Tsantsar Kauna - Kashi na 21
Na Tahir Yusuf (Novels Elite)
Wannan Littafin free ne ba na sayarwa bane.
Anyi suna an gama lafiya, baki duk sun koma gida Fatima ta shiga sabuwar rayuwa tare da Kamal da kuma dansu Affan. Bayan kwana biyar da yin suna na gama hutun da na nema wajen kasuwancin mu, Alhamdulillah, kasuwanci sai habaka yake cibaga da yi, babu abind zamu ce sai dai godiya da Allah.
Nina zaune ina zancen zuci ina tunanin ta yadda na fara har zuwa yanzu, "Allah na Gode maka, ka azurtani da mata ta gari sannan ka bani haihuwa wanda mutane da yawa baka basu ba, wasu ka basu marasa lafiya, wasu kurame, wasu makafi. Bayan haka kuma ka bani dukiya masu yawa, Kai kadai ne abin godiya wanda ba'a hada Ka da wani."
Kukan Affan ne ya katse min zancen zucin da nakeyi, na shiga dakin da sauri don na ga meke faruwa, ashe Fatima ta Shiga Bayi ne shi kuma ya tashi daga bacci, da sauri itama ta fito jin kukan nasa.
Bayan wani lokaci Muna Zaune da Fatima a falo ka Kalle ni ta ce "Ikon Allah Rayuwar nan ba wahala Affan yau watan shi 5 da haihuwa" daidai lokacin da take koya masa zama kan kujera da take zaune. Na dago kaina daga wayar da nake dannawa "Allah kenan, rayuwar ba wahala ai, idan mutuwa ce fa haka za'a ce Yanzu Kamal Watan shi Biyar da rasuwa" Fatima ta murtuke fuska kafin tayi magana ran ta a bace "Gaskiya ka daina irin wanna maganar ana cikin firan jin dadi kana maganar mutuwa'' Affan kuwa babu abinda yakeyi sai dariya domin bai san kan shi ba ma balle kuma wani abu wai dan rayuwar duniya "Allah ya baki hakuri na daina, bari ma na tashi na fita office
"Da yafi da irin wannan firan"
Na tashi na shirya na dauka key din mota nayi waje tana rige da wata yar jaka da nake fita da ita nan bakin mota ta tsaya na shiga tayi min sallama ta koma cikin gida. Na kullo Kofar motar ta niyyar tada ta amma taki tashi, nayi ta gwadawa amma taki, dole na hakura na fito sai na kira bakaniken da ke mana gyaran motoci da yazo gida ya duba min.
Ba'a dauki dogon lokaci ba sai gashi yayi Sallama na amsa ya shigo,
"Me ya faru da Motar?" Ya tambayeni
"Lafiya Lau na shigo gida jiya yau kuma nayi kokarin tayar da ita taki tashi."
"To bari na duba"
Na bashi key din nace idan ya gama kawai kya kawo min motar office ina sauri zan hau adaidaita kawai, Na koma na sanar da Fatima ga mai gyara nan, ni zan wuce idan ya gama zai kawo min motar.
Na Fita bayi nisa ba na ga wani mai adaidaita na tsayar da shi tare da wasu yan mata guda biyu a ciki suna da kyau amma basu kai Fatima na ba, na shiga ya tayar da adaidaitan muka wuce, una tafiya sai satan kallon su nakeyi suna suna satan kallo na, sai dai nayi kamar ban gansu ba na dake kawai na share su, wayata ma na dauko na cigaba da latsawa muna tafiya har muka isa kusa da office din mu na sauka suka wuce.
A cikin adaidaita kuwa Zainab da Maryam suka dasa firan Kamal, Maryam ta kalli Zainab ta ce
"Gaskiya Gayen nan ya burgeni"
"ni fa kin riga ni ne kawai amma ni kai na wallahi ya burgeni"
"Gaskiya duk yadda za'ayi sai na auri wannan gayen ko ta wani hali don gaskiya yayi min"
"Ke Maryam, idan kuma yana da Mata fa?"
"Ba abinda ya dame ni da matarsa, in ta kama ma na kore ta a gidan"
"Gaskiya da baki kyauta ba kuwa, kika san irin zaman Lafiya da soyayyar da sukeyi? Kiji Tsoron Allah Maryam"
"Nidai abinda na sani shine ina son shi kuma sai na aure shi ko ta halin yaya.
To ana dara ga dare, Wacece Maryam? Tana Auren Kamal ko kuwa bata samun nasarar auren shi? ku cigaba da bibiyar wannan littafin.
Kada ku manta da comment da sharing na wannan post din domin wasu ma su sami nishadin da kuke samu, Nagode.