Tsantsar Kauna - Kashi na 21
Na Tahir Yusuf (Novels Elite)
Wannan Littafin free ne ba na sayarwa bane.
Wacece Maryam?
Maryam dai iyayen ta yan asalin Yola ne, kuma su biyu ne a wajen iyayen su Ita Maryan din da Yayanta Salima, Salima tana aure da Ibrahim shima dan Girei ne dake Yola, Aiki ya kawo shi Zaria, yanayin Shakuwar Maryam da Salima yasa aka nema mata makaranta Jam'iar Ahmadu Bello da ke Zaria, Tana zaune a Hostel ne Amma duk Karshen mako tana zuwa Gyallesu inda Salima da Mijin ta Ibrahim.
Ibrahim da Salima Suna son junan su sosai ba'a taba jin kansu ko sun sami matsala a zamantakewar su ta aure, da kansu suke sulhunta kansu. Suna son Maryam sosai domin bata taba neman wani abu ta rasa a wajen su ko iyayenta.
Gidan su Maryam suna da arziki amma ba wani sosai can ba, kuma baza ka ce musu talakawa ba.
Zainab kuwa nan Gyallesu suka hadu yar makwabtarsu ce da itama dake karatu a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Sun Shaku sosai da Maryam koda yaushe suna tare bacci ne kawai ke raba su komai tare sukeyi.
wannan shine dan takaitaccen tarihin Maryam da yadda suka hadu da Zainab.
Tun da Maryam ta ga Kamal hankalinta ya tashi sosai tana ta kulle-kullen yadda za'a yi ta nemo Kamal da yadda zatayi ta mallakeshi. Zainab ce ta shigo cikin dakin Maryam ba tare da ta sani ba tana can tana tunanin Kamal saida Zainab ta taba ta sannan ta san da wani mutum a kusa da ita.
"Haba Maryam tun dazu ina tsaye fa, tunanin me kikeyi haka"
"Zainab wallahi gayen nan ne na dazu da muka hadu a adaidaita, shine kawai nake ta tunanin sa, ina sa son shi sosai. Kin san Hausawa sunce da Zafi-Zafi ake dukan karfe"
"To ke yanzu menene abinyi, Mutumin nan baki sanshi ba, baki san wanenen shi ba, Maryam ki bar maganar mutumin nan dan Allah" Zainab ta fada haka daidai lokacin da ta dafa kafadar Maryam kafin ta zauna kusa da ita.
"Zainab kece yakamata ki taya ni neman mafita amma ba irin wannan maganar ba, haba kawata, kin san bani da kamar ki."
"Shikenan yanzu me zamu fara" Zainab ta amsa ba don zuciyarta tana so ba.
Maryam ta gyara zama ta kalli Zainab da kyau "Kawata yanzu ta inda aka daukeshi a adaidaita din zamu koma mu sami wani mu tambaya ko zamu sameshi tunda har hotonsa na dauka ba tare da ya sani ba, kinga komai zaizo cikin sauki insha Allah"
"To yanzu idan mun same shi ya zakiyi cewa zakiyi kina son shi ko me"
Maryam ta zare ido ta rike hannu Zainab da sauri "Haba kawata ni fa mace ce, wuyar dai mu sami inda yake da sunan sh, sauran abubuwan zasu zo da sauki."
''To shikenan, amma yaushe zamu koma cikin Tudun Wadan?''
"Gobe ya kamata mu koma mu neme shi" Zainab kuwa dai babu yadda zatayi ne shiyasa amma dai bata son wannan sabgar, tsoronta guda daya kada yana da mata suna zaman lafiya ta kawo musu matsala a gidan su.
Washe gari karfe 4 hudu Maryam da Zainab suka koma Tudun Wada daidai ta wajen da aka dauki Kamal a adaidaita, Maigadin wani gida suka gani zaune a kofar gida, sukayi salllama ya amsa. "Malam, Dan Allah Tambaya mukeyi" Maryam tayi tambayar kafin ta ciro waya a cikin jakar da ke makale a kafadarta.
"Allah yasa na sani" Maigadi ya amsa tare da kallo su
Zainab ne ta dan tabi hannun Maryam "Ke Kalli bayan ki, kamar wanda muke nema ne fa"
Maryam ta waro ido kafin ta juwo gaba daya "wallahi kuwa shine, yanzu ya zamuyi?"
Mu hadu a kashi na 23 don jin suna yi ma Kamal magana ko kuwa yaya?
kada a manta ayi comment, gyara ko tambaya a comment section in sha Allah zamuyi reply, sanna ayi sharing wannan littafin domin wasu ma su sami irin wannan nishadin da kuke samu.