadda Kamal ya amsa maganar da suka zo dashi, nan bar su a tsaye na shiga gida.
"Maryam ki zo mu tafi mana, kin ga dai abinda ya faru"
Maryam ta kalli Zainab cikin baccin rai ta ce "mu koma wajen wancan mai gadin''
Suna tafiya kamar wadanda aka cire ma lakkan jiki saboda maganar kamal ya kashe masu jiki a haka suka koma wajen wannan maigadin," Dan Allah ina so zan baka wani aiki, lambar wayar wannan mutumin nake so, na nawa zan baka idan ka samu ka tura min." Ta ciro kudi a jaka ta bashi "wannan ka saka kati''
Maigadi ya amshi kudi ya ce "sai kin ji daga gareni"
Sannan ta juya suka kama hanyar su ta komawa gida.
Basuyi wata-wata ba gidan su Zainab suka fara wucewa, daga shigar su Maman Zainab ta kalle su kafin tace "Lafiya kuwa naga kamar wasu wadanda akayi ma mutuwa, Meya faru?''
Maryam ce tayi karfin hali ta amsa "Mama wani mai adaidaita ne ya bata mana rai"
ta tabe baki tace "Allah ya Kyauta"
suka nufi dakin Zainab suka shiga, daga shigarsu kowa ya wurgar da jakarsa ya fada kan gado sun kwanta da niyyar bacci amma baccin yaki zuwa maganar Kamal ne kawai ke dawo ma kowa cikin zuciyarta, da haka dai har barci ya daukesu.
Bayan Kamal ya shiga gida ran sa a bace ya tarada Fatima da Affan a falo suna zauna tana masa wasa yana ta wangale baki da sunan dariya. Ganin yadda Affan ke dariya ya sanya zuciyarsa ta danyi sanyi ba kamar yadda ya shigo gidan ba.
"Kinyi Sallah kuwa" na tambayeta kafina na zaub=na kusa da ita.
"A'a saidai shiri, dama ina jira ka dawo ka dauke shi sai na ta fi nayi"
Na cigaba da yi masa wasa ita kuma ta shiga cikin daki don gabatar da sallar Azuhur.
Maryam da Zainab kuwa basu tashi ba sai bayan La'asar, duk suka tashi nan suka gabatar da Sallar La'asar kafin kuma su cigaba da maganar yadda za'a bullo ma Kamal.
"Maryam ni a ganina kawai ki hakura ganin abinda ya faru da zu kuma......."
"tsaya Zainab nifa gaskiya bazan hakua ba domin ko da wani hanya ne sai na mallakeshi ba fashi zai gane da wa yakeyi."
"Maryam ki bi komai a hankali, mu jira a sami nuber din mu bishi ta lallami mu gani mu bashi lokaci yayi tukuna."
"toshikenan bari ayi yadda kikace, amma ina son shi, kuma irin namijin da nake so ne"
karfe biyar da wajen rabi Zainab ta raka Maryam ta wuce gida.
Bayan kwana biyu da haduwar su Maryam da Kamal, Maigadi ya kira Maryam...............
mu hadu a kashi na 23 don jin yadda zata kaya, an sami number ko ba'a samu ba?
kada ku manta ayi sharing sannan ku fadi ra'a
yoyin ku ko tambaya ko kuma gyara a inda mukayi kuskure.